This repository has been archived by the owner on Feb 5, 2019. It is now read-only.
-
Notifications
You must be signed in to change notification settings - Fork 0
/
Copy pathha.gumi.txt
6249 lines (6247 loc) · 924 KB
/
ha.gumi.txt
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52
53
54
55
56
57
58
59
60
61
62
63
64
65
66
67
68
69
70
71
72
73
74
75
76
77
78
79
80
81
82
83
84
85
86
87
88
89
90
91
92
93
94
95
96
97
98
99
100
101
102
103
104
105
106
107
108
109
110
111
112
113
114
115
116
117
118
119
120
121
122
123
124
125
126
127
128
129
130
131
132
133
134
135
136
137
138
139
140
141
142
143
144
145
146
147
148
149
150
151
152
153
154
155
156
157
158
159
160
161
162
163
164
165
166
167
168
169
170
171
172
173
174
175
176
177
178
179
180
181
182
183
184
185
186
187
188
189
190
191
192
193
194
195
196
197
198
199
200
201
202
203
204
205
206
207
208
209
210
211
212
213
214
215
216
217
218
219
220
221
222
223
224
225
226
227
228
229
230
231
232
233
234
235
236
237
238
239
240
241
242
243
244
245
246
247
248
249
250
251
252
253
254
255
256
257
258
259
260
261
262
263
264
265
266
267
268
269
270
271
272
273
274
275
276
277
278
279
280
281
282
283
284
285
286
287
288
289
290
291
292
293
294
295
296
297
298
299
300
301
302
303
304
305
306
307
308
309
310
311
312
313
314
315
316
317
318
319
320
321
322
323
324
325
326
327
328
329
330
331
332
333
334
335
336
337
338
339
340
341
342
343
344
345
346
347
348
349
350
351
352
353
354
355
356
357
358
359
360
361
362
363
364
365
366
367
368
369
370
371
372
373
374
375
376
377
378
379
380
381
382
383
384
385
386
387
388
389
390
391
392
393
394
395
396
397
398
399
400
401
402
403
404
405
406
407
408
409
410
411
412
413
414
415
416
417
418
419
420
421
422
423
424
425
426
427
428
429
430
431
432
433
434
435
436
437
438
439
440
441
442
443
444
445
446
447
448
449
450
451
452
453
454
455
456
457
458
459
460
461
462
463
464
465
466
467
468
469
470
471
472
473
474
475
476
477
478
479
480
481
482
483
484
485
486
487
488
489
490
491
492
493
494
495
496
497
498
499
500
501
502
503
504
505
506
507
508
509
510
511
512
513
514
515
516
517
518
519
520
521
522
523
524
525
526
527
528
529
530
531
532
533
534
535
536
537
538
539
540
541
542
543
544
545
546
547
548
549
550
551
552
553
554
555
556
557
558
559
560
561
562
563
564
565
566
567
568
569
570
571
572
573
574
575
576
577
578
579
580
581
582
583
584
585
586
587
588
589
590
591
592
593
594
595
596
597
598
599
600
601
602
603
604
605
606
607
608
609
610
611
612
613
614
615
616
617
618
619
620
621
622
623
624
625
626
627
628
629
630
631
632
633
634
635
636
637
638
639
640
641
642
643
644
645
646
647
648
649
650
651
652
653
654
655
656
657
658
659
660
661
662
663
664
665
666
667
668
669
670
671
672
673
674
675
676
677
678
679
680
681
682
683
684
685
686
687
688
689
690
691
692
693
694
695
696
697
698
699
700
701
702
703
704
705
706
707
708
709
710
711
712
713
714
715
716
717
718
719
720
721
722
723
724
725
726
727
728
729
730
731
732
733
734
735
736
737
738
739
740
741
742
743
744
745
746
747
748
749
750
751
752
753
754
755
756
757
758
759
760
761
762
763
764
765
766
767
768
769
770
771
772
773
774
775
776
777
778
779
780
781
782
783
784
785
786
787
788
789
790
791
792
793
794
795
796
797
798
799
800
801
802
803
804
805
806
807
808
809
810
811
812
813
814
815
816
817
818
819
820
821
822
823
824
825
826
827
828
829
830
831
832
833
834
835
836
837
838
839
840
841
842
843
844
845
846
847
848
849
850
851
852
853
854
855
856
857
858
859
860
861
862
863
864
865
866
867
868
869
870
871
872
873
874
875
876
877
878
879
880
881
882
883
884
885
886
887
888
889
890
891
892
893
894
895
896
897
898
899
900
901
902
903
904
905
906
907
908
909
910
911
912
913
914
915
916
917
918
919
920
921
922
923
924
925
926
927
928
929
930
931
932
933
934
935
936
937
938
939
940
941
942
943
944
945
946
947
948
949
950
951
952
953
954
955
956
957
958
959
960
961
962
963
964
965
966
967
968
969
970
971
972
973
974
975
976
977
978
979
980
981
982
983
984
985
986
987
988
989
990
991
992
993
994
995
996
997
998
999
1000
1|1|Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1|2|Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu;
1|3|Mai rahama, Mai jin ƙai;
1|4|Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako.
1|5|Kai muke bauta wa, kuma Kai muke neman taimakonKa.
1|6|Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya.
1|7|Hanyar waɗanda Ka yi wa ni'ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba.
2|1|A. L̃. M̃.
2|2|Wãncan ne Littãfi, bãbu shakka a cikinsa, shiriya ne ga mãsu taƙawa.
2|3|Waɗanda suke yin ĩmãni game da gaibi, kuma suna tsayar da salla, kuma daga abin da Muka azurta su suna ciyarwa.
2|4|Kuma waɗanda suke yin ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar daga gabãninka, kuma game da Lãhira suna yin yaƙĩni.
2|5|Waɗannan suna kan shiriya, daga Ubangjinsu, kuma waɗannan su ne mãsu cin nasara.
2|6|Lalle ne waɗanda suka kãfirta daidai ne a kansu, shin kã yi musu gargaɗi kõ ba ka yi musu gargaɗi ba, ba zã su yi ĩmãni ba.
2|7|Allah Ya sa hãtimi a kan zukãtansu, da a kan jinsu, kuma a Kan ganin su akwai wata yãna; kuma suna da wata azãba mai girma.
2|8|Kuma akwai daga mutãne wanda yake cewa: "Mun yi imani da Allah kuma da Yinin Lãhira." Alhãli kuwa su ba muminai ba ne.
2|9|Suna yaudarayya da Allah da waɗanda suka yi ĩmãni, alhãli bã su yaudarar kõwa fãce kansu, kuma bã su sakankancẽwa!
2|10|A cikin zukãtansu akwai wata cũta. Sai Allah Ya ƙãramusu wata cũta, kuma suna da azãba mai raɗaɗi sabõda ãbin da suka kasance suna yi na ƙarya.
2|11|Kuma idan aka ce musu: "Kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa," sukan ce: "Mũ mãsu kyautatawa kawai ne!"
2|12|To, lalle ne su, sũne mãsu ɓarna, kuma amma bã su sansancewa.
2|13|Kuma idan aka ce musu: "ku yi ĩmãni kamar yadda mutãne suka yi ĩmãni," sukan ce: "Zã mu yi ĩmãni ne kamar yadda wãwãye suka yi ĩmãni?" To, lalle ne su, sũ ne wãwãye, kuma amma bã su sani.
2|14|Kuma idan sun haɗu da waɗanda suka yi ĩmãni, sukan ce: "Mun yi ĩmãni. "Kuma idan sun wõfinta zuwa ga shaiɗãnunsu, sukan ce: "Lalle ne muna tãre da ku: Mu mãsu izgili, kawai ne."
2|15|Allah Yana yin izgili gare su kuma Yana taimakon su a cikin ɓatarsu, suna ɗimuwa.
2|16|Waɗannan su ne waɗanda suka sayi ɓata da shiriya, sai fataucinsu bai yi rĩba ba, kuma ba su kasance masu shiryuwa ba.
2|17|Misãlinsu shĩ ne kamar misãlin wanda ya hũra wuta, to, a lõkacin da ta haskake abin da yake gẽfensa (na abin tsõro), Allah Ya tafi da haskensu, kuma Ya bar su a cikin duffai, bã su gani.
2|18|Kurãme, bẽbãye, makãfi, sabõda haka bã su kõmõwa.
2|19|Ko kuwa kamar girgije mai zuba daga sama, a cikinsa akwai duffai da tsãwa da walƙiya: suna sanyãwar yãtsunsu a cikin kunnuwansu dãga tsãwarwakin, dõmin tsõron mutuwa. Kuma Allah Mai kẽwayewane gã kãfirai!
2|20|Walƙiyar tana yin kusa ta fizge gannansu, ko da yaushe ta haskakã musu, sai su yi tafiya a cikinta, kuma idan ta yi duhu a kansu, sai su yi tsaye. Kuma dã Allah Yã so, sai Ya tafi da jinsu da gannansu. Lalle ne Allah a kan dukan kõme Mai ĩkon yi ne.
2|21|Yã ku mutãne! Ku bauta wa Ubangjinku, Wanda Ya halicce ku, kũ da waɗanda suke daga gabãninku, tsammãninku ku kãre kanku!
2|22|Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa, kuma sama gini, kuma Ya saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Ya fitar da abinci daga 'ya'yan itãce game da shi, sabõda ku. Sabõda haka kada ku sanya wa Allah wasu kĩshiyõyi, alhãli kuwa kuna sane.
2|23|Kuma idan kun kasance a cikin shakka daga abin da Muka sassaukar ga Bãwanmu, to, ku zõ da sũra guda daga misalinsa (Alƙur'ãni). Kuma ku kirãwo shaidunku baicin Allah, idan kun kasance mãsu gaskiya.
2|24|To, idan ba ku aikata (kãwo sura) ba, to, bã zã ku aikataba, sabõda haka, ku ji tsoron wuta, wadda makãmashinta mutãne da duwãtsu ne, an yi tattalinta dõmin kãfurai.
2|25|Kuma ka bãyar da bishãra ga waɗanda suka yi ĩmãni. kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, cẽwa lallene, suna da gidãjen Aljanna, ƙõramu na gudãna daga ƙarƙashinsu. Ko da yaushe aka azurta su da abinci daga wasu 'ya'yan itãce daga gare su, sai su ce: "Wannan shi ne aka azurta mu da shi daga gabãnin haka," Kuma a je musu da shi yana mai kama da juna, Kuma sunã da, a cikin su, mãtan aure mãsu tsarki, kuma su, cikin su madawwama ne.
2|26|Lalle ne, Allah bã Ya jin kunyar Ya bayyana wani misãli, kõwane iri ne, sauro da abin da yake bisa gare shi. To, amma waɗanda suka yi ĩmãni, sai su san cewa lalle shi ne gaskiya daga Ubangijin su, kuma amma waɗanda suka kãfirta, sai su ce: "Mẽne ne Allah Ya yi nufi da wannan ya zama misãli?" na ɓatar da wasu mãsu yawa da shi, kuma Yana shiryar da wasu mãsu yawada shi, kuma bã Ya ɓatarwa da shi fãce fasiƙai.
2|27|Waɗanda suke warware alƙawarin Allah daga bãyan ƙulla shi, kuma su yanke abin da Allah Ya yi umurni da shi a sãdar, kuma suna ɓarna a cikin ƙasa, waɗannan sũ ne mãsu hasãra.
2|28|Yaya kuke kãfirta da Allah, alhãli kuwa kun kasance matattu sa'an nan Ya rãyar da ku, sa'nnan kuma Ya matar da ku, sa'an nan kuma Ya rãya ku, sa'an nan zuwa gare Shi ake mayar da ku?
2|29|Shi ne Wanda Ya halitta muku abin da ke a cikin ƙasa gaba ɗaya, sa'an nan kuma Ya daidaita zuwa sama, sa'an nan Y a aikata su sammai bakwai. Kuma Shi ga dukan kõmai Masani ne.
2|30|Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya ce ga malã'iku: "Lalle ne, Ni Mai sanya wani halĩfa ne a cikin ƙasa," suka ce: "Ashe, zã Ka sanya a cikinta, wanda zai yi ɓarna a cikinta, kuma mu, muna yi maka tasbihi tare da gõde maka, kuma muna tsarkakewa gareka" Ya ce: "Lalle ne, Ni Na san abin da ba ku sani ba."
2|31|Kuma Ya sanar da Ãdam sũnãye dukansu, sa'an nan kuma ya gitta su a kan malã'iku, sa'n nan Ya ce: "Ku gaya mini sũnayen waɗannan, idan kun nasance mãsu gaskiya."
2|32|Suka ce: "Tsarki ya tabbata a gare Ka! Bãbu sani a gare mu, lalle ne Kai, Kai ne Masani, Mai hikima."
2|33|Ya ce: "Yã Ãdam! Ka gaya musu sũnãyensu." To, a lokacin da ya gaya musu sũnãyensu, (Allah) Ya ce: "Ashe, ban ce muku ba, lalle Ni, Inã sane da gaibin sammai da ƙasa, kuma (Inã sane da) abin da kuke bayyanawa da abin da kuka kasance kuna ɓõyewa?"
2|34|Kuma a lõkacin da Muka ce ga malã'iku: "Ku yi sujada ga Ãdam," Sai suka yi sujada, fãce Ibilĩsa ya ƙi, kuma ya yi girman kai, kuma ya kasance daga kãfirai.
2|35|Kuma muka ce: "Ya Ãdam! Ka zauna kai da matarka a gidan Aljanna, kuma ku ci daga gare ta, bisa wadãta, inda kuke so, kuma kada ku kusanci wannan itãciyar, har ku kasance daga azzãlumai."
2|36|Sai Shaiɗan ya talãlãɓantar da su ga barinta, sai ya fitar da su daga abin da suka kasance a cikinsa. Kuma muka ce: "Sãshenku nã maƙiyi ga sãshe, kuma kuna da a cikin ƙasa matabbata da jin dãɗi zuwa ga wani lõkaci."
2|37|Sai Ãdam ya karɓi wasu kalmõmi daga Ubangjjinsa, sabõda haka ya karɓi tũba a kansa. Lalle ne Shi, Shĩ ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai.
2|38|Muka ce: "Ku ku sauka daga gare ta gabã ɗaya. To, imma lalle shiriya ta je muku daga gare Ni, to, wanda ya bi shiriya ta to, bãbu tsõro a kansu, kuma bã su yin baƙin ciki."
2|39|"Kuma waɗanda suka kãfirta, kuma suka ƙaryata game da ãyõyinMu, waɗannan sũ ne abõkan Wuta; sũ a cikinta madawwama ne."
2|40|Yã Banĩ Isrã'Ĩla! Ku tuna ni'imãTa a kanku, kuma ku cika alƙawariNa, In cika muku da alƙawarinku. kuma Ni, ku ji tsõro Na.
2|41|Kuma, ku yi ĩmãni da abin da na saukar, mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da ku, kuma kada ku kasance farkon kãfiri game da shi, Kuma kada ku sayi 'yan kuɗi kaɗan da ãyõyiNa. Kuma ku ji tsõrõNa, Nĩ kaɗai.
2|42|Kuma kada ku lulluɓe gaskiya da ƙarya, kuma ku ɓõye gaskiya, alhãli kuwa kuna sane.
2|43|Kuma ku tsayar da salla; kuma ku bãyar da zakka; kuma ku yi rukũ'i tãre da mãsu yin rukũ'i.
2|44|Shin, kuna umurnin mutãne da alhẽri, kuma ku manta da kanku alhãli kuwa kuna karatun littãfi? Shin, bãzã ku hankalta ba?
2|45|Kuma ku nẽmi taimako da yin haƙuri, da salla. Kuma lalle ne ita, haƙĩƙa, mai girma ce fãce fa a kan mãsu tsõron Allah.
2|46|Waɗanda suka tabbata cẽwa lalle ne su mãsu haɗuwa da Ubangijinsu, kuma lalle ne sũ a gareshi mãsu kõmãwa ne.
2|47|Yã banĩ Isrã'ĩla! Ku tuna ni'imaTa, wadda Na ni'imta a kanku, kuma lalle ne Ni, na fĩfĩta ku a kan tãlikai.
2|48|Kuma ku ji tsron wani yini, (a cikinsa) rai bã ya Wadãtar da wani rai da kõme, kuma bã a karɓar cetõ daga gareshi, kuma ba a karɓar fansa daga gare shi, kuma bã su zama ana taimakon su ba.
2|49|Kuma a lõkacin da muka tsĩrar da ku daga mutãnen Fir'auna, su na taya muku muguntar azãba, su na yayyanke ɗiyanku maza su na rãyar da mãtanku. Kuma a cikin wancan akwai jarabawa mai girma daga Ubangijinku.
2|50|Kuma a lõkacin da Muka raba tẽku sabõda ku, sai Muka tsĩrar da ku kuma Muka nutsar da mutãnen Fir'auna, alhãli kuwa kũ kuna kallo.
2|51|Kuma a lõkacin da muka yi wa'adi ga Mũsa, dare arba'in, sa'an nan kuma kuka riƙi maraƙi daga bãyansa, alhãli kũ, kuna mãsu zãlunci (da bauta masa).
2|52|Sa'an nan kuma muka yãfe muku daga bãyan wancan, tsammãninku, kuna gõdẽwa.
2|53|Kuma a lõkacin da Muka baiwa Mũsa Littãfi da rarrabẽwa, tsammãninku, kuna shiryuwa.
2|54|Kuma a lõkacin da Mũsa ya ce ga mutãnensa: "Ya mutãnena! Lalle ne ku, kun zãlunci kanku game da riƙonku maraƙin, sai ku tũba zuwa ga Mahaliccinku, sai ku kashe kãwunanku. Wancan ne mafii alheri a wajen mahaliccinku. Sa'an nan Ya karɓi tuba a kanku. lalle ne Shi, Shi ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai.
2|55|Kuma a lõkacin da kuka ce: "Ya Musa! Bã zã mu yi ĩmãni ba dõminka, sai munga Allah bayyane," sabada haka tsãwar nan ta kamaku, alhãli kuwa kuna kallo.
2|56|Sa'an nan kuma Muka tãyar da ku daga bãyan mutuwarku, tsammãninku, kuna gõdẽwa.
2|57|Kuma Muka sanya girgije ya yi inuwa a kanku, kuma Muka saukar da darɓa da tantabaru a kanku; "Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurta ku." kuma ba su zãlunce Mu ba, kuma amma kansu suka kasance suna zãlunta.
2|58|Kuma a lokacin da Muka ce: "Ku shiga wannan alƙarya. San nan ku ci daga gareta, idan kuka so, bisa wadata, kuma ku shiga ƙofa kuna masu tawalu'i, kuma ku ce; "kãyar da zunubai" Mu gãfarta muku laifukanku, kuma zã mu ƙãra wa mãsu kyautatawa."
2|59|Sai waɗanda suka yi zalunci suka sake magana watar wannan da aka ce musu, saboda haka muka saukar a kan waɗanda suka yi zãlunci da azãba daga sama sabõda abin da suka kasance suna yi na fãsiƙanci.
2|60|Kuma a lokacin da Mũsa ya nemi shãyarwa domin mutãnensa, Muka ce; "Ka dõki dũtsen da sandarka." Sai marmaro gõma sha biyu suka ɓuɓɓugo, haƙĩƙa, kõwaɗanne mutãne sun san wurin shansu. "Ku ci kuma ku sha daga arziƙin Ubangijinku, kuma kada ku yi fasadi, a cikin ƙasa, kuna mãsu ɓarna."
2|61|Kuma a lõkacin da kuka ce: "Yã Mũsã! Bã zã mu yi haƙuri ba a kan abinci guda. Sai ka rõƙa mana Ubangijinka Ya fitar mana daga abin da ƙasa take tsirarwa daga ganyenta, dumanta, da alkamarta da albasarta. Ya ce: "Kuna nẽman musanya abin da yake mafi ƙasƙanci da wanda yake mafi alhẽri? Ku sauka wani birni (daga cikin birane), lalle ne, kuna da abin da kuka rõƙa. "Kuma Muka dõka musu walãƙanci da talauci. Kuma suka kõma da wani fushi daga Allah. Wancan sabõda lalle su, sun kasance suna kãfirta da ãyõyin Allah, kuma suna kashe Aannabãwa, bãda hakki ba. Wancan, sabõda sãɓawarsu ne, kuma sun kasance suna ƙẽtarewar haddi.
2|62|Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, da waɗanda suka tũba, da Nasãra da Makarkata, wana ya yi ĩmani da Allah da Yinin Lãhira, kuma ya aikata aikin ƙwarai, to, suna da ijãrarsu a wurin Ubangijinsu, kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna yin baƙin ciki ba.
2|63|Kuma a lõkacin da Muka riƙi alƙawarinku, kuma Muka ɗaukaka dũtse a bisa gareku: "Ku kãma abin da Muka baku da ƙarfi. Kuma ku ambaci abin da yake a cikin sa, tsammãninku ku kãrekanku.
2|64|Sa'an nan kuma kuka jũya daga bayan wancan, to, bã dõmin falalar Allah ba da rahamarSa a kanku, haƙĩƙa, dã kun kasance daga mãsu hasãra."
2|65|Kuma lalle ne, haƙĩƙa, kun san waɗanda suka ƙẽtare haddi daga gare ku a cikin Asabar, sai muka ce musu: "ku kasance birai ƙasƙantattu."
2|66|Muka sanya ta (mas'alar) azãba, dõmin abin da yake gaba gareta, da yake a bãyanta, kuma wa'azi ga mãsu taƙawa.
2|67|Kuma a lõkacin da Musa yace ga mutanensa: "Lalle ne, Allah Yana umurtar ku da ku yanka wata sãniya." Suka ce: "Shin kana riƙon mu ne da izgili?" Ya ce: "Ina nẽman tsari daga Allah da in kasance daga jãhilai."
2|68|Suka ce: "Ka rõƙa mana Ubangijinka, Ya bayyana mana, mecẽ ce ita?" Ya ce: "Lalle ne, Shi, Yana cewa: "Lalle ne ita sãniya ce; bã tsõfuwa ba, bã kuma budurwa ba, tsakãtsaki ce a tsakãnin wancan,' sai ku aikata abin da ake umurninku."
2|69|Suka ce: "Ka rõƙa mana Ubangijinka Ya bayyana mana abin da yake launinta." Ya ce: "Lalle ne, Shi Yana cewa: "Ita wata saniya ce fatsa-fatsa, mai tsan-tsan launi, tana faranta ran mausu kallonta."
2|70|Suka ce: "Ka rõƙa mana Ubangijinka, Ya bayyana mana abin da yake ita, lalle ne shãnu suna yi mana kamã da jũna, kuma mu, idan Allah Yã so, haƙĩƙa, shiryuwa ne."
2|71|Ya ce: "Lalle ne Shi, Yana cẽwa: "Ita wata sãniya ce; ba horarra bã tana noman ƙasa, kuma ba ta shayar da shuka, lãfiyayya ce: bãbu wani sõfane a cikinta." Suka ce: "Yanzu kã zo da gaskiya. Sai suka yanka ta, kamar ba zã su aikata ba.
2|72|Kuma a lõkacin da kuka yi kisan kai, kuka dinga tunkuɗa wa jũna laifĩ a cikinsa, kuma Allah Mai fitar da abin da kuka kasance kuna ɓõyẽwa ne.
2|73|Sai Muka ce: "Ku dõke shi da wani sãshenta." Kamar wancan ne Allah Yake rãyar da matattu, kuma Ya nũna muku ayõyinSa, tsammãninku kuna hankalta.
2|74|San'nan kuma zukãtanku, suka ƙẽƙashe daga bãyan wancan. Sabõda haka suka zamanto kamar duwatsu. Ko mafi tsananin ƙeƙashewa. kuma lalle ne daga duwãtsu, haƙĩka, akwai abin da maremari suke ɓuɓɓuga daga gare shi, kuma lalle ne daga gare su, haƙĩƙa, akwai abin da yake tsatstsagewa har ruwa ya fita daga gare shi, kuma lalle ne, haƙĩƙa, daga gare su, haƙĩƙa, akwai da yake fãɗõwa dõmin tsõron Allah, kuma Allah bai zama gãfili ba daga barin abin da kuke aikatãwa.
2|75|Shin fa kuna tsammãnin zã su yi imãni sabõda ku, alhãli kuwa, haƙĩƙa, wata ƙungiya daga gare su sun kasance suna jin maganar Allah, sa'an nan kuma su karkatar da ita daga bãyan sun gãne ta, alhãli sũ, suna sane?
2|76|Kuma idan sun haɗu da waɗanda suka yi ĩmãni sukan ce: "Mun yi ĩmãni," kuma idan sãshensu ya wõfinta zuwa ga sãshe, sukan ce: "Shin, kuna yi musu magana da abin da Allah Ya buɗa muku ne dõmin su yi muku hujja da shi a wurin Ubangijinku?" Shin fa, bã ku hankalta?
2|77|Shin, kuma bã su sanin cẽwa lalle ne Allah Yana sanin abin da suke ɓõyẽwa da abin da suke bayyanãwa?
2|78|Kuma daga cikinsu akwai ummiyyai, bã su da sanin Littãfi, fãce tãtsuniyoyi, kuma sũ bã kõme suke yi ba fãce suna yin zato.
2|79|To, bone ya tabbata ga waɗanda suke rubũta littãfi da hannuwansu sa'an nan kuma su ce wannan daga wurin Allah yake, dõmin su sayi kuɗi kaɗan da shi, san nan bone ya tabbata a gare su daga abin da hannayensu ke rubũtãwa, kuma bone ya tabbata a gare su daga abin da suke sanã'antãwa.
2|80|Kuma suka ce: "Wuta bã zã ta shãfe mu ba, fãce, 'yan kwãnuka ƙidãyayyu."Ka ce: "Ashe kun riƙi wani alkawari a wurin Allah, sa'an nan Allah ba zai sãɓa wa alkawarinSa ba ko kuwa kuna faɗin abin da ba ku sani ba bisa ga Allah?"
2|81|Na'am! Wanda ya yi tsiwur-wurin mũgun abu, kuma laifinsa ya kẽwaye shi, to, waɗannan su ne 'yan Wuta, sũ a cikinta madawwama ne.
2|82|Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, waɗannan, 'yan Aljanna ne, sũ a cikinta madawwama ne.
2|83|Kuma a lõkacin da Muka karɓi alkawarin Bani-Isrã'ĩla: "Kada ku bauta wa kõwa fãce Allah, kuma ga mahaifa ku kyautata, da mai zumunta da marãyu da matalauta, kuma ku faɗi magana mai kyau zuwa ga mutãne, kuma ku tsayar da salla, kuma ku bãyar da zakka, sa'an nan kuka jũya bãya, fãce kaɗan daga gare ku, alhãli kuwa kuna mãsu bijirẽwa.
2|84|Lõkacin da Muka riƙi alkawarinku; bã zã ku zubar da jininku ba, kuma bã zã ku fitar da kanku daga gidãjenku ba; sa'an nan kuka tabbatar alhãli kuwa kuna bãyar da shaida (a kanku).
2|85|Sa'an nan kuma, gã ku, yã waɗannan! Kuna kashe kanku, kuma kuna fitar da wani ɓangare daga gare ku daga gidãjensu, kuna taimakon jũna a kansu da zunubi da zãlunci kuma idan kãmammu suka je muku kuna fansarsu alhãli kuwa shĩ fitar da su abin da aka haramta muku ne. Shin fa, kuna ĩmãni da sãshen Littãfin ne, kuma ku kãfirta da sãshe? To, mẽne ne sakamakon wanda ke aikata wancan daga gare ku fãce wulãkanci a cikin rãyuwar dũniya? Kuma a Rãnar ¡iyãma ana mayar da su zuwa ga mafi tsananin azãba. Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga barin abin da kuke aikatãwa.
2|86|Waɗannan su ne waɗanda suka sayi rãyuwar dũniya da Lãhira, dõmin haka bã zã a sauƙaƙa azãba ba daga kansu, kuma sũ, bã ataimakonsu.
2|87|Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Munbai wa Mũsã Littãfi, kuma Mun biyar daga bãyansa da wasu Manzanni, kuma Muka bai wa Ĩsã ɗan Maryama hujjõji bayyanannu, kuma Muka ƙarfafa shi da Rũhi mai tsarki. Shinfa, kõ da yaushe wani manzo ya je muku tãre da abin da rãyukanku bã su so, sai ku kangara, wani ɓangare kun ƙaryata, kuma wani ɓangare kuna kashẽwa?
2|88|Kuma suka ce: "Zukatanmu suna cikin rufi." A'a, Allah Yã la'ane su, dõmin kafircinsu kadan kwarai suke yin ĩmãni!
2|89|Kuma a lõkacin da wani Littãfi daga wurin Allah ya je musu, mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da su, alhãli kuwa sun kasance daga gabãnin haka suna fãtar taimako da shi a kan waɗanda suka kãfirta. To, a lõkacin da abin da suka sani ya je musu, sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka la'anar Allah ta tabbata a kan kãfirai.
2|90|Tir, da abin da suka sayi rãyukansu da shi; watau su kãfirta da abin da Allah Ya saukar sabõda zãlunci; kada Allah Ya saukar da falalarsa a kan wanda Yake so daga bãyinsa. Sai suka kõmo da fushi game da wani fushi. Kuma ga kãfirai akwai azãba mai wulãƙantarwa.
2|91|Kuma idan aka ce musu: "Ku yi ĩmãni da abin da Allah Ya saukar." Sai su ce: "Muna ĩmãni da abin da aka saukar a gare mu," kuma suna kãfircẽwa da abin da ke bãyansa, alhãli kuwa, shi ne gaskiyar (da suka sani) mai gaskatawa ga abin da yake tãre da su (na Attaura) Ka ce: "To, don me kuke kashe annabãwan Allah gabãnin wannan, idan kun kasance mãsu bãyar da gaskiya?"
2|92|Kuma lalle ne haƙĩƙa Mũsã ya zo muku da hujjõji bayyanannu, sa'an nan kuka riƙi maraƙi (daga bãyansa, alhãli kuwa kuna mãsu zãlunci.
2|93|Kuma a lõkacin da Muka riƙi alkawarinku kuma Muka ɗaukaka dutse a bisa gare ku, (Muka ce:) "Ku riƙi abin da Muka kãwo muku da ƙarfi kuma ku ji" Suka ce: "Mun ji kuma mun ƙi." Kuma aka zuba son maraƙin a cikin zukatansu sabõda kãfircinsu. Ka ce: "Tir da abin da ĩmãninku yake umurnin ku da shi, har idan kun kasance mãsu ĩmãni!"
2|94|Ka ce: "Idan Gidan Lãhira ya kasance sabõda ku, a wurin Allah keɓe bã da sauran mutãne ba, to, ku yi gũrin mutuwa, idan kun kasance mãsu gaskiya."
2|95|Kuma bã zã su yi gũrinta bahar abada sabõda abin da hannayensu, suka gabãtar. Kuma Allah Masani ne ga azzãlumai.
2|96|Kuma lalle ne, zã ka sãme su mafiya kwaɗayin mutãne a kan rãyuwa, kuma sũ ne mafiya kwaɗayin rãyuwa daga waɗanda suka yi shirka. ¦ayansu yana son dã zã a rãyar da shi shekara dubu, kuma bã ya zama mai nĩsantar da shi daga azãba dõmin an rãyar da shi. Kuma Allah, Mai gani ne ga abin da suke aikatãwa.
2|97|Ka ce: Wanda ya kasance maƙiyi ga Jibirilu, to, lalle ne shi ya saukar da shi a kan zũciyarka da izinin Allah, yana mai gaskatãwa ga abin da yake gaba gare shi, kuma da shiriya da bishãra ga mũminai.
2|98|Wanda ya kasance maƙiyi ga Allah da malã'ikunSa da manzanninSa da Jibirĩla da Mĩkã'ĩla to, lalle ne, Allah Maƙiyi ne ga kãfirai.
2|99|Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun saukar, zuwa gare ka, ãyõyi bayyanannu, kuma ba wanda yake kãfirta da su fãce fãsikai.
2|100|Shin, kuma a kõ da yaushe suka ƙulla wani alkawari sai wani ɓangare daga gare su ya, yi jĩfa da shi? Ã'a, mafi yawansu bã su yin ĩmãni.
2|101|Kuma a lõkacin da wani manzo (Muhammadu) daga wurin Allah ya je musu, mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da su, sai wani ɓangare daga waɗanda aka bai wa Littãfi, suka yar da Littãfin (Alƙur'ãnin) Allah a bãyan bãyansu, kamar dai sũ ba su sani ba.
2|102|Kuma suka bi abin da shaiɗãnu ke karantawa a kan mulkin Sulaimãnu, kuma Sulaimãnu bai yi kãfirci ba, kuma Shaidãnun, sũ ne suka yi kãfirci, suna karantar da mutãne sihiri. Kuma ba a saukar da shi ba a kan malã'iku biyu a Bãbila, Harũta da Mãrũta. Kuma ba su sanar da kõwa ba balle su ce: "Mũ fitina kawai ne, sabõda haka kada ka kãfirta," balle har su yi ta nẽman ilmin abin da suke rarrabẽwa tsakãnin mutum da mãtarsa da shi daga gare su. Kuma su (mãsu yin sihirin) ba su zama mãsu cũtar da kõwa da shi ba, fãce da iznin Allah. Kuma suna nẽman ilmin abin da yake cũtar da su, kuma bã ya amfaninsu. Kuma lalle ne, haƙiƙa, sun sani, tabbas, wanda ya saye shi, bã ya da wani rabo a cikin Lãhira. Kuma tir da abin da suka sayar da rãyukansu da shi, dã sun kasance suna sani.
2|103|Kuma dã lalle ne sũ, sun yi ĩmani, kuma sun yi taƙawa, haƙiƙa, da sakamako daga wurin Allah shi ne mafi alhẽri, dã sun kasance suna sani.
2|104|Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku ce: 'Rã'inã' kuma ku ce: 'Jinkirtã manã', kuma ku saurara. Kuma kãfirai suna da azãba mai raɗaɗi.
2|105|Waɗanda suka kãfirta daga Ma'abuta Littãfi, bã su son a saukar da wani alhẽri a kanku daga Ubangijinku, kuma mushirikai mã bã su so. Kuma Allah Yana keɓance da wanda Yake so da rahamarSa. Kuma Allah Ma'abũcin falala mai girma ne.
2|106|Abin da Muka shãfe daga ãya, ko kuwa Muka jinkirtar da ita, zã Mu zo da mafi alhẽri daga gare ta ko kuwa misãlinta. Ashe, ba ka sani ba, cẽwa lalle ne, Allah a kan dukkan kõme Mai ĩkon yi ne?
2|107|Shin ba ka sani ba, cẽwa lalle ne Allah, Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa kuma bã ku da, baicin Allah, wani majiɓinci, kuma bã ku da wani mataimaki?
2|108|Kõ kuna nufin ku tambayi Manzonku, kamar yadda aka tambayi Mũsã a gabãnin haka? Kuma wanda ya musanya kãfirci da ĩmãni, to, lalle ne yã ɓace tsakar hanya.
2|109|Mãsu yawa daga Ma'abuta Littãfi sunã gũrin dã sun mayar da ku, daga bãyan ĩmãninku, kãfirai, sabõda hãsada daga wurin rãyukansu, daga bayãn gaskiya tã bayyana a gare su. To, ku yãfe, kuma ku kau da kai, sai Allah Yã zo da umurninSa. Lalle ne Allah a kan dukkan kõme Mai ĩkon yi ne.
2|110|Kuma ku tsayar da salla, kuma ku bãyar da zakka. Kuma abin da kuka gabãtar dõmin kanku daga alhẽri, zã ku sãme shi a wurin Allah. Lalle ne Allah, ga abin da kuke aikatãwa Mai gani ne.
2|111|Kuma suka ce: "Bãbu mai shiga Aljanna fãce waɗanda suka zama Yahũdu ko Nasãra." Waɗancan tãtsũniyõyinsu ne. Ka ce: "Ku kãwo dalilinku idan kun kasance mãsu gaskiya."
2|112|Na'am! Wanda ya sallama fuskarsa ga Allah, alhãli kuwa yana mai kyautatãwa, to, yana da ijãrarsa, a wurin Ubangijinsa, kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna baƙin ciki ba.
2|113|Kuma Yahũdãwa suka ce: "Nasãra ba su zamana a kan kõme ba," kuma Nasãra suka ce: "Yahũdãwa ba su zamana a kan kõmeba," alhãli kuwa su, suna karãtun Littãfi. Kamar wancan ne waɗanda ba su sani ba suka faɗa, kamar maganarsu sabõda haka Allah ne ke yin hukunci a tsakãninsu a Rãnar ¡iyãma, a cikin abin da suka kasance suna sãɓawa jũna a cikinsa.
2|114|Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya hana masallãtan Allah, dõmin kada a ambaci sunanSa a cikinsu, sai kuma ya yi aiki ga rushe su? Waɗannan bã ya kasancẽwa a gare su su shigẽ su fãce suna mãsu tsõro. Suna da, a cikin duniya wani wulãkanci, kuma suna da, a cikin Lãhira, azãba mai girma.
2|115|Kuma Allah ɗai yake da gabas da yamma sabõda haka, inda duk aka jũyar da ku, to, a can fuskar Allah take. Lalle ne, Allah Mawadãci ne, Mai ilmi.
2|116|Kuma suka ce: "Allah Yã riƙi ɗã." Tsarki yã tabbata a gare Shi! A'a, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da ƙasa, dukansu, a gare Shi, mãsu ƙanƙan da kai ne.
2|117|Mai kyautata halittar sammai da ƙasa, kuma idan Ya hukunta wani al'amari, sai kawai Ya ce masa: "Kasance." Sai ya yi ta kasancewa.
2|118|Kuma waɗanda bã su da sani suka ce: "Don me Allah bã Ya yi mana magana, ko wata ãyã ta zo mana?" Kamar wancan ne waɗanda suke a gabãninsu suka faɗa, kamar maganarsu. zukãtansu sun yi kamã da jũna. Lalle ne, Mun bayyana ãyõyi ga mutãne masu sakankancewa.
2|119|Lalle ne Mun aike ka da gaskiya, kana mai bãyar da bishãra, kuma mai gargaɗi, kuma bã zã a tambaye ka ba, game da abõkan Wuta.
2|120|Kuma Yahũdu bã zã su yarda da kõme daga gare ka ba, kuma Nasãra bã zã su yarda ba, sai kã bi irin aƙidarsu. Ka ce: "Lalle ne, shiriyar Allah ita ce shiriya." Kuma lalle ne idan ka bi son zũciyõyinsu a bãyan abin da ya zo maka na ilmi, bã ka da, daga Allah, wani majiɓinci, kuma bãbu wani mataimaki.
2|121|Waɗanda Muka bai wa Littãfi suna karãtunsa a kan haƙƙin karãtunsa, waɗannan suna ĩmani da shi (Alƙur'ãni). Kuma wanda ya kãfirta da shi, to, waɗannan sũ ne mãsu hasãra.
2|122|Yã Banĩ Isrã'ĩla! Ku tuna ni'imaTa wadda Na ni'imtar da ita a kanku, kuma lalle ne Nĩ, Nã fĩfĩtã ku a kan tãlikai.
2|123|Ku ji tsõron wani yini, (a cikinsa) wani rai bã ya tunkuɗe wa wani rai kõme kuma bã a karɓar fansa daga gare shi, kuma wani cẽto bã ya amfanin sa, kuma ba su zama ana taimakon su ba.
2|124|Kuma a lõkacin da Ubangijin Ibrãhim Ya jarrabẽ shi da wasu kalmõmi, sai ya cika su. Ya ce: "Lalle ne Nĩ, Mai sanya ka shugaba dõmin mutãne ne." Ya ce: "Kuma daga zũriyata." Ya ce: "AlkawarĩNa bã zai sãmu azzãlumai ba."
2|125|Kuma a lõkacin da Muka sanya ¦ãkin ya zama makõma ga mutãne, da aminci, kuma ku riƙi wurin salla daga Maƙãmi Ibrãhĩm, kuma Muka yi alƙawari zuwa ga Ibrãhĩm, da Ismã'ila da cẽwa: "Ku tsarkake ¦ãkiNa dõmin mãsu ɗawãfi da mãsu lizimta da mãsu rukũ'i, mãsu sujada."
2|126|Kuma a lõkacin da lbrãhĩm ya ce: "Yã Ubangijĩna! Ka sanya wannan gari amintacce, Ka azurta mutãnensa, daga 'ya'yan itãcen, wanda ya yi ĩmãni, daga gare su, da Allah da Ranar Lãhira." Allah Ya ce: "Wanda ya kãfirta ma Ina jiyar da shi dãɗi kaɗan, sa'an nan kuma Ina tĩlastã shi zuwa ga azãbar Wuta. Kuma makõmar, ta munana."
2|127|Kuma a lõkacin da Ibrãhĩm yake ɗaukaka harsãshin gini ga ¦ãkin, da Ismã'ĩla (suna cẽwa:) "Yã Ubangijnmu! Ka karɓa daga gare mu, lalle ne Kai, Kai ne Mai ji, Mai sani.
2|128|"Ya Ubangijnmu! Ka sanyã mu, mu biyu, waɗanda suka sallama (al'amari) gare Ka, kuma daga zuriyarmu (Ka sanya) al'umma mai sallamãwa zuwa gare Ka, Kuma Ka nũna mana wurãren ibãdar hajjinmu, kuma Ka karɓi tũba a kanmu. Lalle ne Kai, Kai ne Mai karɓar tũba, Mai rahama.
2|129|"Ya Ubangijinmu! Ka aiko, a cikinsu, wani manzo daga gare su, yana karanta musu ãyõyinKa, kuma yana karantar da su Littãfin da hikimar, kuma yana tsarkake su. Lalle ne Kai, Kai ne Mabuwãyi Mai hikima."
2|130|Kuma wãne ne yake gudu daga aƙĩdar Ibrãhĩm, fãce wanda ya jãhilta ga ransa? Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zãɓe shi, a cikin dũniya, kuma lalle ne shi, a cikin Lãhira, haƙĩƙa, yana daga sãlihai.
2|131|A lõkacin da Ubangijinsa Ya ce masa: "Ka miƙa wuya," ya ce: "Nã miƙa wuya ga Ubangijin tãlikai."
2|132|Kuma lbrãhĩm ya yi wasiyya da ita ga ɗiyansa, kuma Ya'aƙũbu (ya yi wasiyya, suka ce:) "Yã ɗiyãna! Lalle ne, Allah Ya zãɓã muku addini don haka kada ku mutu, lalle, fãce kuna Musulmi."
2|133|Ko kun kasance halarce a lõkacin da mutuwa ta halarci Ya'aƙũbu, a lõkacin da ya ce wa ɗiyansa: "Mẽne ne zã ku bauta wa daga bãyãna?" Suka ce: "Muna bauta wa Abin bautawarka kuma Abin bautawar ubanninka lbrãhĩm da lsmã'ĩla da Is'hãƙa, Ubangiji Guda, kuma mu a gare Shi mãsu miƙa wuya ne."
2|134|Waccan, wata al'umma ce, ta riga ta shige, tana da abin da ta sanã'anta kuma kuna da abin da kuka sanã'anta, Kuma bã zã a tambaye ku ba daga abin da suka kasance suna aikatãwa.
2|135|Kuma suka ce: "Ku kasance Yahũdãwa ko Nasãra, kwã shiryu."Ka ce: "A'a aƙidar Ibrãhĩm dai, maikarkata, zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba."
2|136|Ku ce: "Mun yi ĩmãni da Allah, da abin da aka saukar zuwa gare mu, da abin da aka saukar zuwa ga Ibrãhĩm da Ismã'ĩla da Is'hãka da Ya'aƙũbu da jĩkõki, da abin da aka bai wa Mũsã da Ĩsã, da abin da aka bai wa annabãwa daga Ubangijinsu, bã mu rarrabẽwa a tsakãnin kõwa daga gare su, kuma mu, a gare Shi, mãsu miƙa wuya ne."
2|137|To, idan sun yi ĩmãni da misãlin abin da kuka yi ĩmãni da shi, to, lalle ne sun shiryu, kuma idan sun jũya bãya, to, suna a cikin sãɓãni kawai sabõda haka Allah zai isar maka a gare su, kuma Shi ne Mai ji, Masani.
2|138|Rinin Allah! Kuma wãne ne mafi kyau ga rini daga Allah? Kuma mu, a gare Shi, mãsu bautãwa ne.
2|139|Ka ce: Shin kuna jãyayyar hujia ne da mu a cikin al'amarin Allah, alhãli kuwa Shi ne Ubangijinmu kuma Ubangijinku, kuma muna da ayyukanmu, kuma kuna da ayyukanku, kuma mũ, a gare Shi, mãsu tsarkakẽwane?
2|140|Ko kuna cẽwa: Lalle ne, Ibrãhĩm da Ismã'ĩla da Is'hãƙa da Ya'aƙũbu da Jĩkõki, sun kasance Yahũdãwa kõ kuwa Nasãra? Ka ce: Shin kũ ne kuke mafi sani kõAllah? Kuma wãne ne ya zama mafi zãlunci daga wanda ya bõye shaida a wurinsa daga Allah? Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga abin da kuke aikatãwa!
2|141|Waccan, wata al'umma ce, tã riga ta shige, suna da abin da suka sana'anta kuma kuna da abin da kuka sana'anta kuma bã a tambayar ku daga abin da suka kasance suna aikatãwa.
2|142|Wãwãye daga mutãne zã su ce: Mẽne ne ya jũyar da su daga alƙiblarsu wadda suka kasance a kanta? Ka ce: "Allah ¦ai ne Yake da gabas da yamma, Yana shiryar da wanda Yake so zuwa ga hanya madaidaiciya."
2|143|Kuma kamar wancan, Muka sanya ku al'umma matsakaiciya dõmin ku kasance mãsu bãyar da shaida a kan mutãne. Kuma Manzo ya kasance mai shaida a kanku. Kuma ba Mu sanya Alƙibla wadda ka kasance a kanta ba, fãce dõmin Mu san wanda yake biyar Manzo daga wanda yake jũyãwa a kan duga-dugansa. Kuma lalle ne, tã kasance haƙĩƙa, mai girma, sai a kan waɗanda Allah Ya shiryar. Kuma ba ya yiwuwa ga Allah Ya tõzartar da ĩmãninku. Lalle ne, Allah, ga mutãne, haƙĩƙa, Mai tausayi ne, Mai jin ƙai.
2|144|Lalle ne, Muna ganin jujjũyãwar fuskarka a cikin sama. To, lalle ne, Mu jũyar da kai ga Alƙibla wadda kake yardã da ita. Sai ka jũyar da fuskarka wajen Masallãci Tsararre, kuma inda duk kuka kasance, to, ku jũyar da fuskõkinku jiharsa. Kuma lalle ne waɗanda aka bai wa Littãfi, haƙĩƙa su, sunã sanin lalle ne, shĩ ne gaskiya, daga Ubangijinka. Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga abin da suke aikatãwa.
2|145|Kuma hakĩka, idan ka je wawaɗanda aka bai wa Littafi da dukan ãyã, bã zã su bi Alƙiblarka ba, kuma kai ba ka zama mai bin Alƙiblarsu ba, kuma sãshensu bã mai bin Alƙiblar sãshe ba ne. Kuma haƙĩƙa, idan ka bi son zũciyõyinsu daga bãyan abin da ya zo maka daga ilmi, lalle ne kai, sa'an nan, haƙiƙa, azzãlumi kake.
2|146|Waɗanda Muka bã su Littãfi, suna saninsa kamar yadda suke sanin ɗiyansu. Kuma lalle ne wani ɓangare daga gare su, haƙiƙa, suna ɓõyewar gaskiya alhãli kuwa sũ, suna sane.
2|147|Gaskiya daga Ubangijinka take sabõda haka, lalle kada ka kasance daga mãsu shakka.
2|148|Kuma kõwane ɓangare yana da alƙibla wadda yake shi mai fuskantar ta ne. Sai ku yi tsẽre zuwa ga ayyukan alhẽri, inda kuka kasance duka Allah zai zo da ku gabã ɗaya. Lalle ne Allah, a kan kõme, Mai ĩkon yi ne.
2|149|Kuma daga inda ka fita, to, sai ka jũyar da fuskarka a wajen Masallãci Tsararre kuma lalle tabbas, shi ne gaskiya daga Ubangijinka. Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga abin da kuke aikatãwa ba.
2|150|Kuma daga inda ka fita, to, ka jũyar da fuskarka a wajen Masallãci Tsararre kuma inda kuke duka, to, ku jũyar da fuskõkinku a wajensa, dõmin kada wata hujja ta kasance ga mutãne a kanku, fãce waɗanda suka yi zãlunci daga gare su. Sabõda haka kada ku ji tsõronsu kuma ku ji tsõrõNa kuma dõmin In cika ni'imaTa a kanku, kuma tsammãninku zã ku shiryu.
2|151|Kamar yadda Muka aika Manzo a cikinku, daga gare ku, yana karanta ãyõyinMu a gare ku kuma yana tsarkake ku, kuma yana sanar da ku Littãfi da hikima, kuma yana sanar da ku abin da ba ku kasance kuna sani ba.
2|152|Sabõda haka, ku tuna Ni, In tunã ku, kuma ku yi gõdiya gare Ni, kuma kada ku butulce Mini.
2|153|Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku nẽmi taimako da haƙuri game da salla. Lalle ne, Allah na tãre da mãsu haƙuri.
2|154|Kada ku ce ga waɗanda ake kashẽwa a cikin hanyar Allah: "Matattu ne." Ã'a, rãyayyu ne, kuma amma bã ku sansancẽwa.
2|155|Kuma lalle ne, Muna jarrabar ku da wani abu daga tsõro da yunwa da naƙasa daga dũkiya da rãyuka da 'ya'yan itãce. Kuma ka yi bishãra ga mãsu haƙuri.
2|156|Waɗanda suke idan wata masĩfa ta sãme su, sai su ce: "Lalle ne mũ ga Allah muke, kuma lalle ne mũ, zuwa gare Shi, muke kõmãwa."
2|157|Waɗannan akwai albarku a kansu daga Ubangijinsu da wata rahama. Kuma waɗannan sũ ne shiryayyu.
2|158|Lalle ne Safã da Marwa suna daga wurãren ibãdar Allah, to, wanda ya yi hajin ¦ãki kõ kuwa ya yi Umra, to, bãbu laifi a kansa ga ya yi ɗawãfi gare su, su biyu. Kuma wanda ya ƙãra yin wani aikin alhẽri to, lalle ne Allah Mai gõdiya ne, Masani.
2|159|Lalle ne waɗanda suke ɓõyẽwar abin da Allah Ya saukar da ga hujjõji bayyanannu, da shiriya, daga bãyan Mun bayyana shi ga mutãne, a cikin Littãfi (Alƙur'ãni), waɗannan Allah Yana la'anar su, kuma mãsu la'ana suna la'anar su.
2|160|Sai waɗanda suka tũba, kuma suka gyãra, kuma suka bayyana, to waɗannan Ina karɓar tũba a kansu kuma Nĩ ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai.
2|161|Lalle ne, waɗanda suka kãfirta kuma suka mutu alhãli kuwa suna kãfirai, waɗannan akwai, a kansu, la'anar Allah da Malã'iku da mutãne gabã ɗaya.
2|162|Suna madawwama a cikinta, bã a sauƙaƙa azãba daga barinsu, kuma ba su zama ana jinkirta musu ba.
2|163|Kuma Ubangijinku Ubangiji Guda ne. Bãbu wani Ubangiji fãce Shi, Mai rahama, Mai jin ƙai.
2|164|Lalle ne, a cikin halittar sammai da ƙasa, da sãɓãwar dare da yini, da jirãge wadaɗnda suke gudana a cikin tẽku (ɗauke) da abin da yake amfãnin mutãne, da abin da Allah Ya saukar daga sama daga ruwa, sai Ya rãyar da ƙasa da shi a bãyan mutuwarta, kuma Ya wãtsa, a cikinta, daga dukan dabba, kuma da jũyãwar iskõki da girgije hõrarre a tsakãnin sama da ƙasa; haƙĩƙa, akwaiãyõyi ga mutãne mãsu yin hankali.
2|165|Kuma akwai daga mutãne wanda yake riƙon kinãye, baicin Allah, suna son su, kamar son Allah, kuma waɗanda suka yi ĩmãni ne mafiya tsananin so ga Allah. Kuma dã waɗanda suka yi zãlunci, suna ganin lõkacin da zã su ga azãba, da cewa lalle ne ƙarfi ga Allah yake duka, da cẽwa lalle neAllah Mai tsananin azãba ne.
2|166|A lõkacin da waɗanda aka bi suka barranta daga waɗanda suka bi, kuma suka ga azãba, kuma sabubba suka yanke da su.
2|167|Kuma waɗanda suka bi, suka ce: "Dã lalle ne muna da wata kõmãwa (dũniya) sai mu barranta dagagare su kamar yadda suka barranta daga gare mu (dã ba su riƙi kinãyen ba)." Kamar wancan ne Allah ke nũna musu ayyukansu, suna da nadãmõmi a kansu, kuma ba su zama mãsu fita daga wutar ba.
2|168|Yã ku mutãne! Ku ci daga abin da yake a cikin ƙasa, wanda yake halal, mai dãɗi. Kuma kada ku bi zambiyõyin Shaiɗan. Lalle ne shi, gare ku, maƙiyi ne bayyananne.
2|169|Yana umurnin ku ne kawai da mugun aiki da alfãsha, kuma da ku faɗi abin da ba ku sani ba ga Allah.
2|170|Kuma idan aka ce musu: "Ku bi abin da Allah Ya saukar," sai su ce: Ã'a, muna bin abin da muka iske ubanninmu a kansa." Shin, kuma kõ dã ubanninsu bã su hankaltar kõme, kuma bã su shiryuwa?
2|171|Kuma misãlin (mai kiran) waɗanda suka kãfirta kamar misãlin wanda ke yin me! me! ga abin da ba ya ji ne, fãce kira da ƙãra, kurãme, bẽbãye, makafi, sabõda haka bã su hankalta.
2|172|Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku ci ku sha daga mãsu dãɗin abin da Muka azurta ku. Kuma ku gõde wa Allah, idan kun kasance Shi kuke bauta wa.
2|173|Kawai abin da Ya haramta a kanku, mũshe da Jini da nãman alade da abin da aka kurũrũta game da shi ga wanin Allah. To, wanda aka matsã, wanin ɗan tãwãye, kuma banda mai zãlunci, to bãbu laifi a kansa. Lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
2|174|Lalle ne waɗannan da suke ɓõye abin da Allah Ya saukar daga Littãfi, kuma suna sayen kuɗi kaɗan da shi; waɗannan bã su cin kome a cikin cikkunansu fãce wuta, kuma Allah bã zai yi musu magana ba a Rãnar ¡iyãma, kuma bã zai tsarkake su ba, kuma suna da azãba mai raɗaɗi.
2|175|Waɗannan su ne waɗanda suka sayi ɓata da shiriya, kuma azãba da gãfara. To, me ya yi haƙurinsu a kan Wuta!
2|176|Wancan dõmin lalle ne Allah Ya saukar da Littafi da gaskiya, kuma lalle ne waɗanda suka sãɓã a cikin Littãfin, haƙĩƙa, suna a cikin sãɓãni mai nĩsa.
2|177|Bai zama addini ba dõmin kun jũyar da fuskõkinku wajen gabas da yamma, kuma amma addini shi ne ga wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira da malã'iku da Littattafan sama da Annabãwa, kuma ya bãyar da dũkiya, akan yana son ta, ga mai zumunta da marãyu da matalauta da ɗan hanya da mãsu rõƙo, kuma a cikin fansar wuya, kuma ya tsayar da salla, kuma ya bãyar da zakka, da mãsu cika alkawari idan sun ƙulla alkawarin da mãsu haƙuri a cikin tsanani da cũta da lõkacin yãƙi. Waɗannan su ne suka yi gaskiya. Kuma waɗannan su ne mãsu taƙawa.
2|178|Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! An wajabta, a kanku, yin ƙisãsi a cikin kasassu. ɗa da ɗa kuma bãwa da bãwa, kuma mace da mace, to, wanda aka yi rangwamen wani abu gare shi daga ɗan'uwansa to a bi da alhẽri da biya zuwa gare, shi da kyautatãwa. Wancan sauƙaƙewa ne daga Ubangijinku, kuma rahama ce. To, wanda ya yi zãlunci a bãyan wancan, to, yana da azãba mai raɗaɗi.
2|179|Kuma kuna da rãyuwa a cikin ƙisãsi, yã ma'abuta hankula; tsammãninku, zã ku yi taƙawa.
2|180|Kuma an wajabta, a kanku idan mutuwa ta halarci ɗayanku, idan ya bar wata dũkiya, wasiyya dõmin mahaifa da dangi bisa ga abin da aka sani; wajabce a kan mãsu taƙawa.
2|181|To, wanda ya musanya masa a bãyan ya ji shi, to, kawai laifinsa yana a kan waɗanda suke musanya shi. Lalle ne, Allah Mai ji ne, Masani.
2|182|To, wanda ya ji tsõron karkata ko kuwa wani zunubi daga mai wasiyyar, sai ya yi sulhi a tsakãninsu to bãbu laifi a kansa. Lalle ne Allah, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
2|183|Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan waɗanda suke daga gabãninku, tsammãninku, zã ku yi taƙawa,
2|184|Kwanuka ƙidãyayyu. To, wanda ya kasance daga gare ku majinyaci ko kuwa yana a kan tafiya, sai (ya biya) adadi daga wasu kwanuka na dabam. Kuma a kan waɗanda suke yin sa da wahala akwai fansa; ciyar da matalauci, sai dai wanda ya ƙãra alhẽri to, shi ne mafi alhẽri a gare shi. Kuma ku yi azumi (da wahalar) ne mafi alhẽri a gare ku idan kun kasance kuna sani.
2|185|Watan Ramalãna ne wanda aka saukar da Alƙur'ãni a cikinsa yana shiriya ga mutãne da hujjõji bayyanannu daga shiriya da rarrabẽwa. To, wanda ya halarta daga gare ku a watan, sai ya azumce shi, kuma wanda ya kasance majinyaci ko kuwa a kan tafiya, sai ya biya adadi daga wasu kwanuka na dabam. Allah Yana nufin sauƙi gare ku, kuma ba Ya nufin tsanani gare ku, kuma dõmin ku cika adadin, kuma dõmin ku girmama Allah a kan Yã shiryar da ku, kuma tsammãninku, zã ku gõde.
2|186|Kuma idan bãyiNa suka tambaye ka daga gare Ni, to, lalle Ni Makusanci ne. Ina karɓa kiran mai kira idan ya kirã Ni. Sabõda haka su nẽmi karɓawaTa, kuma su yi ĩmãni da Ni: tsammãninsu, su shiryu.
2|187|An halatta a gare ku, a daren azumi, yin jima'i zuwa ga matanku sũ tufa ne a gare ku, kuma kũ tufa ne a gare su, Allah Yã sani lalle ne ku kun kasance kuna yaudarar kanku. Sabõda haka Yã karɓi tũbarku, kuma Yã yãfe muku. To, yanzu ku rungume su kuma ku nẽmi abin da Allah yã rubũta muku. Kuma ku ci kuma ku sha har sĩlĩli fari ya bayyana a gare ku daga sĩlĩli baƙi daga alfijiri, sa'an nan kuma ku cika azumi zuwa ga dare. Kuma kada ku rungume su alhãli kuna mãsu itikãfi a cikin masallãtai. Waɗancan iyãkokin Allah ne: don haka kada ku kusancesu kamar haka ne Allah Yake bayyana ãyõyinSa ga mutãne: tsammãninsu, zã su yi taƙawa.
2|188|Kada ku ci dukiyõyinku a tsakãninku da ƙarya, kuma ku sãdu da ita zuwa ga mahukunta dõmin ku ci wani yanki daga dũkiyõyin mutãne da zunubi alhãli kuwa kũ, kuna sane.
2|189|Kuma suna tambayar ka daga jirajiran wata. Ka ce: "Su lõkatai ne dõmin mutãne da haji, kuma bã addini ba ne ku je wa gidãje daga bãyansu: kuma amma abin da yake addini shi ne wanda ya yi taƙawa. Kuma ku je wa gidãje daga ƙõfõfinsu, kuma ku bi Allah da taƙawa: tsammãninku, ku ci nasara.
2|190|Kuma ku yãƙi waɗanda suke yãƙinku, a cikin hanyar Allah, kuma kada ku yi tsõkana, lalle ne Allah bã Ya son mãsu tsõkana.
2|191|Kuma ku yãƙe su inda kuka sãme su, kuma ku fitar da su daga inda suka fitar da ku. Kuma fitina ita ce mafi tsanani daga kisa. Kuma kada ku yãƙe su a wurin Masallãci Tsararre (Hurumin Makka) fãce fa idan sun yãƙe ku a cikinsa. To, idan sun yãƙe ku, sai ku yãƙe su. Kamar wancan ne sakamakon kãfirai yake.
2|192|Sa'an nan idan sun hanu, to, lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
2|193|Kuma ku yãƙe su har ya zama wata fitina bã zã ta kasance ba, kuma addini ya zama na Allah. Sa'an nan idan sun hanu to bãbu tsõkana fãce a kan azzãlumai.
2|194|Watan alfarma da wani watan alfarma alfarmõmi mãsu dũkar jũna ne. Sabõda haka wanda ya yi tsõkana a kanku, sai ku yi tsokana a kansa da misãlin abin da ya yi tsõkana a kanku. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne, Allah Yana tãre da mãsu taƙawa.
2|195|Kuma ku ciyar a cikin hanyar Allah. Kuma kada ku jefa kanku da hannayenku, zuwa ga halaka. Kuma ku kyautata; lalle ne, Allah Yana son mãsu kyautatãwa.
2|196|Kuma ku cika hajji da umra dõmin Allah. To idan an kange ku, to, ku bãyar da abin da ya sauƙaƙa na hadaya. Kuma kada ku aske kãnunku, sai hadaya ta kai wurinta. To, wanda ya kasance majinyaci daga cikinku, kõ kuwa akwai wata cũta daga kansa (ya yi aski) sai fansa (fidiya) daga azumi ko kuwa sadaka ko kuwa yanka. To, idan kuna cikin aminci to, wanda ya ji dãdi da umra zuwa haji, sai ya biya abin da ya sauƙaƙa daga hadaya, sa'an nan wanda bai sãmu ba, sai azumin yini uku a cikin haji da bakwai idan kun kõma, waɗancan gõma ne cikakku. Wancan yana ga wanda iyãlinsa ba su kasance mazaunan Masallãci Tsararre ba. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cewa Allah Mai tsananin uƙũba ne.
2|197|Hajji watanni ne sanannu. To, wanda ya yi niyyar hajji a cikinsu to bãbu jimã'i kuma bãbu fãsiƙanci, kuma bãbu jãyayya a cikin hajji. Kuma abin da kuka aikata daga alhẽri, Allah Ya san shi. Kuma ku yi guzuri. To, mafi alhẽrin guzuri yin taƙawa. Kuma ku bi Ni da taƙawa, ya ma'abuta hankula.
2|198|Bãbu laifi a kanku ga ku nẽmi falala daga Ubangijinku. Sa'an nan idan kun malãlo daga Arafãt, sai ku yi ta ambatar Allah a wurin Mash'aril Harãmi kuma ku tuna Shi kamar shiriyar da Ya yi muku kuma lalle ne kun kasance a gabãninsa, haƙĩƙa, daga ɓatattu.
2|199|Sa'an nan kuma ku malãlo daga inda mutãne suke malalowa. Kuma ku nemi gafara ga Allah. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
2|200|To, idan kun ƙãre ayyukan hajji, sai ku ambaci Allah kamar ambatarku ga ubanninku, kõ kuwa mafi tsanani ga ambato. To, daga cikin mutãne akwai wanda yake cẽwa: "Ya Ubangjinmu! Ka bã mu a cikin dũniya! Kuma bã ya da wanirabo a cikin Lãhira.
2|201|Kuma daga gare su akwai wanda yake cẽwa: "Yã Ubangijinmu! Ka bã mu mai kyau a cikin dũniya da mai kyau a cikin Lãhira, kuma Ka tsare mana azãbar Wuta!"
2|202|Waɗannan suna da rabo daga abin da suka sanã'anta; kuma Allah Mai gaggãwar sakamako da yawa ne.
2|203|Kuma ku ambaci Allah a cikin kwanuka ƙidayayyu. To, wanda ya yi gaggawa a cikin kwana biyu, to, bãbu laifi a kansa, kuma wanda ya jinkirta, to, bãbu laifi a kansa, ga wanda ya yi taƙawa. Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma ku sani cewa lalle ne kũ, zuwa gare Shi ake tãrã ku.
2|204|Kuma akwai daga mutãne wanda maganarsa tana bã ka sha'awa a cikin rãyuwar dũniya, alhãli yanã shaidar da Allah a kan abin da yake cikin zuciyarsa, kuma shi mai tsananin husũma ne.
2|205|Kuma idan ya jũya sai ya yi gaggawa a cikin ƙasa dõmin ya yi ɓarna a cikinta, kuma ya halaka shũka da 'ya'yan dabbõbi. Kuma Allah bã Ya son ɓarna.
2|206|Kuma idan an ce masa: "Ka ji tsõron Allah," sai girman kai da yin zunubi ya ɗauke shi To abin da yake mai isarsa Jahannama ce. Kuma haƙĩƙa, shimfiɗa tã munana.
2|207|Kuma akwai daga mutãne wanda yake sayar da ransa, dõmin nẽman yardar Allah: KumaAllah Mai tausayi ga bãyi ne.
2|208|Yã ku waɗanda suka yi ĩmani! Ku shiga cikin Musulunci gabã ɗaya; kuma kada ku bi zambiyõyin Shaiɗan; lalle ne shĩ a gare ku maƙiyine, bayyananne.
2|209|To, idan kun karkace daga bayan hujjõji bayyanannu sun zo muku to ku sani cẽwa lalle ne Allah, Mabuwãyi ne, Mai hikima.
2|210|Shin suna jira, fãce dai Allah Ya je musu a cikin wasu inuwõyi na girgije, da malã'iku, kuma an hukunta al'amarin? Kuma zuwa ga Allah al'amurra ake mayar da su.
2|211|Ka tambayi Banĩ Isrã'ila, da yawa Muka bã su daga ãyõyi bayyanannu. Kuma wanda ya musanya ni'imar Allah daga bãyan tã je masa, to, lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne.
2|212|An ƙawata rãyuwar dũniya ga waɗanda suka kãfirta, kuma suna izgili daga waɗanda suka yi ĩmãni, alhãli waɗanda suka yi taƙawa suna bisa gare su, a Rãnar ¡iyãma. Kuma Allah Yana azurta wanda Yake so, bã da lissãfi ba.
2|213|Mutãne sun kasance al'umma guda. Sai Allah Ya aiki annabãwa suna mãsu bãyar da bishãra kuma mãsu gargaɗi; kuma Ya saukar da Littãfi da gaskiya tãre da su dõmin (Littãfin) ya yi hukunci a tsakãnin mutãnen a cikin abin da suka sãɓã wa jũna a cikinsa. kuma bãbu wanda ya sãɓã, a cikinsa, fãce waɗanda aka bai wa shi daga bãyan hujjõji bayyanannu sun je musu dõmin zãlunci a tsakãninsu. Sai Allah Ya shiryar da waɗanda suka yi ĩmani ga abin da suka sãɓã a cikinsa daga gaskiya da izninSa. Kuma Allah Yana shiryar da wanda Yake so, zuwa ga hanya madaidaiciya.
2|214|Ko kuna zaton ku shiga Aljanna kuma tun misãlin waɗanda suka shige daga gabãninku bai zo muku ba? Wahalõli da cũta sun shãfe su, kuma aka tsõratar da su har manzonsu da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi su ce: "Yaushe taimakon Allah zai zo?" To! Lalle ne, taimakon Allah yana kusa!
2|215|Suna tambayar ka mẽne nezã su ciyar. Ka ce: Abin da kuka ciyar daga alhẽri sai ga mahaifa da mafi kusantar dangantaka da marãyu da matalauta da ɗan hanya. Kuma abin da kuka aikata daga alhẽri, to, lalle ne, Allah gare shi Masani ne.
2|216|An wajabta yãƙi a kanku, alhãli kuwa shi abin ƙi ne a gare ku, akwai fãtar cẽwa ku ƙi wani abu, alhãli shi ne mafi alhẽri a gare ku, kumaakwai fãtar cẽwa kuna son wani abu alhãli kuwa shi ne mafi sharri a gare ku. Kuma Allah ne Yake sani, kuma kũ ba ku sani ba.
2|217|Suna tambayar ka game da Watan Alfarma: yin yãki a cikinsa. Ka ce: "Yin yãƙi a cikinsa babban zunubi ne, kuma hani daga hanyar Allah, da kuma kãfirci da Shi, da kuma da Masallaci Tsararre, da Kuma fitar da mutãnensa daga gare shi, shi ne mafi girman zunubi a wurin Allah." Kuma fitina ita ce mafi girma daga kisa. Kuma bã su gushẽwa suna yãƙinku har su mayar da ku daga barin addininku idan za su iya. Kuma wanda ya yi ridda daga gare ku ga barin addininsa har ya mutu alhãli kuwa yana kãfiri, to, waɗannan ayyukansu sun ɓãci a cikin dũniya da Lãhira. Kuma waɗannan abõkan Wuta ne, sũ a cikinta madawwama ne.
2|218|Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, da waɗanda suka yi hijira kuma suka yi jihãdi a cikin hanyar Allah waɗannan suna fãtar (sãmun) rahamar Allah kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
2|219|Suna tambayar ka game da giya da cãcã. Ka ce: "A cikinsu akwai zunubi mai girma da wasu amfãnõni ga mutãne, kuma zunubinsu ne mafi girma daga amfaninsu." Kuma suna tambayar ka mẽne ne zã su ciyar; ka ce: "Abin da ya rage." Kamar wancan ne Allah Yake bayyanawar ãyõyi a gare ku; tsammãninku, kuna tunãni.
2|220|A cikin dũniya da Lãhira. Kuma suna tambayar ka game da marãyu. Ka ce: "Kyautatãwa gare su ne mafi alhẽri, kuma idan kun haɗa da su (wajen abinci), to, 'yan'uwanku ne; kuma Allah Yana sanin mai ɓãtãwa daga mai kyautatãwa. Kuma dã Allah Yã so, dã Ya tsananta muku. Lalle ne Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima.
2|221|Kuma kada ku auri mãtã mushirikai sai sun yi ĩmãni: Kuma lalle ne baiwa mũminaita ce mafi alhẽri daga ɗiya kãfira, kuma kõ da tã bã ku sha'awa. Kuma kada ku aurar wa maza mushirikai sai sun yi ĩmãni, kuma lalle ne bãwa mũmini shi ne mafi alhẽri daga da mushiriki, kuma kõ da yã bã ku sha'awa, waɗannan suna kira ne zuwa ga wuta kuma Allah Yana kira zuwa ga Aljanna da gãfara da izninsa. Kuma Yana bayyana ãyõyinsa ga mutãne; tsammãninsu suna tunãwa.
2|222|Kuma suna tambayar ka game da haila Ka ce: Shi cũta ne. Sabõda haka ku nĩsanci mãta a cikin wurin haila kuma kada ku kusance su sai sun yi tsarki. To, idan sun yi wanka sai ku je musu daga inda Allah Ya umurce ku. Lalle ne Allah Yana son mãsu tũba kuma Yana son mãsu tsarkakẽwa.
2|223|Mãtanku gõnaki ne a gare ku, sabõda haka ku je wa gõnakinku yadda kuka so. Kuma ku gabãtar (da alheri) sabõda kanku, ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cẽwa lalle nekũ mãsu haɗuwa da Shi ne. Kuma ka bãyar da bishãra ga mũminai.
2|224|Kuma kada ku sanya Allah kambu ga rantsuwõyinku dõmin kada ku yi wani alhẽri, kuma ku yi taƙawa, kuma ku yi wani gyara tsakãnin mutãne, kuma Allah Mai jĩ ne, Masani.
2|225|Allah ba Ya kãmã ku da laifi sabõda yãsasshiya a cikin rantsuwõyinku. Kuma amma Yana kama ku sabõda abin da zukãtanku suka sanã'anta. Kuma Allah Mai gãfara ne, Mai haƙuri.
2|226|Ga waɗanda suke yin rantsuwa daga matansu akwai jinkirin watã huɗu. To, idan sun kõma, to, lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
2|227|Kuma idan sun yi niyyar saki, to, lalle ne, Allah Mai ji ne, Masani.
2|228|Kuma mãtã waɗanda aka saki aurensu, suna jinkiri da kansu tsarki uku. Kuma bã ya halatta a gare su, su ɓõye abin da Allah Ya halitta a cikin mahaifunsu, idan sun kasance suna yin ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Kuma mazan aurensu su ne mafiya haƙƙi ga mayar da su a cikin wancan, idan sun yi nufin gyãrawa. Kuma sũ mãtan suna da kamar abin da yake a kansu, yadda aka sani. Kuma maza suna da wata daraja a kansu (su mãtan). Kuma Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima.
2|229|Saki sau biyu yake, sai a riƙa da alh ẽri, ko kuwa a sallama bisa kyautatãwa. Kuma ba ya halatta a gare ku (maza) ku karɓe wani abu daga abin da kuka bã su, fãce fa idan su (ma'auran) na tsõron bã zã su tsayar da iyãkõkin Allah ba, Idan kun (danginsu) ji tsõron bã zã su tsayar da iyãkõkin Allah ba, to, bãbu laifi a kansu a cikin abin da ta yi fansa da shi. Waɗancan iyãkõkin Allah ne sabõda haka kada ku kẽtare su. Kuma wanda ya ƙẽtare iyãkõkin Allah, to waɗannan su ne azzãlumai.
2|230|Sa'an nan idan ya sake ta (na uku), to, bã ta halatta a gare shi, daga bãya, sai tã yi jima'i da wani miji waninsa. Sa'an nan idan (sãbon mijin, watau na biyu) ya sake ta, to, bãbu laifi a kansu ga su kõma wa (auren) jũna, idan sun (mijin farko da matar) yi zaton cẽwa zã su tsayar da iyãkõkin Allah, kuma waɗancan dõkõkin Allah ne Yana bayyana su ga mutãne waɗanda suke sani.
2|231|Kuma idan kun saki mãta, sa'an nan suka isa ga ajalinsu (iddarsu), sai ku riƙe su da alhẽri ko ku sallame su da alhẽri, kuma kada ku riƙe su a kan cũtarwa dõmin ta tsawaita idda. Kuma wanda ya aikata wancan, to, haƙĩƙa, yã zãlunci kansa. Kuma kada ku riƙi ãyõyin Allah da izgili. Kuma ku tuna ni'imar Allah da abin da Ya saukar a kanku na Littãfi da hikima. Yana yi muku wa'azi da shi. Kuma ku bi Allah da takawa kuma ku sani cewa lalle ne Allah ga dukan kõme Masani ne.
2|232|Kuma idan kuka saki mãta, har suka isa ga ajalinsu (iddarsu), to, kada ku (waliyyansu) hana su, su auri mazansu (da suka sake su) idan sun yarda da jũna a tsakãninsu (tsõhon miji da tsõhuwar mãta) da alhẽri. Wancan ana yin wa'azi da shi ga wanda ya kasance daga gare ku yana ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Wancan ne mafi mutunci a gare ku, kuma mafi tsarki. Kuma Allah Yana sani, kuma kũ ba ku sani ba.
2|233|Kuma mãsu haifuwa (sakakku) suna shãyar da abin haifuwarsu shẽkara biyu cikakku ga wanda ya yi nufin ya cika shãyarwa. Kuma ciyar da su da tufãtar da su yana a kan wanda aka haifar masa da alhẽri. Bã a kallafa wa rai fãce iyãwarsa. Bã a cũtar da uwa game da ɗanta, kuma bã a cũtar da uba game da ɗansa, kuma a kan magãji akwai misãlin wancan. To, idan suka yi nufin yãye, a kan yardatayya daga gare su, da shãwartar jũna, to bãbu laifi a kansu. Kuma idan, kun yi nufin ku bãyar da ɗiyanku shãyarwa, to, bãbu laifi a kanku idan kun mĩƙa abin da kukazo da shi bisa al'ãda. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne Allah, ga abin da kuke aikatawa, Mai gani ne.
2|234|Kuma waɗanda suke mutuwa daga gare ku suna barin mãtan aure, mãtan suna jinkiri da kansu wata huɗu da kwãna goma. To, idan sun isa ga ajalinsu, to, bãbu laifi a kanku a cikin abin da suka aikata game da kansu ga al'ãda. Kuma Allah ga abin da kuke aikatawa Masani ne.
2|235|Kuma bãbu laifi a kanku a cikin abin da kuka gitta da shi daga nẽman auren mãtãko kuwa kuka ɓõye a cikin zukatanku. Allah Ya san cẽwa lalle ne ku za ku ambata musu (shi). Kuma amma kada ku yi wa jũna alkawari da shia ɓõye, fãce dai ku faɗi magana sananniya. Kuma kada ku ƙulla niyyar daurin auren sai littãfin (idda) ya kai ga ajalinsa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne Allah Yana sanin abin da yake cikin zukatanku, sabõda haka ku ji tsõronsa. Kuma ku sani cewa Allah Mai gãfara ne, Mai haƙuri.
2|236|Kuma bãbu laifi a kanku idan kun saki mãtã matuƙar ba ku shãfe su ba, kuma ba ku yanka musu sadãki ba. Kuma ku bã su kyautar dãɗaɗãwa, a kan mawadãci gwargwadonsa, kuma a kan maƙuntaci gwargwadonsa; dõmin dãɗaɗrwa, da alhẽri, wãjibi ne a kan mãsu kyautatãwa.
2|237|Kuma idan kuka sake su daga gabãnin ku shãfe su, alhãli kuwa kun yanka musu sadãki, to, rabin abin da kuka yanka fãce idan sun yãfe, kõ wanda ɗaurin auren yake ga hannunsa ya yãfe. Kuma ku yãfe ɗin ne mafi kusa da taƙawa. Kuma kada ku manta da falala a tsakãninku. Lalle ne Allah ga abin da kuke aikatãwa Mai gani ne.
2|238|Ku tsare lõkatai a kan sallõli da salla mafificiya. Kuma ku tsayu kuna mãsu ƙanƙan da kai ga Allah.
2|239|To, idan kun ji tsõro, to (ku dai yi salla gwargwadon hali) da tafiya ƙasa kõ kuwa a kan dabbobi. Sa'an nan idan kun amince sai ku ambaci Allah, kamar yadda Ya nũna muku abin da ba ku kasance kuna sani ba.
2|240|Kuma waɗanda suke mutuwa daga gare ku, alhãli suna barin mãtan aure, wasiyya ga mãtan aurensu da dãɗaɗãwa zuwa ga shekara guda bãbu fitarwa, to, idan sun fita to bãbu laifi a kanku a cikin abin da suka aikata game da kansu daga abin da aka sani, kuma Allah Mabuwayi ne, Mai hikima.
2|241|Kuma waɗanda aka saki suna da dãɗaɗãwa gwargwadon hãli, wajabce a kan mãsu taƙawa.
2|242|Kamar wancan ne Allah Yake bayyana muku ãyõyinSa; tsammãninku, kuna hankalta.
2|243|Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda suka fita daga gidãjensu, alhãli kuwa sũ dubbai ne, dõmin tsõron mutuwa? Sai Allah Ya ce musu: "Ku mutu." Sa'an nan kuma Ya rãyar da su, lalle ne Allah, haƙĩƙa Ma'abũcin falala a kan mutãne ne, kuma amma mafi yawan mutãne bã su gõdẽwa.
2|244|Kuma ku yi yãƙi a cikin hanyar Allah, kuma ku sani cẽwa lalle ne, Allah Mai jĩ ne, Masani.
2|245|Wãne ne wanda zai bai wa Allah rance, rance mai kyau, dõmin Ya riɓanya masa, riɓanyãwa mai yawa? Kuma Allah Shi ne ke damƙewa, kuma yana shimfiɗawa, kuma zuwa a gare Shi ake mayar da ku.
2|246|Shin, ba ka gani ba zuwa ga wasu mashãwarta daga Bani Isrã'ĩla daga bãyan Mũsã, a lõkacinda suka ce ga wani annabi nãsu: "Naɗã mana sarki, mu yi yãƙi a cikin hanyar Allah." Ya ce: "Ashe, akwai tsammãninku idan an wajabta yãƙi a kanku cẽwa bã zã ku yi yãƙin ba?" Suka ce: "Kuma mẽne ne a gare mu, ba zã mu yi yãƙi ba, a cikin hanyar Allah, alhãli kuwa, haƙiƙa, an fitar da mu daga gidãjenmu da ɗiyanmu?" To, a lõkacin da aka wajabta yãƙin a kansu, suka jũya, sai kaɗan daga gare su. Kuma Allah Masani ne ga azzãlumai.
2|247|Kuma annabinsu ya ce musu: "Lalle ne, Allah ya naɗa muku ¦ãlũta ya zama sarki." Suka ce: "Yãya ne sarauta zã ta kasance a gare shi, a kanmu, alhãli kuwa mũ ne mafi cancanta da sarauta daga gare shi, kuma ba a bã shi wata wadata ba daga dũkiya?" Ya ce: "Lalle ne, Allah Yã zãɓe shi a kanku, kuma Ya ƙãra masa yalwa a cikin ilmi da jiki. Kuma Allah Yana bãyar da mulkinSa ga wanda Yake so, kuma Allah Mawadaci ne, Masani.
2|248|Kuma annabinsu ya ce musu: "Lalle ne alãmar mulkinSa ita ce akwatin nan ya zo muku, a cikinsa akwai natsuwa daga Ubangijinku da sauran kaya daga abin da Gidan Mũsã da Gidan Hãrũna suka bari malã'iku suna ɗaukarsa. Lalle ne a cikin wancan akwai alãma a gare ku (ta naɗin ¦ãlũta daga Allah ne) idan kun kasance mãsu ĩmãni."
2|249|A lõkacin da ¦ãlũta ya fita da rundunõnin, ya ce: "Lalle ne Allah Mai jarrabarku ne da wani kõgi. To, wanda ya sha daga gare shi, to, ba shi daga gare ni, kuma wanda bai ɗanɗane shi ba to lalle ne shi, yana daga gare ni, fãce, wanda ya kamfata, kamfata guda da hannunsa." Sai suka sha daga gare shi, fãce kaɗan daga gare su. To, a lõkacin da (¦ãlũta) ya ƙẽtare shi, shi da waɗanda suka yi ĩmani tãre da shi, (sai waɗanda suka sha) suka ce: "Babu ĩko a gare mu yau game da Jãlũta da rundunõninsa."Waɗanda suka tabbata cẽwa lalle sũ mãsu gamuwa ne da Allah, suka ce: "Da yawa ƙungiya kaɗan ta rinjayi wata ƙungiya mai yawa da iznin Allah, kuma Allah Yana tãre da mãsu haƙuri."
2|250|Kuma a lõkacin da suka bayyana ga Jãlũta da rundunoninsa, suka ce: "Yã Ubangijinmu! Ka zuba haƙuri a kanmu kuma Ka tabbatar da sãwayenmu, kuma Ka taimake mu a kan mutãnen nan kãfirai."
2|251|Sai suka karya su da iznin Allah. Kuma Dãwudu ya kashe Jãlũta, kuma Allah Ya bã shi mulki da hikima kuma Ya sanar da shi daga abin da Yake so. Kuma bã dõmin tunkuɗẽwar Allah ga mutãne sãshensu da sãshe ba lalle ne dã ƙasa tã ɓãci; kuma amma Allah Ma'abũcin falala ne a kan tãlikai.
2|252|Waɗancan ayõyin Allah ne: Muna karanta su a kanka da gaskiya: Kuma lalle ne kai, hakĩka, kana daga manzanni.
2|253|Waɗancan manzannin Mun fĩfĩta sãshensu a kan sãshe: Daga cikinsu akwai wanda Allah Ya yi masa magana; kuma Ya ɗaukaka sãshensu da darajõji; kuma Muka bai wa Ĩsã dan Maryama hujjõji bayyanannu, kuma Muka ƙarfafã shi da Rũhi mai tsarki. Kuma dã Allah Yã so dã waɗanda suke daga bãyansu, bã zã su yi yãƙi ba, daga bãyan hujjõji bayyanannu sun je musu. Kuma amma sun sãɓa wa jũna, sabõda haka daga cikinsu akwai wanda ya yi ĩmãni, kuma daga cikin su akwai wanda ya kãfirta. Kuma dã Allah Yã so dã bã zã su yãƙi jũna ba, kuma amma Allah Yana aikata abin da Yake nufi.
2|254|Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku ciyar daga abin da Muka azurta ku daga gabãnin wani yini ya zo bãbu ciniki a cikinsa kuma bãbu abũta, kuma bãbu cẽto, kuma kãfirai sũ ne azzãlumai.
2|255|Allah, bãbu wani Ubangiji fãce Shi, Rãyayye, Mai tsayuwa da kõme, gyangyaɗi bã ya kãma Shi, kuma barci bã ya kãma Shi, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa. Wane ne wanda yake yin cẽto a wurinSa, fãce da izninSa? Yana sanin abin da yake a gaba gare su da abin da yake a bãyansu. Kuma bã su kẽwayẽwa da kõme daga ilminSa, fãce da abin da Ya so. KursiyyunSa ya yalwaci sammai da ƙasa. Kuma tsare su bã ya nauyayarSa. Kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma.
2|256|Bãbu tĩlastãwa a cikin addini, haƙĩƙa shiriya tã bayyana daga ɓata; Sabõda haka wanda ya kãfirta da ¦ãgũta kuma ya yi ĩmãni da Allah, to, haƙĩƙa, yã yi riƙo ga igiya amintacciya, bãbu yankẽwa agare ta. Kuma Allah Mai ji ne, Masani.
2|257|Allah Shi ne Masõyin waɗanda suka yi ĩmãni; Yana fitar da su daga duffai zuwa ga haske, kuma waɗanda suka kãfirta, masõyansu ¦ãgũtu ne; suna fitar da su daga haske zuwa ga duffai. Waɗannan abokan Wuta ne, sũ a cikinta madawwama ne.
2|258|Shin, ba ka gani ba zuwa ga wanda ya yi hujjatayya da Ibrãhĩm a cikin (al'amarin) Ubangijinsa dõmin Allah Yã bã shi mulki, a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: "Ubangijina Shi ne Wanda Yake rãyawa kuma Yana matarwa." Ya ce: "Nĩ ina rãyarwa kuma ina matarwa." Ibrãhĩm ya ce: "To, lalle ne Allah Yana zuwa da rana daga gabas: To, ka zo da ita daga yamma." Sai aka ɗimautar da wanda yakãfirta. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne azzãlumai.
2|259|Kõ kuwa wanda ya shũɗe a kan wata alƙarya, alhãli kuwa tana wõfintacciya a kan gadãjen rẽsunanta. Ya ce: "Yaya Allah zai rãyar da wannan a bãyan mutuwarta." Sai Allah Ya matar da shi, shẽkara ɗari; sa'an nankuma ya tãyar da shi. Ya ce: "Nawa ka zauna?" Ya ce: "Na zauna yini ɗaya ko kuwa rabin yini." Ya ce: "A'a kã zauna shẽkara ɗari." To, ka dũba zuwa ga abincinka, da abin shanka, (kõwanensu) bai sãke ba, kuma ka dũba zuwa ga jãkinka, kuma dõmin Mu sanya ka wata ãyã ga mutãne. Kuma ka duba zuwa ga ƙasũsuwa yadda Muke mõtsarda su sa'an nan kuma Mu tufãtar da su, da nãma", To, a lõkacin da (abin) ya bayyana a gare shi, ya ce: "Ina sanin cẽwa lalle Allah a kan dukan kõme Mai ĩkõn yi ne."
2|260|Kuma a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: "Ya Ubangijina! Ka nũna mini yadda Kake rãyar da matattu." Ya ce: "Shin, kuma ba ka yi ĩmãni ba?" Ya ce: "Na'am! Kuma amma dõmin zũciyãta, ta natsu." Ya ce: "To ka riƙi huɗu daga tsuntsãye, ka karkatar da su zuwa gare ka, ka yanka su, sa'an nan kuma ka sanya juzu'i daga gare su a kan kõwane dũtse, sa'an nan kuma ka kira su zã su zo maka gudãne. Kuma ka sani cẽwa lalle Allah Mabuwãyi ne, Masani."
2|261|Sifar waɗanda suke ciyar da dũkiyõyinsu a cikin hanyar Allah, kamar sifar ƙwãyã ce wadda ta tsirar da zangarniya bakwai, a cikin kõwace zangarniya akwai ƙwãya ɗari. Kuma Allah Yana riɓinyawa ga wanda Ya so. Kuma Allah Mawadãci ne, Masani.
2|262|Waɗanda suke ciyar da dũkiyõyinsu a cikin hanyar Allah, sa'an nan kuma bã su biyar wa abin da suka ciyar ɗin da gõri, ko cũta, suna da sakamakonsu a wurin ubangijinsu, kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna baƙin ciki ba.
2|263|Magana mai kyau da gãfartawa su ne mafi alhẽri daga sadaka wadda wata cũtarwa take biyar ta. Kuma Allah Wadatacce ne, Mai haƙuri.
2|264|Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku ɓãta sadakõkinku da gõri da cũtarwa, kamar wanda yake ciyar da dũkiyarsa dõmin nũna wa mutãne, kuma bã ya yin ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. To, abin da yake misãlinsa, kamar falalen dũtse ne, a kansa akwai turɓãya, sai wãbilin hadari ya sãme shi, sai ya bar shi ƙanƙara. Bã su iya amfani da kõme daga abin da suka sanã'anta. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne kãfirai.
2|265|Kuma sifar waɗanda suke ciyar da dũkiyarsu dõmin nẽman yardõjin Allah, kuma da tabbatarwa daga kansu, kamar misãlin lambu ne a jigãwa wadda wãbilin hadari ya sãmu, sai ta bãyar da amfãninta ninki biyu To, idan wãbili bai sãme ta ba, sai yayyafi (ya ishe ta). Kuma Allah ga abin da kuke aikatawa Mai gani ne.
2|266|Shin ɗayanku nã son cẽwa wani lambu ya kasance a gare shi daga dabĩnai da inabõbi' marẽmari suna gudãna daga ƙarƙashinsa, yana da, a cikinsa daga kõwane 'ya'yan itãce, kuma tsũfa ya sãme shi, alhãli kuwa yana da zũriyya masu rauni sai gũguwa wadda take a cikinta akwai wuta, ta sãme shi, har ta ƙõne? Kamar wancan ne Allah Yana bayyanãwar ãyõyi a gare ku, tsammãninku kuna tunãni.
2|267|Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku ciyar daga mai kyaun abin da kuka sanã'anta, kuma daga abin da Muka fitar sabõda ku daga ƙasa, kuma kada ku yi nufin mummuna ya zama daga gare shi ne kuke ciyarwa, alhãli kuwa ba ku zama mãsu karɓarsa ba fãce kun runtse ido a cikinsa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne, Allah Mawadãci ne, Gõdadde.
2|268|Shaiɗan yana yi muku alƙawarin talauci, kuma yana umurnin ku da alfasha, kuma Allah Yana yi muku alƙawarin gãfara daga gare shi da ƙãri, kuma Allah Mawadãci ne, Masani.
2|269|Yana bãyar da hikima (ga fahimtar gaskiyar abubuwa) ga wanda Yake so. Kuma wanda aka bai wa hikima to lalle ne an bã shi alhẽri mai yawa. Kuma bãbu mai tunãni fãce ma'abuta hankula.
2|270|Kuma abin da kuka ciyar daga ciyarwa, kõ kuka cika alwãshi daga wani bãkance, to, lalle ne, Allah Yana sanin sa. Kuma azzãlumai bã su da wasu mataimaka.
2|271|Idan kun nũna sadakõki to, yana da kyau ƙwarai kuma idan kuka ɓõye su kuma kuka je da su ga matalauta, to shi ne mafi alhẽri a gareku, kuma Yana kankarẽwa, daga barinku, daga miyãgun ayyukanku. Kuma Allah ga abin da kuke aikatawa Masani ne.
2|272|Shiryar da su bã ya a kanka, kuma amma Allah Shi ne Yake shiryar da wanda Yake so, kuma abin da kuka ciyar daga alhẽri, to, dõmin kanku ne, kuma bã ku ciyarwa, fãce dõmin nẽman yardar Allah, kuma abin da kuke ciyarwa daga alhẽri zã a cika lãdarsa zuwa gare ku, alhãli kuwa kũ bã a zãluntarku.
2|273|(Ciyarwar a yĩ ta) ga matalautan nan waɗanda aka tsare a cikin hanyar Allah, ba su iya tafiyar fatauci a cikin ƙasa, jãhilin hãlinsu yana zaton su wadãtattu sabõda kãmun kai kana sanin su da alãmarsu, ba su rõƙon mutãne da nãcẽwa. Kuma abin da kuka ciyar daga alhẽri, to, lalle Allah gare shi Masani ne.
2|274|Waɗanda suke ciyar da dukiyõyinsu, a dare da yini, ɓõye da bayyane, to suna da sakamakonsu a wurin Ubangijinsu. Kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna baƙin ciki ba.
2|275|Wadanda suke cin ribã ba su tashi, fãce kamar yadda wanda da Shaiɗan yake ɗimautarwa daga shafa yake tashi. Wancan, dõmin lalle ne sun ce: "Ciniki kamar riba yake."Kuma Allah Ya halatta ciniki kuma Ya haramta riba. To, wanda wa'azi daga Ubangijinsa, ya je masa, sa'an nan ya hanu, to yana da abin da ya shige, kuma al'amarinsa (ana wakkala shi) zuwa ga Allah. Kuma wanda ya kõma, to, waɗannan sũ ne abõkan Wuta, sũ a cikinta madawwama ne.
2|276|Allah Yana shãfe albarkar riba, kuma Yana ƙãra sadakõki. Kuma Allah bã Ya son dukan mai yawan kãfirci, mai zunubi.
2|277|Lalle ne, waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka tsayar da salla, kuma suka bãyar da zakka, suna da sakamakonsu a wurin Ubangijinsu, kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna yin baƙin ciki ba.
2|278|Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa kuma ku bar abin da ya rage daga riba, idan kun kasance mãsu ĩmãni.
2|279|To, idan ba ku aikata ba to, ku sani fa da akwai yãƙi daga Allah da ManzonSa. Kuma idan kun tũba to kuna da asalin dũkiyõyinku, bã ku zãlunta, kuma bã a zãluntar ku.
2|280|Kuma idan ma'abucin wahala ya kasance (mawahalci) to, jinkirtãwa ake yi zuwa ga sauƙin al'amarinsa, kuma dã kun yi sadaka, shi ne mafi alhẽri a gare ku, idan kun kasance kuna sani.
2|281|Kuma ku ji tsõron wani yini wanda ake mayar da ku a cikinsa zuwa ga Allah, sa'an nan kuma a cika wa kõwane rai abin da ya sanã'anta, kuma sũ bã a zãluntar su.
2|282|Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun yi mu'ãmalar bãyar da bãshi zuwa ga wani ajali ambatacce, sai ku rubũta shi. Kuma wani marubuci ya yi rubũtu a tsakaninku da ãdalci. Kuma kada marubũci ya ki rubũtãwa, kamar yadda Allah Ya sanar da shi, sai ya rubũta. Kuma wanda bãshin yake a kansa sai ya yi shibta, kuma ya ji tsõron Allah, Ubangijinsa, da taƙawa, kuma kada ya rage wani abu daga gare shi. To, idan wanda bãshin yake a kansa yã kasance wãwã ne kõ kuwa rarrauna, kõ kuwa shi bã ya iya shibta, to, sai waliyyinsa ya yi shibtar da ãdalci. Kuma ku shaidar da shaidu biyu daga mazanku, to, idan ba su zama maza biyu ba, to, namiji guda da mãtã biyu, daga waɗanda kuke yarda da su daga shaidun dõmin mantuwar ɗayansu, sai gudarsu ta mazãkũtar da ɗayar. Kuma kada shaidun su ƙi, idan an kira su. Kuma kada ku ƙõsa ga rubũta shi, ƙarami ya kasance kõ babba, zuwa ajalinsa. Wancan ne mafi ãdalci a wurin Allah kuma mafi tsayuwa ga shaida, kuma mafi kusa ga rashin shakkarku. Sai idan ya kasance fatauci ne halartacce wanda kuke gẽwayarwa da shi hannu da hannu a tsakãninku to bãbu laifi a kanku, ya zama ba ku rubũta shi ba. Kuma ku shaidar idan kun yi sayayya. Kuma kada a wahalarda marubuci, kuma kada a wahalar da shaidu kuma idan kun aikata to, lalle ne, shi fãsiƙanci ne game da ku. Kumaku bi Allah da takƙawa, kuma Allah Ya sanar da ku. Kuma Allah ga dukan kõme Masani ne.
2|283|Kuma idan kun kasance a kan tafiya, kuma ba ku sami marubũci ba, to, a bãyar da jingina karɓaɓɓiya (ga hannu). To, idan sãshenku ya amince wa sãshe, to, wanda aka amincẽ wannan sai ya bãyar da amãnarsa, kuma ya bi Allah, Ubangijinsa, da taƙawa. Kuma kada ku ɓõye shaida, kuma wanda ya ɓõye ta, to, shi mai zunubin zũciyarsa ne. KumaAllah ga abin da kuke aikatãwa Masani ne.
2|284|Allah ne, da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, kuma idan kun bayyana abin da yake a cikin zukatanku (na shaida), ko kuka ɓõye shi, Allah zai bincike ku da shi, sa'an nan Ya yi gãfara ga wanda Yake so, kuma Ya azabta wanda Yake so. Kuma Allah a kan dukan kõme Mai ĩkon yi ne.
2|285|Manzon Allah yã yi ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare shi daga Ubangijinsa, da mũminai. Kõwanensu yã yi ĩmãni da Allah, da mala'ikunSa, da littattafanSa, da manzanninSa. Bã mu rarrabẽwa a tsakãnin daya daga manzanninSa. Kuma (mũminai) suka ce: "Mun ji kuma mun yi dã'a; (Muna nẽman) gãfararKa, yã Ubangijinmu, kuma zuwa a gare Ka makõma take "
2|286|Allah ba Ya kallafa wa rai fãce ikon yinsa, yana da lãdar abin da ya tsirfanta, kuma a kansa akwai zunubin abin da ya yi ta aikatãwa: "Yã Ubangijinmu! Kada Ka kãmã mu, idan mun yi mantuwa, ko kuma mun yi kuskure. Yã Ubangijinmu! Kuma kada Ka aza nauyi a kanmu, kamar yadda Ka aza shi a kan waɗanda suke a gabãninmu. Yã Ubangijinmu! Kada Ka sanya mu ɗaukar abin da bãbu ĩko gare mu da shi. Kuma Ka yãfe daga gare mu, kuma Ka gãfarta mana, kuma Ka yi jin ƙai gare mu. Kai ne Majibincinmu, sabõda haka Ka taimake mu a kan mutãnen nan kãfirai."
3|1|A. L̃. M̃.
3|2|Allah, bãbu wani abin bautawa fãce Shi, Rãyayye Mai tsayuwa da kõme.
3|3|Yã sassaukar da Littãfi a gare ka da gaskiya, yana mai gaskatãwa ga abin da ke gaba gare shi, kuma Allah Yã saukar da Attaura da Linjĩlã.
3|4|A gabãni, suna shiryar da mutãne, kuma Ya saukar da littattafai mãsu rarrabẽwa. Lalle ne waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Allah, suna da azãba mai tsanani. Kuma Allah Mabuwayi ne, Ma'abucin azãbar rãmuwa.
3|5|Lalle ne, Allah bãbu wani abin da ke ɓõyuwa gare Shi a cikin ƙasa, kuma bãbu a cikin sama.
3|6|Shi ne wanda Yake suranta ku a cikin mahaifu yadda Yake so. Bãbu abin bautãwa fãce Shi Mabuwãyi, Mai hikima.
3|7|Shi ne wanda ya saukar da Littãfi a gare ka, daga cikinsa akwai ãyõyi bayyanannu, su ne mafi yawan Littãfin, da wasu mãsu kamã da jũna. To, amma waɗanda yake a cikin zukãtansu akwai karkata sai suna bin abin da yake da kamã da jũna daga gare shi, dõmin nẽman yin fitina da tãwĩlinsa. Kuma bãbu wanda ya san tãwĩlinsafãce Allah. Kuma matabbata a cikin ilmi sunã cẽwa: "Mun yi ĩmãni da Shi; dukkansa daga wurin Ubangijinmu yake." Kuma bãbu mai tunãni fãce ma'abũta hankula.
3|8|Yã Ubangijinmu! Kada Ka karkatar da zukãtanmu bãyan har Kã shiryar da mu, kuma Ka bã mu rahama daga gunKa. Lalle ne, Kai, Kai ne Mai yawan kyauta.
3|9|"Yã Ubangijimu! Lalle ne Kai, Mai tãra mutãne ne dõmin wani yini wanda bãbu shakka a gare shi, Lalle ne Allah bã Ya sãɓãwar lõkacin alkawari."
3|10|Lalle ne waɗanda suka kãfirta, dũkiyõyinsu bã su tunkuɗe musu kõme daga Allah, kuma 'ya'yansu bã su tunkuɗẽwa, kuma waɗannan, sũ ne makãmashin wuta.
3|11|Kamar ɗabi'ar mutãnen Fir'auna da waɗanda ke a gabãninsu, sun ƙaryata ãyõyinMu, sai Allah Ya kãmã su sabõda zunubansu, kuma Allah Mai tsananin uƙũba ne.
3|12|Ka ce wa waɗanda suka kãfirta: "Za a rinjãye ku, kuma a tãraku zuwa Jahannama, kuma shimfiɗar tã mũnana!
3|13|"Lalle ne wata ãyã tã kasance a gare ku a cikin ƙungiyõyi biyu da suka haɗu; ƙungiya guda tana yãƙi a cikin hanyar Allah, da wata kãfira, suna ganin su ninki biyu nãsu, a ganin ido. Kuma Allah Yana ƙarfafa wanda Yake so da taimakonSa. Lalle ne a cikin wannan, hakĩƙa, akwai abin kula ga maabũta basĩra.
3|14|An ƙawata wa mutãne son sha'awõyi daga mãtã da ɗiya da dũkiyõyi abũbuwan tãrãwa daga zinariya da azurfa, da dawãki kiwãtattu da dabbõbin ci da hatsi. Wannan shi ne dãɗin rãyuwar dũniya. Kuma Allah a wurinsa kyakkyãwar makõma take.
3|15|Ka ce: Shin kuma, in gaya muku mafi alhẽri daga wannan? Akwai gidãjen Aljanna a wurin Ubangiji sabõda waɗanda suka bi Shi da taƙawa, kõguna suna gudãna daga ƙarƙashinsu, suna madawwama a cikinsu, da mãtan aure tsarkakakku, da yarda daga Allah. Kuma Allah Mai gani ne ga bãyinSa.
3|16|Waɗanda suke cẽwa: "Ya Ubangijinmu! Lalle ne mu, mun yi ĩmãni, sai Ka gãfarta mana zunubanmu kuma Ka tsare mu daga azãbar wuta."
3|17|Mãsu haƙuri, da mãsu gaskiya, da mãsu ƙanƙan da kai, da mãsu ciyarwa da mãsu istingifari a lõkutan asuba.
3|18|Allah Ya shaida cẽwa: Lalle ne bãbu abin bautãwa fãce Shi kuma malãiku da ma'abũta ilmi sun shaida, yana tsaye da ãdalci, bãbu abin bautãwa face Shi, Mabuwãyi, Mai hikima.
3|19|Lalle ne, addini a wurin Allah, Shi ne Musulunci. Kuma waɗanda aka bai wa Littafi ba su sãɓã ba, fãce a bãyan ilmi ya je musu, bisa zãlunci a tsakãninsu. Kuma wanda ya kãfirta da ãyõyin Allah, to, lalle ne Allah Mai gaugãwar sakamako ne.
3|20|To, idan sun yi musu da kai, sai ka ce: "Nã sallama fuskata ga Allah, kuma wanda ya bi ni (haka)." Kuma ka ce wa waɗanda aka bai wa littãfi da Ummiyyai: "Shin kun sallama?" To, idan sun sallama, haƙĩƙa, sun shiryu kuma idan sun jũya, to, kawai abinda ke kanka, shi ne iyarwa. Kuma Allah Mai gani ne ga bãyinSa.
3|21|Lalle ne waɗanda suke kãfirta da ãyõyin Allah, kuma suna kashe Annabãwa bã da wani hakki ba, kuma suna kashe waɗanda ke umurni da yin ãdalci daga mutãne, to, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi.
3|22|Waɗannan ne waɗanda ayyukansu suka ɓãci a cikin dũniya da Lãhira, kuma bã su da wasu mataimaka.
3|23|Shin, ba ka ga waɗanda aka bai wa rabo daga littãfi ba ana kiran su zuwa ga Littãfin Allah dõmin ya yi hukunci a tsakãninsu sa'an nan wata ƙungiya daga cikinsu ta jũya bãya, kuma sunã mãsu bijirẽwa?
3|24|Wannan kuwa, dõmin lalle ne su sun ce: "Wutã bã zã ta shãfe mu ba, fãce a 'yan kwãnaki ƙidãyayyu." Kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa na ƙarya ya rũɗẽ su a cikin addininsu.
3|25|To, yãya idan Mun tãra su a yini wanda bãbu shakka a cikinsa, kuma aka cikã wa kõwane rai sakamakon abin da ya tsirfanta, alhãli kuwa, sũ bã zã a zãlunce su ba?
3|26|Ka ce: "Yã Allah Mamallakin mulki, Kanã bayar da mulki ga wanda Kake so, Kanã zãre mulki daga wanda Kake so, kuma Kanã buwãyar da wanda Kake so, kuma Kanã ƙasƙantar da wanda Kake so, ga hannunKa alhẽri yake. Lalle ne Kai, a kan kõwane abu, Mai ĩkon yi ne."
3|27|"Kanã shigar da dare a cikin yini, kuma Kanã shigar da yini a cikin dare, kuma Kana fitar da mai rai daga mamaci, kuma Kanã fitar da mamaci daga mai rai, kuma Kanã azurta wanda Kake so bã da lissafi ba."
3|28|Kada mũminai su riƙi kãfirai masõya, baicin mũminai. Kuma wanda ya yi wannan, to, bai zama a cikin kõme ba daga Allah, fãce fa dõmin ku yi tsaro daga gare su da 'yar kãriya. Kuma Allah yana tsõratar da ku kanSa. Kuma zuwa ga Allah makõma take.
3|29|Ka ce: "Idan kun ɓõye abin da ke a cikin ƙirãzanku, kõ kuwa kun bayyana shi, Allah Yana sanin sa. Kuma Yana sanin abin da ke a cikin sammai da ƙasa. Kuma Allah a kan kõwane abu Mai ĩkon yi ne."
3|30|A Rãnar da kõwane rai yake sãmun abin da ya aikata daga alhẽri, a halarce, da kuma abin da ya aikata daga sharri, alhãli yana gũrin, dã dai lalle a ce akwai fage mai nĩsa a tsakãninsa da abin daya aikata na sharrin! Kuma Allah Yanã tsõratar da kũ kanSa. Kuma Allah Mai tausayi ne ga bãyinSa.
3|31|Ka ce: "Idan kun kasance kunã son Allah to, ku bĩ ni, Allah Ya sõ ku, kuma Ya gãfarta muku zunubanku. Kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."
3|32|Ka ce: "Ku yi ɗã'a ga Allah da Manzo." To, amma idan sun jũya bãya, to, lalle ne Allah bã Ya son kãfirai.
3|33|Lalle ne Allah Yã zãɓi Ãdama da Nũhu da Gidan Ibrãhĩma da Gidan Imrãna a kan tãlikai.
3|34|Zuriyya ce sãshensu daga sãshe, kuma Allah Mai ji ne, Masani.
3|35|A lõkacin da mãtar Imrãna ta ce: "Ya Ubangijina! Lalle ni, nã yi bãkancen abin da ke cikin cikĩna gare Ka; ya zama 'yantacce, sai Ka karɓa daga gare ni. Lalle ne Kai, Kai ne Mai ji, Masani."
3|36|To, a lõkacin da ta haife ta sai ta ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne nĩ, nã haife ta mace!"KumaAllah ne Mafi sanin abin da ta haifa." Kuma namiji bai zama kamar mace ba. Kuma nĩ nã yi mata suna Maryamu kuma lalle ne ni, ina nẽma mata tsari gare Ka, ita da zũriyarta daga Shaiɗan jẽfaffe."
3|37|Sai Ubangijinta Ya karɓe ta karɓa mai kyau. Kuma Ya yabanyartar da ita yabanyartarwa mai kyau, kuma Ya sanya rẽnonta ga Zakariyya. Ko da yaushe Zakariyya ya shiga masallãci, a gare ta, sai ya sãmi abinci a wurinta. (Sai kuwa) ya ce: "Yã Maryamu! Daga ina wannan yake gare ki?" (Sai) ta ce: "Daga wurin Allah yake. Lalle ne Allah yana azurta wanda Ya so ba da lissafi ba."
3|38|A can ne Zakariyya ya rõki Ubangijinsa, ya ce: "Ya Ubangijina! Ka bã ni zuriyya mai kyau daga gunKa. Lalle ne Kai Mai jin addu'a Kake."
3|39|Sai malã'iku suka kirãye shi, alhãli kuwa shĩ yanã tsaye yana salla a cikin masallãci. (Suka ce), "Lalle ne Allah yana bã ka bushãra da Yahaya, alhãli yana mai gaskatãwar wata kalma daga Allah, kuma shugaba, kuma tsarkakke kuma annabi daga sãlihai."
3|40|Ya ce: "Yã Ubangijina! Yãya yãro zai sãmu a gare ni, alhãli kuwa, lalle tsũfa ya sãme ni, kuma mãtãta bakarãriya ce?" Allah ya ce, "Kamar hakan ne, Allah yana aikata abin da Yake so."
3|41|Ya ce: "Yã Ubangijinã! Ka sanya mini wata alãma!" (Allah) Ya ce "Alãmarka ita ce ba zã ka iya yi wa mutãne magana ba har yini uku face da ishãra. Sai ka ambaci Ubangijinka da yawa. Kuma ka yi tasbĩhi da marece da sãfe."
3|42|Kuma a lõkacin da malã'iku suka ce: "Ya Maryamu! Lalle ne, Allah Ya zãɓe ki, kuma Ya tsarkake ki, kuma Ya zaɓe ki a kan mãtan tãlikai."
3|43|"Yã Maryamu! Ki yi ƙanƙan da kai ga Ubangijinki, kuma ki yi sujada, kuma ki yi rukũ'i tãre da mãsu rukũ'i."
3|44|Wannan yana daga lãbarun gaibi, Munã yin wahayinsa zuwa gare ka (Muhammadu). Ba ka kasance ba a wurinsu a lõkacin da suke jẽfa alƙalumansu (domin ƙuri'a) wãne ne zai yi rẽnon Maryam. Kuma ba ka kasance a wurinsu ba a lõkacin da suke ta yin husũma.
3|45|A lõkacin da malã'iku suka ce "Yã Maryamu! Lalle ne Allah Yana bã ki bushãra da wata kalma daga gare Shi; sũnansa Masĩhu ĩsa ɗan Maryama, yana mai daraja a dũniya da Lãhira kuma daga Makusanta.
3|46|"Kuma yana yi wa mutãne magana a cikin shimfiɗar jariri, da kuma lõkacin da yana dattijo, kuma yana daga sãlihai."
3|47|Ta ce: "Yã Ubangijina! Yãya yãro zai kasance a gare ni, alhãli kuwa wani mutum bai shãfe ni ba?" (Allah) Ya ce: "Kamar wannan ne, Allah yana halittar abin da Yake so. Idan Ya hukunta wani al'amari, sai ya ce masa, "Ka kasance!, Sai yana kasancẽwa."
3|48|Kuma Ya sanar da shi rubũtu da hikima da Taurata da injĩla.
3|49|Kuma (Ya sanya shi) manzo zuwa ga Bani Isrãila'ĩla (da sãko, cẽwa), Lalle ne, ni haƙĩƙa nã zõ muku, da wata ãyã daga Ubangijinku. Lalle ne ni ina halitta muku daga lãka, kamar siffar tsuntsu sa'an nan in hũra a cikinsa, sai ya kasance tsuntsu, da izinin Allah. Kuma ina warkar da wanda aka haifa makãho da kuturu, kuma ina rãyar da matottu, da izibin Allah. Kuma ina gayã muku abin da kuke ci da abin da kuke ajiyẽwa acikin gidãjenku. Lalle ne, a cikin wannan akwai ãyã a gare ku, idan kun kasance mãsu yin ĩmãni.
3|50|"Kuma inã mai gaskatãwa ga abin da yake a gabãnina daga Taurata. Kuma (nãzo) dõmin in halatta muku sãshen abin da aka haramta muku. Kuma nã tafo muku da wata ãyã daga Ubangijinku. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã.
3|51|"Lalle Allah shi ne Ubangijina, kuma Ubangijinku, sai ku bauta Masa. Wannan ce hanya madaidaiciya."
3|52|To, a lõkacin da Ĩsa ya gane kãfirci daga gare su, sai ya ce: "Su wãne ne mataimakãna zuwa ga Allah?" Hawãriyãwa suka ce: "Mu ne mataimakan Allah. Mun yi ĩmani da Allah. Kuma ka shaida cẽwa lalle ne mu, mãsu sallamãwa ne.
3|53|"Yã Ubangijinmu! Mun yi imãni da abin da Ka saukar, kuma mun bi ManzonKa, sai Ka rubũta mu tãre da mãsu shaida..
3|54|Kuma (Kãfirai) suka yi mãkirci, Allah kuma Ya yi musu (sakamakon) makircin, kuma Allah ne Mafi alhẽrin mãsu sãka wamãkirci.
3|55|A lõkacin da Ubangiji Ya ce: "Ya Ĩsa! Lalle NĨ Mai karɓar ranka ne, kuma Mai ɗauke ka ne zuwa gare Ni, kuma Mai tsarkake ka daga waɗanda suka kãfirta, kuma Mai sanya waɗanda suka bĩ ka a bisa waɗanda suka kãfirta har Rãnar ¡iyãma. Sa'an nan kuma zuwa gare Ni makõmarku take, sa'an nan in yi hukunci a tsakãninku, a cikin abin da kuka kasance kuna sãɓã wa jũna.
3|56|"To, amma waɗanda suka kãfirta sai In azabta su da azãba mai tsanani, a cikin dũniya da Lãhira, kuma bã su da wasu mãsu taimako.
3|57|Kuma amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sai (Allah) Ya cikã musu ijãrõrinsu. Kuma Allah bã Ya son azzãlumai.
3|58|"Wannan Muna karanta shi a gare ka (Muhammad) daga ãyõyi, da Tunatarwa mai hikima (Alƙur'ãni)."
3|59|Lalle ne misãlin Ĩsã a wurin Allah kamar misãlin Ãdama ne, (Allah) Yã halitta shi daga turɓãya, sa'an nan kuma Ya ce masa: "Ka kasance: "Sai yana kasancewa.
3|60|Gaskiya daga Ubangijinka take sabõda haka kada ka kasance daga mãsu shakka.
3|61|To, wanda ya yi musu da kai a cikinsa, a bãyan abin da ya zo maka daga ilmi, to ka ce: "Ku zo mu kirãyi, 'yã'yanmu da 'yã'yanku da mãtanmu da mãtanku da kanmu da kanku sa'an nan kuma mu ƙanƙantar da kai sa'an nan kuma mu sanya la'anar, Allah a kan maƙaryata."
3|62|Lalle ne wannan, haƙĩƙa, shi ne lãbãri tabbatacce, kuma bãbu wani abin bautawa fãce Allah, kuma lalle ne, Allah, haƙĩƙa, Shi ne Mabuwãyi Mai hikima.
3|63|To, idan sun jũya bãya, to, lalle Allah Masani ne ga maɓannata.
3|64|Ka ce: "Yã ku Mutãnen Littãfi! Ku tafo zuwa ga kalma mai daidaitãwa a tsakã ninmu da ku; kada mu bauta wa kõwa fã ce Allah. Kuma kada mu haɗa kõme da Shi, kuma kada sãshenmu ya riƙi sãshe Ubangiji, baicin Allah." To, idan sun jũya bã ya sai ku ce: "ku yi shaida cẽwa, lalle ne mu masu sallamã wa ne."
3|65|Yã Mutãnen Littãfi! Don me kuke hujjacẽwa a cikin sha'anin lbrãhĩma, alhãli kuwa ba a saukar da Attaura da injĩla ba fãce daga bãyansa? Shin bã ku hankalta?
3|66|Gã ku yã waɗannan! Kun yi hujjacẽwa a cikin abin da yake kunã da wani ilmi game da shi, to, don me kuma kuke yin hujjacẽwa a cikin abin da bã ku da wani ilmi game da shi? Allah yana sani, kuma kũ, ba ku sani ba!
3|67|Ibrãhĩma bai kasance Bayahũde ba, kuma bai kasance Banasãre ba, amma yã kasance mai karkata zuwa ga gaskiya, mai sallamãwa, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba.
3|68|Lalle ne mafi hakkin mutãne da Ibrãhĩma haƙĩƙa, sũ ne waɗanda suka bi shi a (zamaninsa) da wannan Annabi (Muhammadu) da waɗanda suka yi ĩmãni. Kuma Allah ne Majiɓincin mũminai.
3|69|Wata ƙungiya daga Mutãnen Littãfi sun yi gũrin su ɓatar da ku, to, ba su ɓatar da kõwa ba fãce kansu, kuma bã su sansancewa!
3|70|Yã Mutãnen Littãfi! Don me kuka kãfirta da ãyõyin Allah, alhãli kuwa kũ, kuna shaida (cẽwa sũ gaskiya ne)?
3|71|Yã Mutãnen Littãfi! Don me kuke lulluɓe gaskiya da ƙarya, kuma kuke ɓõye gaskiya, alhãli kuwa kuna sane?
3|72|Kuma wata ƙungiya daga Mutãnen Littãfi ta ce: "Ku yi ĩmãni da abin da aka saukar a kan waɗanda suka yi ĩmãni (da Muhammadu) a farkon yini, kuma ku kãfirta a ƙarshensa; tsammãninsu, zã su kõmõ."
3|73|"Kada ku yi ĩmãni fãce da wanda ya bi addininku." Ka ce: "Lalle ne, shiriya ita ce shiriyar Allah. (Kuma kada ku yi ĩmãni) cẽwa an bai wa wani irin abin da aka bã ku, kõ kuwa su yi musu da ku a wurin Ubangijinku." Ka ce: "Lalle ne falala ga hannun Allah take, yana bãyar da ita ga wanda Yake so, kuma Allah Mawadãci ne, Masani."
3|74|Yanã keɓance wanda Ya so da rahamarSa, kuma Allah Ma'abucin falala ne, Mai girma.
3|75|Kuma daga Mutãnen Littãfi akwai wanda yake idan ka bã shi amãnar kinɗãri, zai bãyar da shi gare ka, kuma daga gare su akwai wanda idan ka bã shi amãnar dĩnari, bã zai bãyar da shi gare ka ba, fãce idan kã dawwama a kansa kanã tsaye. Wannan kuwa, dõmin lalle ne sũ sun ce, "Bãbu laifi a kanmu a cikin Ummiyyai." Suna faɗar ƙarya ga Allah, alhãli kuwa suna sane.
3|76|Na'am! Wanda ya cika alkawarinsa, kuma ya yi taƙawa, to, lalle ne Allah yana son mãsu taƙawa.
3|77|Lalle ne waɗanda suke sayen 'yan tamani kaɗan da alkawarin Allah da rantsuwõyinsu, waɗannan bãbu wani rabo a gare su a Lãhira, Kuma Allah bã Ya yin magana da su, kuma bã Ya dũbi zuwa gare su, a Rãnar ¡iyãma, kuma bã Ya tsarkake su, kuma sunã da azãba mai raɗaɗi.
3|78|Kuma lalle ne, daga gare su akwai wata ƙungiya suna karkatar da harsunansu da Littãfi dõmin ku yi zaton sa daga Littãfin, alhãli kuwa bã shi daga Littãfin. Kuma suna cẽwa: "Shi daga wurinAllah yake." Alhãli kuwa shi, bã daga wurin Allah yake ba. Sunã faɗar ƙarya ga Allah, alhãli kuwa sunã sane.
3|79|Ba ya yiwuwa ga wani mutum, Allah Ya bã shi Littãfi da hukunci da Annabci, sa'an nan kuma ya ce wa mutãne: "Ku kasance bãyi gare ni, baicin Allah." Amma (zai ce): "Ku kasance mãsu aikin ibãda da abin da kuka kasance kuna karantar da Littãfin, kuma da abin da kuka kasance kuna karantãwa."
3|80|Kuma ba ya umurnin ku da ku riƙi malã'iku da annabãwa lyãyengiji. Shin, zai umurce ku da kãfirci ne a bãyan kun riga kun zama mãsu sallamãwa (Musulmi)?
3|81|Kuma a lõkacin da Allah Ya riƙi alkawarin Annabãwa: "Lalle ne ban bã ku wani abu ba daga Littãfi da hikima, sa'an nan kuma wani manzo ya je muku, mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da ku; lalle ne zã ku gaskata Shi, kuma lalle ne zã ku taimake shi." Ya ce: "Shin, kun tabbatar kuma kun riƙi alkawarĩNa a kan wannan a gare ku?" suka ce: "Mun tabbatar." Ya ce: "To, ku yi shaida, kuma Nĩ a tãre da ku Inã daga mãsu shaida."
3|82|To, waɗanda kuma suka jũya bãya a bãyan wannan, to, waɗannan sũ ne fãsiƙai.
3|83|Shin wanin Addinin Allah suke nẽma, alhãli kuwa a gare Shi ne waɗanda ke cikin sama da ƙasa suka sallama wa, a kan sõ da ƙĩ, kuma zuwa gare Shi ake mayar da su?
3|84|Ka ce: "Mun yi ĩmãni da Allah kuma da abin da aka saukar mana da abin da aka saukar wa Ibrãhĩma da Isma'ĩla da Is'hãƙa da Yãƙũba da jĩkõki, da abin da aka bai wa Mũsã da ĩsã da annabãwa daga Ubangijinsu, bã mu bambantãwa a tsakãnin kõwa daga gare su. Kuma mũ, zuwa gare Shi mãsu sallamãwa ne."
3|85|Kuma wanda ya nẽmi wanin Musulunci ya zama addini, to, bã zã a karɓa daga gare shi ba. Kuma shi a Lãhira yana daga cikin mãsu hasãra.
3|86|Yãya Allah zai shiryar da mutãne waɗanda suka kãfirta a bãyan ĩmãninsu, kuma sun yi shaidar cẽwa, lalle Manzo gaskiya ne, kuma hujjõji bayyanannu sun je musu? Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai.
3|87|Waɗannan, sakamakonsu shi ne, lalle a kansu akwai la'anar Allah da mãla'iku da mutãne gabã ɗaya.
3|88|Sunã mãsu dawwama a cikinta, bã a sauƙaƙa azãbar gare su, kuma ba su zama ana yi musu jinkiri ba.
3|89|Fãce waɗanda suka tũba daga bãyan wannan, kuma suka yi gyãra, to, lalle ne Allah Mai gãfara ne Mai jin ƙai.
3|90|Lalle ne waɗanda suka kãfirta a bãyan ĩmãninsu, sa'an nan kuma suka ƙãra kãfirci bã zã a karɓi tũbarsu ba. Kuma waɗannan sũ ne ɓatattu.
3|91|Lalle ne wanɗanda suka kãfirta, kuma suka mutu alhãli kuwa suna kãfirai to bã zã a karɓi cike da ƙasa na zinãri daga ɗayansu ba, kõ dã ya yi fansa da shi, waɗannan sunã da azãba mai raɗaɗi, kuma bã su da wasu mataimaka.
3|92|Bã zã ku sãmi kyautatãwa ba, sai kun ciyar daga abin da kuke so. Kuma abin da kuka ciyar, kõ mẽne ne, to, lalle ne Allah, gare shi, Masani ne.
3|93|Dukan abinci yã kasance halal ne ga Bani lsrã'ĩla, fãce abinda Isrã'ĩla ya haramta wa kansadaga gabãnin saukar da Attaura. Ka ce: "To, ku zo da Attaura sa'an nan ku karantã ta, idan kun kasance mãsu gaskiya ne.
3|94|"To, wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah daga bãyan wannan, to, waɗannan sũ ne azzãlumai."
3|95|Ka ce: "Allah Ya yi gaskiya, sabõda haka ku bi aƙĩdar Ibrãhĩma mai karkata zuwa ga gaskiya; kuma bai kasance daga mãsu shirki ba."
3|96|Kuma lalle ne, ¦aki na farko da aka aza dõmin mutãne, haƙĩƙa, shi ne wanda ke Bakka mai albarka kuma shiriya ga tãlikai.
3|97|A cikinsa akwai ãyõyi bayyanannu; (ga misãli) matsayin Ibrãhĩma. Kuma wanda ya shige shi yã kasance amintacce. Kuma akwai hajjin ¦ãkin dõmin Allah a kan mutãne, ga wanda ya sãmi ĩkon zuwa gare shi, kuma wanda ya kafirta to lalle Allah Mawadãci ne daga barin tãlikai.
3|98|Ka ce: "Ya kũ Mutãnen Littãfi! Don me kuke kãfirta da ãyõyin Allah, alhãli kuwa Allah Mai shaida ne a kan abin da kuke aikatãwa?"
3|99|Ka ce: "Ya ku Mutãnen Littãfi! Don me kuke taushe wanda ya yi ĩmani, daga hanyar Allah, kuma kunã nẽman ta zama karkatacciya, alhãli kuwa kunã mãsu shaida? Kuma Allah bai gushe daga abin da kuke aikatãwa ba yana Masani."
3|100|Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun yi ɗã'aga wani ɓangare daga waɗanda aka bai wa Littãfi, zã su mayar da ku kãfirai a bãyan ĩmãninku!
3|101|Kuma yãyã kuke kãfircẽwa alhãli kuwa anã karanta ãyõyin Allah a gare ku, kuma a cikinku akwai manzonSa? Kuma wanda ya nẽmi tsari da Allah, to, an shiryar da shi zuwa ga hanya miƙaƙƙiya.
3|102|Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa, a kan hakkin binsa da taƙawa, kuma kada ku mutu fãce kuna mãsu sallamawa (Musulmi).
3|103|Kuma ku yi daidami da igiyar Allah gabã ɗaya, kuma kada ku rarraba. Kuma ku tuna ni'imar Allah a kanku a lõkacin da kuka kasance maƙiya sai Ya sanya sõyayya a tsakãnin zukãtanku sabõda haka kuka wãyi gari, da ni'imarSa, 'yan'uwa. Kuma kun kasance a kan gãɓar rãmi na wutã sai Ya tsãmar da ku daga gare ta, Kamar wannan ne Allah Yake bayyana muku ayõyinSa, tsammãninku, zã ku shiryu.
3|104|Kuma wata jama'a daga cikinku, su kasance suna kira zuwa ga alhẽri, kuma suna umurnida alhẽri, kuma suna hani dagaabin da ake ƙi. Kuma waɗannan, sũ ne mãsu cin nasara.
3|105|Kuma kada ku kasance kamar waɗanda suka rarrabu kuma suka sãɓã wa jũna, bãyan hujjõji bayyanannu sun je musu kuma waɗannan sunã da azãba mai girma.
3|106|A rãnar da wasu fuskõki suke yin fari kuma wasu fuskõki suke yin baƙi (zã a ce wa waɗanda fuskokinsu suke yin baƙin): "Shin kun kãfirta a bayan ĩmãninku? Don haka sai ku ɗanɗani azãba sabõda abin da kuka kasance kuna yi na kãfirci."
3|107|Kuma amma waɗanda fuskõkinsu suka yi fari, to sũ suna cikin rahamar Allah kuma, su a cikinta, madawwama, ne.
3|108|Waɗannan ãyõyin Allah ne, muna karanta su a gare ka da gaskiya, kuma Allah bã Ya nufin wani zãlunci ga tãlikai.
3|109|Kuma abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa na Allah ne, kuma zuwa gare Shi ake mayar da al'amurra.
3|110|Kun kasance mafi alhẽrin al'umma wadda aka fitar ga mutãne kuna umurni da alhẽri kuma kunã hani daga abin da ake ƙi, kuma kunã ĩmãni da Allah. Kuma dã Mutãnen Littãfi sun yi ĩmãni, lalle ne, dã (haka) yã kasance mafi alhẽri a gare su. Daga cikinsu akwai mũminai, kuma mafi yawansufãsiƙai ne.
3|111|Bã zã su cũce ku ba, fãce dai tsangwama. Kuma idan sun yãƙe ku zã su jũya muku bãya, sa'an nan kuma bã zã a taimake su ba.
3|112|An dõka ƙasƙanci a kansu a inda duk aka sãme su fãce da wani alkawari daga Allah, da alkawari daga mutãne. Kuma sun kõma da fushi daga Allah, kuma aka dõka talauci a kansu. Wannan kuwa dõmin sũ, lalle sun kasance suna kãfirta da ãyõyin Allah, kuma suna kashe annabãwa, bã da wani haƙƙi ba. Wannan kuwa dõmin sãɓãwar da suka yi ne, kuma sun kasance suna yin ta'adi.
3|113|Ba su zama daidai ba; daga Mutãnen Littafi akwai wata al'umma wadda take tsaye, suna karãtun ayõyin Allah a cikin sã'õ'in dare, alhãli kuwa sunã yin sujada.
3|114|Suna ĩmãni da Allah da Yinin Lãhira, kuma suna umurui da abin da aka sani kuma suna hani daga abin da ba a sani ba, kuma sunã gaugãwa a cikin alhẽrai. Kuma waɗannan suna cikin sãlihai.
3|115|Kuma abin da suka aikata daga alhẽri, to, bã zã a yi musu musunsa ba. Kuma Allah Masani ne ga mãsu taƙawa.
3|116|Lalle ne waɗanda suka kãfirta, dũkiyõyinsu kõ ɗiyansu bã zã su wadatar musu da kõme ba daga Allah kuma waɗannan abõkan wuta ne, sũ, acikinta, madawwama ne.
3|117|Misãlin abin da suke ciyarwa, a cikin wannan rãyuwar dũniya, kamar misãlin iska ce (wadda) a cikinta akwai tsananin sanyi, ta sãmi shukar wasu mutãne waɗanda suka zãlunci kansu, sai ta halakar da ita. Allah bai zãlunce su ba, amma kansu suka kasance sunã zãlunta.
3|118|Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi abõkan asĩri daga waninku, ba su taƙaita muku ɓarna. Kuma sun yi gũrin abin da zã ku cũtu da shi. Haƙĩka, ƙiyayya tã bayyana daga bãkunansu, kuma abin da zukãtansu ke ɓõyẽwane mafi girma. Kuma lalle ne, Mun bayyana muku ãyõyi, idan kun kasance kunã hankalta.
3|119|Gã ku yã waɗannan! Kunã son su bã su son ku, kuma kuna ĩmãni da Littãfi dukansa. Kuma idan sun haɗu da ku sukan ce "Mun yi ĩmani". Kuma idan sun kaɗaita sai su ciji yãtsu a kanku don takaici. Ka ce "Ku mutu da takaicinku. Lalle ne, Allah Masani ne ga abin da ke cikin ƙirãza."
3|120|Idan wani alhẽri ya shãfe ku sai ya baƙanta musu rai, kuma idan wata cũtar ta shãfe ku sai su yi farin ciki da ita. Kuma idan kun yi haƙuri kuma kuka yi taƙawa, ƙullinsu bã ya cũtar ku da kõme. Lalle ne, Allah ga abin da suke aikatãwa Mai kẽwayẽwa ne.
3|121|Kuma a lõkacin da ka yi sauko daga iyãlanka kana zaunar da mũminai a wurãren zamadõmin yãƙi, kuma Allah Mai ji ne, Masani.
3|122|A lõkacin da ƙungiyõyi biyu daga gare ku suka yi niyyar su karye, kuma Allah ne Majiɓincinsu, don haka, ga Allah mũminai sai su dogara.
3|123|Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Allah Yã taimake ku a Badar, alhãli kuwa kunã mafiya rauni, sabõda haka ku bi Allah da taƙawa tsammãninku, kuna gõdẽwa.
3|124|A lõkacin da kake cẽwa ga mũminai, "Shin bai ishe ku ba, Ubangijinku Ya taimake ku da dubu uku daga malã'iku saukakku?"
3|125|"Na'am! Idan kuka yi haƙuri, kuma kuka yi taƙawa, kuma suka zo muku da gaugawarsu, irin wannan, Ubangijinku zai ƙãre ku da dubu biyar daga malãiku mãsu alãma."
3|126|Kuma Allah bai sanya shi ba, fãce dõmin bushãra a gare ku, kuma dõmin zukãtanku su natsu da shi. Taimako bai kasance ba fãce daga wurin Allah, Mabuwãyi, Mai hikima.
3|127|Dõmin Ya katse wani gẽfe daga waɗanda suka kãfirta ko kuma Ya ƙasƙantã su, har su jũya, suna mãsu ruɓushi.
3|128|Bãbu kõme a gare ka game da al'amarin (shiryar da su banda iyar da manzanci). Ko Allah Ya karɓi tũbarsu, kõ kuwa Ya yimusu azãba, to lalle ne sũ, mãsu zãlunci ne.
3|129|Allah ne da mulkin abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, yana gãfarta wa wanda Yake so, kuma yana azabta wanda Yake so, kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
3|130|Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku ci riba ninkininki, riɓanye, kuma ku bi Allah da taƙawa, tsammãninku zã ku ci nasara.
3|131|Kuma ku ji tsõron wutã wadda aka yi tattali dõmin kãfirai.
3|132|Kuma ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, tsammaninku a yi muku rahama.
3|133|Kuma ku yi gaugawa zuwa ga nẽman gãfara daga Ubangijinku da wata Aljanna wadda fãɗinta (dai dai da) sammai da ƙasa ne, an yi tattalinta dõmin mãsu taƙawa.
3|134|Waɗanda suke ciyarwa a cikin sauƙi da tsanani kuma suke mãsu haɗiyẽwar fushi, kuma mãsu yãfe wa mutãne laifi. Kuma Allah Yana son mãsu kyautatãwa.
3|135|Kuma waɗanda suke idan suka aikata wata alfãsha ko suka zãlunci kansu sai su tunã da Allah, sabõda su nẽmi gãfarar zunubansu ga Allah. Kuma wãne ne ke gãfara ga zunubai, fãce Allah? Kuma ba su dõge a kan abin da suka aikata ba, alhãli kuwa suna sane.
3|136|Waɗannan sakamakonsu gãfara ce daga Ubangijinsu, daga Gidajen Aljanna (waɗanda) ƙõramu na gudana daga ƙarƙashinsu, suna madawwama a cikinsu. Kuma mãdalla da ijãrar mãsu aiki.
3|137|Lalle ne misãlai sun shũɗe a gabãninku, sai ku yi tafiya a cikin ƙasa sa'an nan ku dũba, yãyã ãƙibar mãsu ƙaryatãwa ta kasance.
3|138|Wannan bayãni ne ga mutãne, kuma shiryuwa ce da wa'azi ga mãsu taƙawa.
3|139|Kuma kada ku yi rauni, kuma kada ku yi baƙin ciki, alhãli kuwa kũ ne mafiya ɗaukaka, idan kun kasance mãsu ĩmãni.
3|140|Idan wani mĩki ya shãfe ku, to, lalle ne, wani mĩki kamarsa ya shãfi mutãnen, kuma waɗancan kwãnaki Muna sarrafa su a tsakãnin mutãne dõmin Allah Ya san waɗanda suka yi ĩmãni kuma Ya sãmi mãsu shahãda daga gare ku. Kuma Allah ba Ya son azzãlumai.
3|141|Kuma dõmin Allah Ya ɗauraye waɗanda suka yi ĩmãni, kuma Ya ƙõƙe kãfirai.
3|142|Ko kun yi zaton ku shiga Aljanna alhãli kuwa Allah bai bãda sanin waɗanda suka yĩ jihãdi daga gare ku ba, kuma Ya san mãsu haƙuri?
3|143|Kuma lalle ne, haƙĩƙa kun kasance kuna gũrin mutuwa tun a gabãnin ku haɗu da ita, to lalle ne kun gan ta, alhãli kuwa kuna kallo.
3|144|Kuma Muhammadu bai zama ba face manzo lalle ne manzanni sun shũɗe a gabãninsa. Ashe idan ya mutu ko kuwa aka kashe shi, zã kujũya a kan dugaduganku? To, wanda ya jũya a kan dugadugansa, bã zai cũci Allah da kõme ba. Kuma Allah zai sãka wa mãsu gõdiya.
3|145|Kuma bã ya yiwuwa ga wani rai ya mutu fãce da iznin Allah, wa'adi ne mai ƙayyadadden ajali. Kuma wanda yake nufin sakamakon dũniya Muna bã shi daga gare ta. Kuma wanda ke nufin samakon Lãhira Muna bã shi daga gare ta. Kuma zã Mu sãka wa mãsu godiya.
3|146|Kuma da yawa wani Annabi wanda ya yi yãƙi, akwai jama'a mãsu yawa tãre da shi, sa'an nan ba su yi laushi ba ga abin da ya same su a cikin hanyar Allah, kuma ba su yi rauni ba kuma ba su sad da kai ba. Kuma Allah yana son mãsu haƙuri.
3|147|Kuma bãbu abin da ya kasance maganarsu fãce faɗarsu cẽwa: "Ya Ubangijinmu! Ka gãfarta mana zunubanmu da ɓarnarmu a cikin al'amarinmu, kuma Ka tabbatar da dugaduganmu, kuma Ka taimake mu a kan mutãnen nan kãfirai."
3|148|Allah Yã sãka musu da sakamakon dũniya da kuma kyakkyawan sakamakon Lãhira. Kuma Allah yana son mãsu kyautatãwa.
3|149|Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun yi ɗa'aga waɗanda suka kãfirta zã su mayar da ku a kan dugãduganku, har ku jũya kunã mãsu hasãra.
3|150|Ã'a, Allah ne Majiɓincinku kuma ShĨ ne Mafi alhẽrin matai maka.
3|151|Zã Mu jẽfa tsõro a cikin zukãtan waɗanda suka kãfirta sabõda shirkin da suka yi da Allah gãme da abin da bai saukar da wani dalili ba game da shi. Kuma makõmarsu wuta ce, kuma tir da mazaunin azzãlumai!
3|152|Kuma lalle ne haƙĩƙa Allah Yã yi muku gaskiya ga wa'adinSa, a lokacin da kuke kashe su da izninSa har zuwa lõkacin da kuka kãsa, kuma kuka yi jãyayya a cikin al'amarin, kuma kuka sãɓã a bãyan (Allah) Ya nũna muku abin da kuke so. Daga cikinku akwai wanda yake nufin duniya kuma daga cikinku akwai wanda ke nufin Lãhĩra. Sa'an nan kuma Ya jũyar da ku daga gare su, dõmin Ya jarrabe ku. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Ya yãfe muku laifinku. Kuma Allah Ma'abucin falala ne ga mũminai.
3|153|A lõkacin da kuke hawan dũtse, gudãne. Kuma ba ku karkata a kan kõwa ba, alhãli kuwa Manzon Allah nã kiran ku a cikin na ƙarshenku. Sa'an nan (Allah) Ya sãkã muku da baƙin ciki a tãre da wani baƙin ciki. Domin kada ku yi baƙin ciki a kan abin da ya kuɓuce muku, kuma kada ku yi baƙin cikin a kan abin da ya sãme ku. Kuma Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa.
3|154|Sa'an nan kuma (Allah) Ya saukar da wani aminci a gare ku daga bãyan baƙin cikin; gyangyaɗi yanã rufe wata ƙungiya daga gare ku, kuma wata ƙungiya, lalle ne, rãyukansu sun shagaltar da su, suna zaton abin da bã shi ne gaskiya ba, a game da Allah, irin zaton jahiliyya, suna cẽwa: "Ko akwai waniabu a gare mu dai daga al'amarin?" Ka ce, "Lalle ne al'amari dukansa na Allah ne." Suna ɓõyẽwa a cikin zukatansu, abin da bã su bayyana shi a gare ka. Suna cẽwa: "Da munã da wani abu daga al'amarin dã ba a kashe mu ba a nan."Ka ce: "Kõ dã kun kasance a cikin gidãjenku, dã waɗanda aka rubũta musu kisa sun fita zuwa ga wurãren kwanciyarsu;" kuma (wannan abu yã auku ne) dõmin Allah Ya jarrabi abin da ke cikin ƙirãzanku. Kuma dõmin Ya tsarkake abin da ke cikin zukãtanku. Allah Masani ne ga abin da ke cikin ƙirãza.
3|155|Lalle ne waɗanda suka jũya daga gare ku a ranar haɗuwar jama'a biyu, shaiɗan kawai ne ya talãlãɓantar da su, sabõda sãshen abin da suka tsirfanta. Kuma lalle ne haƙĩƙa, Allah Ya yãfe laifidaga gare su. Lalle Allah ne Mai gãfara Mai haƙuri.
3|156|Yã ku waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku kasance kamar waɗanda suka kãfirta kuma suka ce wa'yan'uwansu idan, sun yi tafiya a cikin ƙasa kõ kuwa suka kasance a wurin yãƙi: "Dã sun kasance a wurinmu dã ba su mutun ba, kuma dã ba a, kashe su ba." (Wannan kuwa) Dõmin Allah Ya sanya waccan magana ta zama nadãma a cikin zukãtansu. Kuma Allah ne Yake rãyarwa kuma Yake matarwa. Kuma Allah, ga abin da kuke aikatãwa, Mai gani ne.
3|157|Kuma lalle ne idan aka kashe, ku a cikin hanyar Allah, ko kuwa kuka mutu, haƙĩƙa, gãfara daga Allah da rahama ne mafi alhẽri daga abin da suke tãrãwa.
3|158|Kuma lalle ne idan kun mutu ko kuwa aka kashe ku, haƙĩƙa, zuwa ga Allah ake tãra ku.
3|159|Sabõda wata rahama ce daga Allah ka yi sanyin hali a gare su. Kuma dã kã kasance mai hushi mai kaurin zuciya, dã sun wãtse daga gẽfenka. Sai ka yãfe musu laifinsu, kuma ka nẽma musu gãfara, kuma ka yi shãwara da su a cikin al'amarin. Sa'an nan kuma idan ka yi niyyar zartarwa, to, ka dõgara ga Allah, lalle ne, Allah Yana son mãsu tawakkali.
3|160|Idan Allah Ya taimake ku, to, bãbu marinjayi a gare ku. Kuma idan Ya yarɓe ku, to, wãnẽ ne wanda yake taimakon ku bãyanSa? Kuma ga Allah sai mũminai su dõgara.
3|161|Kuma bã ya yiwuwa ga wani annabi ya ci gulũlu. Wanda ya ci gulũlu zai je da abin da ya ci na gulũlun, a Rãnar ¡iyama. Sa'an nan a cika wa kõwane rai sakamakon abin da ya tsirfanta. Kuma sũ, bã zã a zãlunce su ba.
3|162|Shin fa, wanda ya bĩbiyi yardar Allah, yana zama kamar wanda ya kõma da fushi daga Allah kuma makomarsa Jahannama ce? Kuma tir da makõma ita!
3|163|Sũ, darajõji ne a wurin Allah, kuma Allah Mai gani ne ga abin da suke aikatawa.
3|164|Lalle ne haƙĩƙa Allah Yã yi babbar falala a kan mũminai, dõmin Yã aika a cikinsu, Manzo daga ainihinsu yana karanta ãyõyinSa a gare su, kuma yana tsar kake su, kuma yana karantar da su Littãfi da hikima kuma lalle, sun kasance daga gabãni, haƙĩƙa suna cikin ɓata bayyananniya.
3|165|Shin kuma a lõkacin da wata masĩfa, haƙĩƙa, ta sãme ku alhãli kuwa kun sãmar da biyunta, kun ce: "Daga ina wannan yake?" Ka ce: "Daga wurin rãyukanku yake." Lalle ne, Allah, a kan dukan kõme, Mai ĩkon yi ne.
3|166|Kuma abin da ya sãme ku a rãnar haɗuwar jama'a biyu, to, da izinin Allah ne, kuma dõmin (Allah) Ya san mũminai (na gaskiya).
3|167|Kuma dõmin Ya san waɗanda suka yi munãfunci, kuma an ce musu: "Ku zo ku yi yãƙi a cikin hanyar Allah, kõ kuwa ku tunkuɗe." Suka ce: "Dã mun san (yadda ake) yãƙi dã mun bĩ ku." Sũ zuwa ga kãfirci a rãnar nan, sun fi kusa daga gare su zuwa ga ĩmãni. Sunã cẽwa da bãkunansu abin da bã shi ne a cikin zukãtansu ba. Allah ne Mafi sani ga abin da suke ɓõyewa.
3|168|Waɗanda suka ce wa 'yan'uwansu kuma suka zauna abinsu: "Dã sun yi mana ɗã'a, dã ba a kashe su ba." Ka ce: "To, ku tunkuɗe mutuwa daga rãyukanku, idan kun kasance mãsu gaskiya."
3|169|Kada ka yi zaton waɗanda aka kashe a cikin hanyar Allah matattu ne. A'a, rãyayyu ne su, a wurin bangijinsu. Ana ciyar da su.
3|170|Suna mãsu farin ciki sabõda abin da Allah Ya bã su daga falalarSa, kuma suna yin bushãra ga waɗanda ba su risku da su ba, daga bayansu; "Bãbu tsõro a kansu kuma ba su zama suna yin baƙin ciki ba."
3|171|Suna yin bushãra sabõda wata ni'ima daga Allah da wata falala. Kuma lalle ne, Allah bã Ya tozartar da ijãrar mũminai.
3|172|Waɗanda suka karɓa kira zuwa ga Allah da ManzonSa, daga bãyan mĩki ya sãme su. Akwai wata lãda mai girma ga waɗanda suka kyautata yi daga gare su, kuma suka yi taƙawa.
3|173|Waɗanda mutãne suka ce musu: "Lalle ne, mutãne sun tãra (rundunõni) sabõda ku, don haka ku ji tsõrnsu. Sai (wannan magana) ta ƙara musu ĩmãni, kuma suka ce: "Mai isarmu Allah ne kuma mãdalla da wakili Shĩ."
3|174|Sa'an nan sukajũya da wata ni'ima daga Allah da wata falala, wata cũta ba ta shãfe su ba, kuma suka bi yardar Allah. Kuma Allah ne Ma'abucin falala Mai girma.
3|175|Wancan, Shaiɗan ne kawai yake tsõratar da, ku masõyansa. To, kada ku ji tsõronsu ku ji tsõro Na idãn kun kasance mãsu ĩmãni.
3|176|Kuma waɗannan da suke gaugãwa a cikin kãfirci kada su ɓãta maka rai. Lalle ne su, bã zã su cũci Allah da kõme ba. Allah yanã nufin cẽwa, bã zai sanya musu wani rabo ba a cikin Lãhira kuma suna da wata azãba mai girma.
3|177|Lalle ne, waɗanda suka sayi kãfirci da ĩmani, ba zã su cũci Allah da kõme ba. Koma sunã da azãba mai raɗaɗi.
3|178|Kuma kada waɗanda suka kãfirta su yi zaton cẽwa, lalle ne jinkirin da Muke yi musu alhẽri ne ga rãyukansu. Munã yi musu jinkirin ne dõmin su ƙãra laifi kawai kuma suna da azãba mai wulãƙantarwa.
3|179|Allah bai kasance yana barin mũminai a kan abin da kuke kansa ba, sai Ya rarrabe mummũna daga mai kyau. Kuma Al lah bai kasance Yanã sanar da ku gaibi ba. Kuma amma Allah Yana zãɓen wanda Ya so daga manzanninSa. Sabõda haka ku yi ĩmãni da Allah da manzanninSa Kuma idan kun yi ĩmãni kuma kuka yi taƙawa, to, kunã da lãdã mai girma.
3|180|Kuma kada waɗannan da suke yin rõwa da abin da Allah Ya bã su daga falalarSa su yi zaton shĩ ne mafi alhẽri a gare su A'a, shĩ mafi sharri ne a gare su. Zã a yi musu saƙandami da abin da suka yi rõwa da Shi a Rãnar ¡iyãma Kuma ga Allah gãdon sammai da ƙasa yake, kuma Allah, ga abin da kuke aikatãwa, Masani ne.
3|181|Lalle ne, haƙĩƙa Allah Yã ji maganar waɗanda suka ce: "Lalle ne, Allah faƙĩri ne, mũ ne wadãtattu." za mu rubũta abin da suka faɗa, da kisan da suka yi wa Annabãwa bã da wani haƙƙi ba kuma Mu ce: "Ku ɗanɗani azãbar gõbara!
3|182|"Wannan (azãbar) kuwa sabõda abin da hannuwanku suka gabãtar ne. Kuma lalle ne Allah bai zama mai zãlunci ga bãyinsa ba."
3|183|Waɗanda suka ce: "Lalle ne Allah Yã yi alkawari zuwa gare mu, kada mu yi ĩmãni sabõda wani Manzo sai yã zo mana da Baiko wadda wuta za ta ci." Ka ce: "Lalle ne wasu manzanni sun je muku, a gabãnĩna, da hujjõji bayyanannu, kuma da abin da kuka faɗa, to, don me kuka kashe su, idan kun kasance mãsu gaskiya?"
3|184|To, idan sun ƙaryata ka, to lalle ne, an ƙaryata wasu manzanni a gabãninka, sun je musu da hujjõji bayyanannu da littattafai, da kuma Littafi mai haske.
3|185|Kõwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne. Kuma ana cika muku ijãrõrinku kawai ne a Rãnar ¡iyãma. To, wanda aka nĩsantar daga barin wuta, kuma aka shigar da shi Aljanna, to, lalle ne yã tsĩra. Kuma rãyuwar dũniya ba ta zama ba fãce jin dãɗin rũɗi.
3|186|Lalle ne zã a jarraba ku a cikin dũkiyarku da rãyukanku, kuma lalle ne kuna jin cũtarwa mai yawa daga waɗanda aka bai wa Littãfi a gabãninku da kuma waɗanda suka yi shirki. Kuma idan kun yi haƙuri, kuma kuka yi taƙawa, to lalle ne, wannan yana daga manyan al'amurra.
3|187|Kuma a lõkacin da Allah Ya riƙi alkawarin waɗanda aka bai wa Littãfi, "Lalle ne kuna bayyana shi ga mutãne, kuma bã zã ku ɓõye shi ba." Sai suka jẽfarda shi a bãyan bãyansu, kuma suka sayi 'yan kuɗi kaɗan da shi. To, tir da abin da suke saye!
3|188|Kada lalle ka yi zaton waɗanda suke yin farin ciki da abin da suka bãyar, kuma suna son a yabe su da abin da ba su aikatã ba. To, kada lalle ka yi zaton su da tsĩra daga azãba. Kuma suna da azãba mai raɗadi.
3|189|Kuma ga Allah mulkin sammai da ƙasa yake. Kuma Allah, a kan kõme, Mai ĩkon yi ne.
3|190|Lalle ne, a cikin halittar sammai da ƙasa da sãɓãwar dare da yini akwai ãyõyi ga ma'abũta hankali.
3|191|Waɗanda suke ambatar Allah a tsaye da zaune da a kan sãsanninsu, kuma suna tunãni a kan halittar sammai da ƙasa: "Yã Ubangijinmu! Ba Ka halitta wannan a kan banza ba. TsarkinKa! Sabõda haka Ka tsare mu daga azãbar wuta.
3|192|"Ya Ubangijinmu! Lalle ne Kai, wanda Ka shigar a cikin wuta to, haƙĩƙa, Ka tozarta shi kuma bãbu wasu mataimaka ga azzãlumai.
3|193|"Yã Ubangijinmu! Lalle ne mũ mun ji Mai kira yanã kira zuwa ga ĩmãni cẽwa, 'Ku yi ĩmãni da Ubangijinku.' Sai muka yi ĩmãni. Yã Ubangijinmu! Sabõda haka Ka gãfarta mana zunubanmu, kuma Ka kankare miyãgun ayyukanmu daga gare mu. Kuma Ka karɓi rãyukanmu tãre da mutãnen kirki.
3|194|"Yã Ubangijinmu! Ka bã mu abin da Ka yi mana wa'adi (alkawari) a kan manzanninKa, kuma kada Ka tozarta mu a Rãnar ¡iyãma. Lalle ne Kai, bã Ka sãɓãwar alkawari."
3|195|Sabõda haka Ubangijinsu Ya karɓa musu cẽwa, "Lallene Nĩ bã zan tozartar da aikin wani mai aiki ba daga gare ku, namiji ne ko kuwa mace, sãshenku daga sãshe. To, waɗanda suka yi hijira kuma aka fitar da su daga gidãjensu, kuma aka cũtar da su a cikin hanyaTa, kuma suka yi yãƙi, kuma aka kashe su, lalle ne zan kankare musumiyagun ayyukansu, kuma lalle ne zan shigar da su gidãjen Aljanna (waɗanda) ƙoramu ke gudãna daga ƙarƙashinsu, a kan sakamako daga wurin Allah. Kuma a wurinSa akwai kyakkyawan sakamako.
3|196|Kada jujjuyawar waɗanda suka kãfirta a cikin garũruwa ta rũɗe ka.
3|197|Jin dãɗi ne kaɗan sa'an nan makõmarsu Jahannama ce, kuma tir da shimfiɗa ita!
3|198|Amma waɗanda suka bi Ubangijinsu da taƙawa sunã da Gidãjen Aljanna (waɗabda) ƙoramu ke gudãna a ƙarƙashinsu suna madawwama a cikinsu, a kan, liyãfa daga wurin Allah, kuma abin da ke wurin Allah ne mafi alhẽri ga barrantattu.
3|199|Kuma lalle ne daga Mutãnen Littãfi haƙĩƙa akwai wanda yake yin ĩmãnĩ da Allah da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar zuwa gare su, sunã mãsu tawãlu'i ga Allah, bã su sayen tamani kaɗan da ãyõyin Allah. Waɗannan suna da ijãrarsu a wurin Ubangijinsu. Lalle ne Allah Mai gaugãwar sakamako da yawa ne.
3|200|Yã ku waɗanda suka yi ĩmani! Ku yi haƙuri kuma ku yi dauriya, kuma ku yi zaman dãko, kuma ku yi taƙawa, tsammãninku zã ku ci nasara.
4|1|Ya ku mutãne! Ku bi Ubangijinku da taƙawa Wanda Ya halitta ku daga rai guda, kuma Ya halitta, daga gare shi, ma'auransa, kuma Ya watsa daga gare su maza mãsu yawa da mãtã. Kuma ku bi Allah da taƙawa Wanda kuke rõƙon jũna da (sũnan), shi, da kuma zumunta. Lalle ne Allah Ya kasance, a kanku, Mai tsaro ne.
4|2|Kuma ku bai wa marãyu dũkiyõyinsu, kuma kada ku musanya mummuna da mai kyau. Kuma kada ku ci dũkiyõyinsu zuwa ga dũkiyõyinku. Lalle shi, yã kasance zunubi ne mai girma.
4|3|Kuma idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci ba a cikin marãyu, to, (akwai yadda zã a yi) ku auri abin da ya yi muku dãɗi daga mãtã; biyu-biyu, da uku-uku, da huɗu-huɗu. Sa'an nan idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci ba, to, (ku auri) guda ko kuwa abin da hannayenku na dama suka mallaka. Wannan shi ne mafi kusantar zama ba ku wuce haddi ba.
4|4|Kuma ku bai wa mãtã sadãkõkĩnsu da sauƙin bãyarwa. Sa'an nan idan suka yãfe muku wani abu daga gare shi, da dãɗin rai, to, ku ci shi da jin dãɗi da sauƙin haɗiya.
4|5|Kada ku bai wa wãwãye dũkiyarku, wadda Allah Ya sanya ta a gare ku, kunã mãsu tsayuwa (ga gyãranta). Kuma ku ciyar da su a cikinta, kuma ku tufãtar da su, kuma ku gaya musu magana sananniya ta alhẽri.
4|6|Kuma ku jarraba marãyu, har a lõkacin da suka isa aure. To, idan kun lura da shiriya daga gare su, to, ku mĩƙa musu dũkiyõyinsu. Kada ku cĩ ta da ɓarna, kuma da gaggawa kãfin su girma. Kuma wanda yake wadãtacce, to, ya kãma kãnsa, kuma wanda yake faƙĩri, to, ya ci, gwargwadon yadda ya kamata. To, idan kun mĩƙa musu dũkiyõyinsu, sai ku shaidar a kansu. Kuma Allah Ya isa Ya zama Mai bincike.
4|7|Maza suna da rabo daga abin da iyãye biyu da mafi kusantar dangi suka bari, kuma mãtã suna da rabo daga abin da iyãye biyu da mafi kusantar dangi suka bari, daga abin da ya ƙaranta daga gare shi kõ kuwa ya yi yawa, rabo yankakke.
4|8|Kuma idan ma'abũta zumunta da marãyu da matalauta suka halarci rabon, to, ku azurta su daga gare shi, kuma ku faɗa musu magana sananniya ta alhẽri.
4|9|Kuma waɗanda suke dã sun bar zuriyya mãsu rauni a bãyansu, zã su ji tsõro a kansu, su yi sauna, sa'an nan su bi Allah da taƙawa, kuma su faɗi magana madaidaiciya.
4|10|Lalle ne, waɗanda suke cĩn dũkiyar marãyu da zãlunci, to, wuta kawai suke ci a cikin cikkunansu, kuma za su shiga cikin wata wuta mai tsanani.
4|11|Allah Yanã yi muku wasiyya a cikin 'ya'yanku; namiji yanã da rabon mãtã biyu. Idan sun kasance mãtã ne fiye da biyu kuwa, to, suna da biyu daga kashi uku ɗin abin da ya bari, kuma idan ta zama guda ce (kawai) to, tana da rabi. Kuma iyãyensa biyu kõwane ɗaya daga cikinsu yanã da ɗaya daga kashi shida ɗin abin da ya bari idan wani rẽshe ya kasance gare shi, to, idan rẽshe bai kasance gare shi ba, kuma iyãyensa ne (kawai) suka gãje shi, to, uwa tanã da sulusi (ɗaya daga cikin kashi uku). Sa'an nan idan 'yan'uwa sun kasance gare shi, to, uwarsa tana da sudusi (ɗaya daga cikin kashi shida) daga bayan wasiyya wadda ya yi kõ kuwa bãshi. Ubanninku da 'yã'yan ku, ba ku sani ba, wannensu ne mafi kusantar amfani, a gare ku. Yankawa daga Allah. Lalle ne, Allah Yã kasance Masani Mai hikima.
4|12|Kuma kunã da rabin abin da mãtanku na aure suka bari idan rẽshe bai kasance gare su ba. Sa'an nan idan rẽshe ya kasance gare su, to, kunã da rubu'i (ɗaya daga cikin kashi huɗu) daga abin da suka barin, daga bãyan wasiyya wadda suka yi kõ kuma bãshi. (Sũ) kuma suna da rubu'i daga abin da kuka bari idan rẽshe bai kasance ba gare ku, idan kuwa rẽshe ya kasance gare ku, to, sunã da sumuni (ɗaya daga cikin kashi takwas) daga abin da kuka bari, daga bãyan wasiyya wadda kuka yi kõ kuwa bãshi. Idan wani namiji ya kasance ana gãdon sa bisa kalãla, ko kuwa wata mace alhãli kuwa yana da ɗan'uwa kõ 'yar'uwa to, kõwane ɗaya daga cikinsu yana da sudusi (ɗaya daga cikin kashi shida), sai idan sun kasance mafi yawa daga wannan, to, sũ abõkan tãrayya ne a cikinsulusi (ɗaya bisa uku), daga bãyan wasiyya wadda aka yi kõ kuma bãshi. Bã da yana mai cũtarwa ba, ga wasiyya, daga Allah. Kuma Allah Masani ne Mai haƙuri.
4|13|Waɗancan iyãkõkin Allah ne. Wanda ya yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, (Allah) zai shigar da shi gidãjen Aljanna (waɗanda) ɗõramu suna gudana daga ƙarƙashinsu, suna madawwama a cikinsu, kuma wannan shi ne rabo babba.
4|14|Kuma wanda ya sãɓã wa Allah da ManzonSa, kuma ya ƙẽtare iyãkõkinSa, zai shigarda shi wuta, yana madawwami a cikinta, kuma yana da wata azãba mai walãkantarwa.
4|15|Kuma waɗanda suka je wa alfãsha daga mãtanku, to, ku nẽmi Shaidar mutãne huɗu daga gare ku a kansu. To, idan sun yi shaida, sai ku tsare su a cikin gidãje har mutuwa ta karɓi rãyukansu, ko kuwa Allah Ya sanya wata hanya a gare su.
4|16|Kuma waɗanda (mazã biyu) suka je mata daga ku, to, ku cũtar da su, sa'an nan idan sun tũba kuma suka kyautata hãlãyensu, sai ku kau da kai da ga barinsu. Lalle ne Allah Yã kasance Mai kaɓar tũba ne, Mai jin ƙai
4|17|Abar da take tũba kawai ga Allah, ita ce ga waɗanda suke aikatãwar mugun aiki da jãhilci sa'an nan su tũba nan kusa to, waɗannan Allah Yanã karɓar tũ barsu kuma Allah Yã kasance Masani ne, Mai hikima.
4|18|Bã tũba ba ce ga waɗanda suke aikatãwar mũnanan ayyuka har idan mutuwa ta halarci ɗayansu ya ce: "Lalle ne ni, na tũba yanzu," kuma bã tũba ba ce ga waɗanda suke mutuwa alhãli kuwa sunã kãfi rai Waɗannan mun yi musu tattalin wata azãba mai raɗaɗi
4|19|Ku waɗanda suka yi ĩmãni! Bã ya halatta a gare ku, ku gãji mãtã a kan tĩlas kuma kadaku hana su aure dõmin ku tafi da sãshen abin da kuka ba su, fãce idan suka zo da wata alfãsha bayya nanniya kuma ku yi zamantakẽwa da su da alhẽri sa'an nan idan kun ƙĩ su, to akwai tsammãnin ku ƙi wani abu alhãli kuwa Allah Ya sanya wani alhẽri mai yawaa cikinsa.
4|20|Kuma idan kun yi nufin musanya mãta a matsayin wata mãta, alhãli kuwa kun bai wa ɗayarsu ƙinɗari to kada ku karɓi kõme daga gare, shi, shin, zã ku karɓe shi da ƙarya da zunubi bãyyananne?
4|21|Kuma yãyã zã ku karɓe shi alhãli kuwa, haƙĩƙa, sãshenkuyã sãdu zuwa ga sãshe, kuma sun riƙi alkawari mai kauri daga gare ku?
4|22|Kuma kada ku auri abin da ubanninku suka aura daga mãtã, fãce abin da ya shige. Lalle ne shi, ya kasance alfãsha da abin ƙyãma. Kuma ya mũnana ya zama hanya.
4|23|An haramta muku uwãyenku, da 'yã'yanku, da 'yan'uwanku mãtã, da goggonninku, da innoninku, da 'yã'yan ɗan'uwa, da 'ya'yan 'yar'uwa, da uwãyenku waɗanan da suka shãyar da ku mãma, da 'yan'uwanku mãtã na shan mãma, da uwãyen mãtanku, da agõlolinku waɗanda suke cikin ɗãkunanku daga mãtanku, waɗanda kuka yi duhũli da su, kuma idan ba ku yi duhũli da sũ ba, to, bãbu laifi a kanku, da mãtan 'yã'yanku waɗanda, suke daga tsatsonku, kuma kada ku haɗa tsakanin 'yan'uwa biyu mãtã, fãce abin da ya shige. Lalle ne, Allah Yã kasance Mai gãfara ne Mai jin ƙai.
4|24|Da tsararrun auren wasu maza, fãce dai abin da hannuwanku suka mallaka. (Ku tsare) Littãfin Allah a kanku. Kuma an halatta muku abin da yake bayan wancan. Ku nẽma da dukiyõyinku, kunã mãsu yin aure, bã mãsu yin zina ba. sa'an nan abin da kuka ji daɗi da shi daga gare su, to, ku bã su ijãrõrinsu bisa farillar sadãki. Bãbu laifia gare ku ga abin da kuka yi yardatayya da shi a bãyan farillar sadãki. Lalle ne Allah Yã kasance Masani ne, Mai hikima.
4|25|Kuma wanda bai sãmi wadãta ba daga cikinku bisa ga ya auri 'ya'ya mũminai, to, (ya aura) daga abin da hannuwanku na dãma suka mallaka, daga kuyanginku mũminai. Kuma Allah ne Mafi sani ga ĩmãninku, sãshenku daga sãshe. Sai ku aurẽ su da izinin mutãnensu. Kuma ku bã su ijãrõrinsu bisa ga abin da aka sani, suna mãsu kamun kai bã mãsu zina ba, kuma bã mãsu riƙon abõkai ba. To, idan aka aure su, sai kuma suka zo da wata alfãsha, to, akwai a kansu rabin abin da ko a kan, 'ya'ya daga azãba. wancan (auren kuyanga) ga wanda ya ji tsõron wahala ne daga gare ku. Kuma ku yi haƙuri shi ne mafi alhẽri a gare ku. Kuma Allah Mai gãfara ne Mai jin ƙai.
4|26|Allah Yanã nufin Ya bayyana muku, kuma Ya shiryar da ku hanyõyin waɗanda suke a gabãninku kuma Ya karɓi tũbarku. Kuma Allah Masani ne Mai hikima.
4|27|Kuma Allah Yanã nufin Ya karɓi tũbarku. Kuma waɗanda suke bin sha'awõyi suna nufin ku karkata, karkata mai girma.
4|28|Allah Yana nufin Ya yi muku sauƙi, kuma an halitta mutum yana mai rauni.
4|29|Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku ci dũkiyõyinku a tsakãninku da yaudara, fãce idan ya kasance, daga fatauci ne, bisa yardatayya daga gare ku. Kuma kada ku kashe kãnku. Lalle ne Allah Yã kasance, game da ku, Mai jin ƙai ne.
4|30|Wanda ya aikata wancan bisa ta'adi da zãlunci, to, zã Mu ƙõne shi da Wuta. Kuma wannan yã kasance ga Allah (abu ne) mai sauƙi.
4|31|Idan kuka nĩsanci manyan abubuwan da ake hana ku aikatãwa, to, zã Mu kankare mũnanan ayyukanku daga gare ku, kuma Mu shigar da ku mashiga ta karimci.
4|32|Kuma kada ku yi gurin abin da Allah Ya fifita sãshenku da shi a kan sãshe; maza suna da rabo daga abin da suka tsirfanta, kuma mãtã suna da rabo daga abin da suka tsirfanta. Ku rõƙi Allah daga falalarSa. Lalle ne Allah Yã kasance ga dukkan kõme, Masani.
4|33|Kuma ga kõwa, Mun sanya magada daga abin da mahaifa da mafiya kusancin zumunta suka bari. Kuma waɗanda rantsuwõyinku suka ƙulla ku bã su rabonsu. Lalle ne, Allah Yã kasance, a kan dukkan kõme, Mahalarci.
4|34|Maza mãsu tsayuwa ne a kan mãtã, sabõda abin da Allah Ya fifita sãshensu da shi a kan sãshe kuma sabõda abin da suka ciyar daga dũkiyõyinsu. To, sãlihanmãtã mãsu ɗã'a ne, mãsu tsarẽwa ga gaibi sabõda abin da Allah Ya tsare. Kuma waɗanda kuke tsõron bijirewarsu, to, ku yi musu gargaɗi, kuma ku ƙaurace musu a cikin wurãren kwanciya, kuma ku dõke su. Sa'an nan kuma, idan sun yi muku ɗa'a, to, kada ku nẽmiwata hanya a kansu. Lalle ne Allah Yã kasance Maɗaukaki, Mai girma.
4|35|Kuma idan kun ji tsõron sãɓãwar tsakãninsu to ku aika da wani mai sulhu daga mutãnensa da wani mai sulhu daga mutãnenta. Idan sun yi nufin gyãrãwa, Allah zai daidaita tsakãninsu (ma'auran). Lalle ne Allah Yã kasance Masani Mai jarrabãwa.
4|36|Kuma ku bauta wa Allah kuma kada ku haɗa wani da Shi, kuma ga mahaifa ku yi kyautatãwa, kuma ga ma'abũcin zumunta da marãyu da matalauta, da maƙwabci ma'abũcin kusanta, da maƙwabci manĩsanci, da abõki a gẽfe da ɗan hanya, da abin da hannuwanku na dãma suka mallaka. Lalle ne Allah bã Ya son wanda ya kasance mai tãƙama, mai yawan alfahari.
4|37|Waɗanda suke yin rõwa, kuma sunã umurnin mutãne da yin rõwa, kuma suna ɓõyewar abin da Allah Ya bã su na falalarSa. Kuma Mun yi tattali, sabõda kãfirai, azãba mai walãkantarwa.
4|38|Kuma waɗanda suke ciyar da dũkiyõyinsu dõmin nũna wa mutãne, kuma bã su yin ĩmãni da Allah, kuma bã su yin ĩmãnida Rãnar Lãhira kuma wanda Shaiɗan ya kasance abõkin haɗi a gare shi, to, yã mũnana ga abõkinhaɗi.
4|39|Kuma mẽne ne a kansu, idan sun yi ĩmãni da Allah, kumada Rãnar Lãhira, kuma sun ciyar da abin da Allah Yã azurtã su, kuma Allah Ya kasance, gare su, Masani?
4|40|Lalle ne, Allah bã Ya zãluncin gwargwadon nauyin zarra, idan ta kasance alhẽri ce, zai riɓanya ta, kuma Ya kãwo daga gunsa ijãra mai girma.
4|41|To, yãyã, idan Mun zo da shaidu daga dukkan al'umma, kuma Muka zo da kai a kan waɗannan, kana mai shaida!
4|42|A rãnar nan, waɗanda suka kãfirta kuma suka sãɓã wa Manzo, sunã gũrin dã an baje ƙasa dasu, kuma bã su ɓõye wa Allah wani labãri.
4|43|Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku kusanci salla alhãli kuwa kuna mãsu mãye, sai kun san abin da kuke faɗa kuma haka idan kuna mãsu janaba, fãce mai ƙẽtare hanya, har ku yi wanka. Kuma idan kun kasance majinyata, ko kuwa a kan tafiya ko kuwa wani daga cikinku, idan ya zo daga kãshi, kõ kuwa kun shãfi mãtã ba ku sãmi ruwa ba, to ku nufi, fuskar ƙasa mai kyau, ku yi shãfa ga fuskokinku da hannuwanku. Lalle ne Allah Yã kasance Mai yãfẽwa Mai gãfara.
4|44|Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda aka bai wa rabo daga Littafi, suna sayen ɓata, kuma suna nẽman ku ɓace daga hanya?
4|45|Kuma Allah ne Mafi sani ga maƙiyanku, kuma Allah Yã isa Ya zama Majibinci, kuma Yã isa Ya zama Mataimaki.
4|46|Daga waɗanda suka tũba (Yahũdu), akwai wasu sunã karkatar da magana daga wurãrenta suna cẽwa: "Munjiya kuma mun ƙiya, kuma ka jiya a wani wurin jiyãwa, kuma rã'ina (da ma'anar 'ruɓaɓɓe'), ka tsare mu," dõmin karkatarwa da harsunansu, kuma dõmin sũkã a cikin addini. Kuma dã lalle sũ, sun ce: "Mun jiya kuma mun yi ɗa'a, kuma ka saurãra kuma ka dãkata mana," haƙĩƙa, dã ya kasance mafi alhẽri a gare su, kuma mafi daidaita; amma Allah Yã la'anẽ su, sabõda kãfircinsu don haka bã zã su yi ĩmãni ba, sai kaɗan.
4|47|Yã kũ waɗanda aka bai wa Littãfi! Ku yi ĩmãni da abinda Muka saukar, yana mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da ku, tun gabanin Mu shãfe wasu fuskõki, sa'an nan Mu mayar da su a kan bãyayyakinsu, ko Mu la'ane su kamar yadda Muka la'ani masu Asabar. Kuma umurnin Allah ya kasance abin aikatãwa.
4|48|Lalle ne, Allah ba Ya gãfarta a yi shirki game da Shi, kuma Yana gãfarta abin da yake bãyan wannan ga wanda Yake so, kuma wanda ya yi shirki da Allah, to, lalle ne ya ƙirƙiri zunubi mai girma.
4|49|Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda suke tsarkake kansu? Ã'a, Allah ne Yake tsarkake wanda Yake so. Kuma ba za a zalunce su da zaren gurtsun dabĩno ba.
4|50|Ka dũba yadda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah! Kuma shi ya isa ga zama zunubi bayyananne.
4|51|Shin, ba ka gani ba zuwa ga waɗanda aka bai wa rabõ da ga Littafi suna ĩmãni da gunki da Shaiɗan kuma suna cẽwa ga waɗanda suka kãfirta: "Waɗannan ne mafiya shiriya daga waɗanda suka yi ĩmãni ga hanya"?
4|52|Waɗannan ne waɗanda Allah Ya la'ane su, kuma wanda Allah Ya la'ana to bã zã ka sãmi mataimaki a gare shi ba.
4|53|Ko suna da rabõ ne daga mulki? To, a sa'an nan bã zã su iya bai wa mutãne hancin gurtsun dabino ba.
4|54|Ko suna hãsadar mutãne ne a kan abin da Allah Ya bã su daga falalarSa? To, lalle ne, Mun bai wa gidan Ibrãhĩm Littãfida hikima kuma Mun bã su mulki mai girma.
4|55|To, daga cikinsu akwai wanda ya yi ĩmãni da shi, kuma daga cikinsu akwai wanda ya kange daga gare shi. Kuma yã isa Jahannama ta hũru da shi.
4|56|Lalle ne waɗanda suka kãfirta da ayõyinMu za Mu ƙõne su da wuta, kõ da yaushe fãtunsu suka nuna, sai Mu musanya musu wasu fãtun, dõmin su ɗanɗani azãba. Lalle ne Allah Yã kasance Mabuwãyi, Mai hikima.
4|57|Kuma waɗanda suka yiĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, zã Mu shigar da su gidãjen Aljanna, (waɗanda) ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã dawwamammu a cikinsu har abada suna da, a cikinsu, mãtan aure mãsu tsarki, Kuma Munã shigar da su a wata inuwa matabbaciyar lumshi.
4|58|Lalle ne Allah Yanã umurnin ku ku bãyar da amãnõni zuwa ga mãsu sũ. Kuma idan kun yi hukunci a tsakãnin mutãne, ku yi hukunci da ãdalci. Lalle ne Allah mãdalla da abin da Yake yi muku wa'azi da shi. Lalle ne Allah Yã kasance Mai ji ne, Mai gani.
4|59|Yã kũ waɗanda suka yiĩmãni! Ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga ManzonSa, da ma'abũta al'amari daga cikinku. Idan kun yi jãyayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa idan kun kasance kunã ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. wannan ne mafi alhẽri, kuma mafi kyau ga fassara.
4|60|Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda suke riyãwar cẽwa sunã ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare ka da abin da aka saukar daga gabãninka, sunã nufin su kai ƙãra zuwa ga ¦ãgũtu alhãli kuwa, lalle ne, an umurce su da su kãfirta da shi, kuma Shaiɗan yanã nẽman ya ɓatar da su, ɓatarwa mai nĩsa.
4|61|Kuma idan aka ce musu: "Ku zo zuwa ga abin da Allah Ya saukar, kuma zuwa ga Manzo" zã ka ga munãfukai sunã kange mutãne daga gare ka, kangẽwa.
4|62|To, yaya, idan wata masĩfa ta sãme su, sabõda abin da hannuwansu suka gabãtar sa'an nan kuma su je maka sunã rantsuwa da Allah cẽwa, "Ba mu yi nufin kõme ba sai kyautatawa da daidaitãwa."?
4|63|Waɗannan ne waɗanda Allah Ya san abin da ke cikin zukãtansu. Sabõda haka ka kau da kai daga gare su, kuma ka yi musu gargaɗi, kuma ka gaya musu, a cikin sha'anin kansu, magana mai nauyi da fasãha.
4|64|Kuma ba Mu aiki wani Manzo ba fãce dõmin a yi masa ɗã'a da izinin Allah. Kuma dã dai lalle sũ a lõkacin da suka zãlunci kansu, sun zo maka sa'an nan suka nẽmi gãfarar Allah kuma Manzo ya nẽma musu gãfara, haƙĩƙa, dã sun sãmi Allah Mai karɓar tũba Mai jin ƙai.
4|65|To, a'aha! Ina rantsuwa da Ubangijinka, ba za su yi ĩmãni ba, sai sun yarda da hukuncinka ga abin da ya sãɓa a tsakãninsu, sa'an nan kuma ba su sãmi wani ƙunci a cikin zukãtansu ba, daga abin da ka hukunta, kuma su sallama sallamãwa.
4|66|Kuma dã dai lalle Mũ, Mun wajabta musu cẽwa, "Ku kashe kanku, ko kuwa ku, fita daga gidãjenku," dã ba su aikata shi ba, fãce kaɗan daga gare su. Kuma dã dai lalle sũ sun aikata abin da ake yi musu gargaɗi da shi, haƙĩƙa, dã yã kasance mafi alhẽri dagagare su, kuma mafi tsanani ga tabbatarwa.
4|67|Kuma a sa'an nan, haƙĩƙa, dã Mun bã su, lãda mai girma, daga gunMu.
4|68|Kuma lalle ne, dã Mun shiryar da su hanya madaidaiciya.
4|69|Kuma waɗannan da suka yi ɗã'a ga Allah da Mazonsa, to, waɗannan sunã tãre da waɗanda Allah Ya yi ni'ima a kansu, daga annabãwa da mãsu yawan gaskatãwa, da masu shahãda da sãlihai. kuma waɗannan sun kyautatu ga zama abõkan tafiya.
4|70|Waccan falalar daga Allah take, kuma Allah Yã isa zama Masani.
4|71|Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku riƙi shirinku sa'an nan ku fitar da hari jama'a, jama'a ko ku fitar da yaƙi gaba ɗaya.
4|72|Kuma lalle ne daga cikinku akwai mai fãsarwa. To idan wata masĩfa ta sãme ku, sai ya ce: "Lalle ne, Allah Ya yi mini ni'ima dõmin ban kasance mahalarci tãre da su ba."
4|73|Kuma lalle ne idan wata falala daga Allah ta sãme ku haƙĩƙa, tabbas, yanã cẽwa, kamar wata sõyayya ba ta kasance a tsakãninku da shi ba: "Yã kaitona! Dã na zama tãre da su dai, dõmin in rabonta da rabõ mai girma!"
4|74|Sai waɗanda suke sayar da rayuwar dũniya su karɓi ta Lãhira su yi yãƙi, a cikin hanyar Allah. Kuma wanda ya yi yãki a cikin hanyar Allah to a kashe shi ko kuwa ya rinjãya, sa'an nan zã Mu ba shi ijãra mai girma.
4|75|Kuma mẽne ne ya sãme ku, bã ku yin yãƙi a cikin hanyar Allah, da waɗanda aka raunanar daga maza da mata da yãra sunã cewa: "Yã Ubangijinmu! Ka fitar da mu daga wannan alƙarya wadda mutãnenta suke da zãlunci, kuma Ka sanya mana majiɓinci daga gunKa, kuma Ka sanya mana mataimaki daga gunKa."?
4|76|Waɗanda suka yi ĩmãni, sunã yãki a cikin hanyar Allah, kuma waɗanda suka kãfirta sunã yãƙi a cikin hanyar ¦ãgũtu (Shaiɗan). To, ku yãƙi majiɓintan Shaiɗan. Lalle ne kaidin Shaiɗan yã kasance mai rauni.
4|77|Shin, ba ka gani ba zuwa ga waɗanda aka ce musu: "Ku kange hannuwanku, kuma ku tsayar da salla, kuma ku bãyar da zakka."? To a lõkacin da aka wajabta musu yãƙi sai ga wani ɓangare daga cikinsu sunã tsõron mutãne kamar tsõron Allah kõ kuwa mafi tsanani ga tsõron, kuma suka ce: "Ya Ubangijinmu! Don me Ka wajabta yãƙi a kanmu? Me ya hana Ka jinkirta mana zuwa ga wani ajali na kusa?"Ka ce: "Jin dãɗin dũniya kaɗan ne, kuma Lãhira ce mafi alhẽri ga wanda ya yi taƙawa. Kuma bã a zãluntar ku da sĩlĩlin hancin gurtsun dabĩno!
4|78|"Inda duk kuka kasance, mutuwa zã ta riske ku, kuma kõ da kun kasance ne a cikin gãnuwõyi ingãtattu!"Kuma idan wani alhẽri ya sãme su sai su ce: "Wannan daga wurin Allah ne," kuma idan wata cũta ta sãme su, sai su ce: "Wannan daga gare ka ne."Ka ce: "Dukkansu daga Allah ne." To, me ya sãmi waɗannan mutãne, bã su kusantar fahimtar magana?
4|79|Abin da ya sãme ka daga alhẽri, to, daga Allah yake, kuma abin da ya sãme ka daga sharri, to, daga kanka yake, kuma Mun aike ka zuwa ga mutãne, (kana) Manzo, kuma Allah Yã isa ga zama shaida.
4|80|Wanda ya yi ɗã'a ga Manzo, to, haƙĩƙa, yã yi ɗã'a ga Allah. Kuma wanda ya jũya bãya, to, ba Mu aike ka ba don ka zama mai tsaro a kansu.
4|81|Kuma sunã cẽwa, "Dã'a" sa'an nan idan sun fita daga wurinka, sai wata ƙungiya daga cikinsu ta kwãna da niyyar wanin abin da take faɗa, alhãli kuwa Allah na rubũta abin da suke kwãna da niyyarsa. Sabõda haka ka kau da kai daga gare su, kuma ka dõgara ga Allah, kuma Allah Yã isa ya zama wakĩli.
4|82|Shin, bã su kula da Alƙur'ãni, kuma dã yã kasance daga wurin wanin Allah haƙĩƙa, dã sun sãmu, a cikinsa, sãɓã wa jũnamai yawa?
4|83|Kuma idan wani al'amari daga aminci ko tsõro ya je musu, sai su wãtsa shi. Dã sun mayar da shi zuwa ga Manzo da ma'abũta al'amari daga gare su, lalle ne, waɗanda suke yin bincikensa, daga gare su, zã su san shi. Kuma bã dõmin falalar Allah bã a kanku da rahamarSa, haƙĩƙa, dã kun bi Shaiɗan fãce kaɗan.
4|84|Sabõda haka, ka yi yãƙi a cikin hanyar Allah, ba a kallafa maka ba, face a kanka, kuma ka kwaɗaitar da mũminai. Akwai tsammãnin Allah Ya kange gãfin waɗanda suka kãfirta, kuma Allah ne Mafi tsananin gãfi, kuma Mafi tsananin azabtãwa.
4|85|Wanda ya yi cẽto, cẽto mai kyau, zai sãmi rabo daga gare shi, kuma wanda ya yi cẽto, cẽto mummũna, zai sãmi ma'aunidaga gare shi, Kuma Allah Yã kasance, a kan dukkan kõme, Mai ƙayyade lõkaci.
4|86|Kuma idan an gaishe ku da wata gaisuwa, to, ku yi gaisuwa da abin da yake mafi kyau daga gare ta, kõ kuwa ku mayar da ita. Kuma Allah Yã kasance a kan dukkan kõme Mai lissãfi.
4|87|Allah bãbu abin bautawa face Shi. Lalle ne haƙĩƙa Yana tãra ku har zuwa ga Yinin ¡iyãma bãbu shakka a cikinsa. Kuma wãne ne mafi gaskiya daga Allah ga 1ãbãri.
4|88|To, mẽne ne ya sãme ku a cikin munãfukai kun zama ƙungiya biyu, alhãli kuwa Allah ne Ya mayar da su sabõda abin da suka tsirfanta? Shin, kunã nufin ku shiryar da wanda Allah Ya ɓatar ne? Kuma wanda Allah Ya ɓatar to bã zã ka sãmi wata hanya ba zuwa gare shi.
4|89|Suna gũrin ku kãfirta kamar yadda suka kãfirta, dõmin ku kasance daidai. Sabõda haka kada ku riƙi wasu masõya daga cikinsu, sai sun yõ hijira a cikin hanyar Allah. Sa'an nan idan sun jũya, to, ku kãmã su kuma ku kashe su inda duk kuka sãme su. Kuma kada ku riƙi wani masõyi daga gare su ko wani mataimaki.
4|90|Fãce dai waɗanda suke sãduwa zuwa ga wasu mutãne waɗanda a tsakãninku da su akwai alkawari, kõ kuwa waɗanda suke sun je muku (domin) ƙirãzansu sun yi ƙunci ga su yãke ku, kõ su yãƙi mutãnensu. Kuma dã Allah Yã so lalle ne, dã Yã bã su ĩko a kanku, sa'an nan, haƙĩka, su yãke ku. To, idan sun nĩsance ku sa'an nan ba su yãƙe ku ba, kuma suka jẽfa sulhu zuwa gare ku, to, Allah bai sanya wata hanya ba, a gare ku, a kansu.
4|91|Za ku sãmi wasu sunã nufin su amintar da ku kuma su amintar da mutãnensu, kõ da yaushe aka mayar da su ga fitina, sai a dulmuyã su a cikinta. To, idan ba su nĩsance ku ba, kuma sun jẽfa sulhu zuwa gare ku, kuma sun kange hannuwansu, to, ku kãmã su, kuma ku kashe su inda duk kuka kãmã su, kuma waɗannan, Mun sanya muku dalĩli bayyanannea kansu.
4|92|Kuma bã ya kasancẽwa ga mũmini ya kashe wani mũmini, fãce bisa ga kuskure. Kuma wanda ya kashe mũmini bisa ga kuskure, sai ya 'yanta wuya mũmina tare da mĩƙa diyya ga mutãnensa, ãce idan sun bari sadaka. Sa'an nan idan (wanda aka kashe) ya kasance daga wasu mutãne maƙiya a gare ku, kuma shi mũminine, sai ya 'yanta wuya mũmina. Kuma idan ya kasance daga wasu mutãne ne (waɗanda) a tsakãninku da tsakãninsu akwai alkawari, sai ya bãyar da diyya ga mutãnensa, tare da 'yanta wuya mũmina. To, wanda bai sãmi (wuyan ba) sai azumin watanni biyu jẽre, dõmin tũba daga Allah. Kuma Allah Yã kasance Masani, Mai hikima.
4|93|Kuma wanda ya kashe wani mũmini da ganganci, to, sakamakonsa Jahannama, yana madawwami a cikinta kuma Allah Yã yi fushi a kansa, kuma Ya la'ane shi, kuma Ya yi masa tattalin azãba mai girma.
4|94|Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun yi tafiya (a cikin ƙasa), dõmin jihãdi, to, ku nẽmi bãyani. Kuma kada ku ce wa wanda ya jĩfa sallama zuwa gare ku: "Bã Musulmi kake ba." Kunã nẽman hãjar rãyuwar dũniya, to, a wurin Allah akwai ganimõmi mãsu yawa. Kamar wannan ne kuka kasance a gabãnin ku musulunta, sa'an nan Allah Ya yi muku falala. Sabõda haka ku zan nẽman bayãni. Lalle ne Allah Yã kasance, ga abin da kuke aikatãwa, Masani.
4|95|Mãsu zama daga barin yãƙi daga mũminai, wasun ma'abũta larũra da mãsu jihãdi a cikin hanyar Allah da dũkiyõyinsu da rãyukansu, bã su zama daidai. Allah Yã fĩfĩta mãsu jihãdi da dũkiyoyinsu da rãyukansu a kan mãsu zama, ga daraja. Kuma dukansu Allah Yã yi musu alkawari da abu mai kyau. Kuma Allah yã fĩfĩta mãsu jihãdi a kan mãsu zama da lãda mai girma.
4|96|Darajõji daga gare Shi da gãfara da rahama. Kuma Allah Yã kasance Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
4|97|Lalle ne, waɗanda malã'ĩku suka karɓi rãyukansu, (alhãli) sunã mãsu zãluntar kansu, sun ce (musu): "A cikin me kuka kasance?" (Su kuma) suka ce: "Mun kasance waɗanda aka raunana a cikin ƙasa." Suka ce: "Ashe ƙasar Allah ba ta kasance mayalwaciya ba, dõmin ku yi hijira a cikinta?" To, waɗannan makõmarsu Jahannama ce. Kuma tã mũnana ta zama makõma.
4|98|Fãce waɗanda aka raunana daga maza da mãtã da yãra waɗanda bã su iya yin wata dabãra, kuma bã su shiryuwa ga hanya.
4|99|To, waɗannan akwai tsammãnin Allah Ya yãfe laifi daga gare su, kuma Allah Yã kasance Mai yãfẽwa ne, Mai gãfara.
4|100|Kuma wanda ya yi hijira a cikin hanyar Allah, zai sãmu, a cikin ƙasa, wurãren jũyãwa mãsu yawa da yalwa. Kuma wanda ya fita daga gidansa yana mai hijira zuwa ga Allah da ManzonSa, sa'an nan kuma mutuwa ta riske shi, to, lalle ne, lãdarsa tã auku ga Allah, Kuma Allah Yã kasance, a gare ku, Mai gãfara, Mai jin ƙai.
4|101|Kuma idan kun yi tafiya a cikin ƙasa to, bãbu laifi a kanku ku rage daga salla idan kun ji tsõron waɗanda suka kãfirta su fitine ku. Lalle ne kãfirai sun kasance, a gare ku, maƙiyi bayyananne.
4|102|Kuma idan kã kasance a cikinsu, sai ka tsayar musu da salla, to, wata ƙungiya daga gare su ta tsaya tãre da kai, kuma sai su riƙe makãmansu. Sa'an nan idan sun yi salla, to, sai su kasance daga bãyanku. Kuma wata ƙungiya ta dabam (ta) waɗanda ba su yi sallar ba, ta zo, sa'an nan su yi sallar tãre da kai. Kuma su riƙi shirinsu da makãmansu. Waɗanda suka kãfirta sun yi gũrin dã dai kuna shagala daga makamanku da kãyanku dõmin su karkata a kanku, karkata guda. Kuma bãbu laifi, a kanku idan wata cũta daga ruwan sama ta kasance a gare ku, kõ kuwa kun kasance mãsu jinya ga ku ajiye makãmanku kuma dai ku riƙi shirinku. Lalle ne, Allah Yã yi tattali, ga kãfirai, azãba mai walakantarwa.
4|103|Sa'an nan idan kun ƙãre salla, to ku ambaci Allah tsaye da zaune da a kan sãsanninku. Sa'an nan idan kun natsu, to, ku tsayar da Salla. Lalle ne salla tã kasance a kan mũminai, farilla mai ƙayyadaddun lõkuta.
4|104|Kuma kada ku sassauta a cikin nẽman mutãnen idankun kasance kuna jin zõgi, to, lalle sũ ma, suna jin zõgi kamar yadda kuke jin zõgi. Kuma kuna tsammãni, daga Allah, abin da bã su tsammãni. Kuma Allah Yã kasance Masani Mai hikima.
4|105|Lalle ne, Mũ, Mun saukar, zuwa gare ka, Littãfi da gaskiya, dõmin ka yi hukunci a tsakãnin mutãne da abin da Allah Ya nũna maka, kuma kada ka kasance mai husũma dõmin mãsu yaudara.
4|106|Kuma ka nẽmi Allah gãfara. Lalle ne Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai.
4|107|Kuma kada ka yi jãyayya dõmin tunkuɗe wa waɗanda suka yaudari kansu. Lalle ne Allah ba Ya son wanda ya kasance mai yawan hã'inci mai yawan zunubi.
4|108|Suna nẽman ɓõyewa daga mutãne kuma bã su nẽmanɓõyewa daga Allah, alhãli kuwa Shi Yana tãre da su a lõkacin da suke kwãna da niyyar yin abin da bã Ya yarda da shi daga maganar. Kuma Allah Yã kasance ga abin da suke aikatãwa Mai kẽwayẽwa.
4|109|Gã ku, yã waɗannan! Kun yi jidãli, dõmin tunkuɗe musu (kunya) a cikin rãyuwar dũniya, to, wane ne zai yi jidali domin tunkuɗe musu a Rãnar ¡iyãma? Ko kuwa wãne ne zai kasance wakĩli a kansu?
4|110|Kuma wanda ya aikata cũta kõ kuwa ya zãlunci kansa, sa'an nan kuma ya nẽmi Allah gãfara, zai sãmi Allah Mai gãfara, Mai jin ƙai.
4|111|Kuma wanda ya yi tsirfanci zunubi, to yanã tsirfarsa ne a kan kansa kawai. Kuma Allah Yã kasance Masani, Mai hikima.
4|112|Kuma wanda ya yi tsiwirwirin kuskure ko kuwa zunubi sa'an nan kuma ya jẽfi wani barrantacce da shi, to, lalle ne yã tattali ƙirƙiren ƙarya da zunubi bayyananne.
4|113|Kuma bã dõmin falalar Allah ba, a kanka, da rahamarSa, haƙĩƙa, dã wata ƙungiya daga gare su ta himmatu ga su ɓatar da kai. Kuma bã su ɓatarwa fãce kansu, kuma bã su cũtar ka daga kõme, Kuma Allah Yã saukar da Littãfi da hikima gare ka, kuma Ya sanar da kai abin da ba ka kasance kã sani ba. Kuma falalar Allah tã kasance mai girma a gare ka.
4|114|Bãbu wani alhẽri a cikin mãsu yawa daga gãnawarsu fãce wanda ya yi umurni da wata sadaka kõ kuwa wani alhẽri kõ kuwa gyãra a tsakãnin mutãne. Wanda ya aikata haka dõmin nẽman yardõdin Allah to zã Mu bã shi lãda mai girma.
4|115|Kuma wanda ya sãɓã wa Manzo daga bãyan shiriya tã bayyana a gare shi, kuma ya bi wanin hanyar mũminai, zã Mu jiɓintar masa abin da ya jiɓinta, kuma Mu ƙõne shi da Jahannama. Kuma tã mũnana ta zama makõma.
4|116|Lalle ne, Allah ba Ya gãfarta a yi shirki da Shi, kuma Yana gãfarta abin da yake bãyan wannan, ga wanda Yake so. Kuma wanda ya yi shirki da Allah, to, lalle ne ya ɓace ɓata mai nĩsa.
4|117|Bã su kiran kõwa, baicin Shi, fãce mãtã kuma bã su kiran kõwa fãce Shaiɗan, mai tsaurin kai.
4|118|Allah Yã la'ane shi. Kuma ya ce: "Lalle ne, zã ni riƙi rabõ yankakke, daga bãyinKa.
4|119|"Kuma lalle ne, inã ɓatar da su, kuma lalle ne inã sanya musu gũri, kuma lalle ne ina umurnin su dõmin su kãtse kunnuwan dabbõbi, kuma lalle ne inã umurnin su dõmin su canza halittar Allah." Kuma wanda ya riƙi Shaiɗan majiɓinci, baicin Allah, to, haƙĩƙa yã yi hasara, hasara bayyananniya.
4|120|Yanã yi musu alkawari, kuma yanã sanya musu gũri, alhãli Shaiɗan bã ya yi musu wani wa'adĩn kõme face ruɗi.
4|121|Waɗannan matattararsu Jahannama ce, kuma bã sãmun makarkata daga gare ta.
4|122|Kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, zã mu shigar da su gidãjen Aljanna (waɗanda) ƙõramu sunã gudãna a ƙarƙashinsu, sunã mãsu dawwama a cikinsu har abada bisa ga wa'adin Allah tabbatacce. Wãne ne mafi gaskiya daga Allah ga magana?
4|123|(Al'amari) bai zama gũrace- gũracenku ba, kuma ba gũrace- gũracen Mutãnen Littãfi ba ne. Wanda ya aikata mummunan aiki zã a sãka masa da shi kuma bã zai sãmi wani masõyi ba, baicin Allah, kuma bã zai sãmi mataimaki ba.
4|124|Kuma wanda ya yi aiki daga ayyukan ƙwarai, namiji ne ko kuwa mace, alhãli kuwa Yanã mũmini, to, waɗannan sunã shiga Aljanna kuma bã zã a zãlunce su da gwargwadon hancin gurtsun dabĩ no ba.
4|125|Kuma wãne ne ya fi kyau ga addini daga wanda ya sallama fuskarsa ga Allah, alhãli kuwa yanã mai kyautatawa kuma ya bi aƙidar Ibrãhĩm, Yanã mai karkata zuwa ga gaskiya? Allah Yã riƙi Ibrãhĩm badãɗayi.
4|126|Kuma Allah ke da (mallakar) abin da ke cikin sammai da kuma abin da ke cikin ƙasa kuma Allah Yã kasance, a dukkan, kõme, Mai kẽwayewa.
4|127|Sunã yi maka fatawa a cikin sha'anin mãtã. Ka ce: "Allah Yanã bayyana fatawarku a cikin sha'aninsu, da abin da ake karantãwa a kanku a cikin Littãfi, a cikin sha'anin marãyun mãtã waɗanda ba ku bã su abin da aka rubũta musu (na gãdo) ba, kuma kunã kwaɗayin ku aurẽ su, da sha'anin waɗanda aka raunana daga yãra, da sha'anin tsayuwarku ga marãyu da ãdalci. Kuma abin da kuka aikata daga alhẽri, to, lalle ne, Allah Yã kasance Masani a gare shi."
4|128|Kuma idan wata mace ta ji tsõron ƙiyo daga mijinta kõ kuwa bijirẽwa to, bãbu laifi a kansu su yi sulhu a tsakãninsu, sulhu (mai kyau) Kuma yin sulhu ne mafi alhẽri. Kuma an halartar wa rayũka yin rõwa. Kuma idan kun kyautata, kuma kuka yi taƙawa, to, lalle ne, Allah Yã kasance, ga abin da kuke aikatãwa, Masani.
4|129|Kuma bã zã ku iya yin ãdalci ba a tsakanin mãtã kõ dã kun yi kwaɗayin yi. Sabõda haka kada ku karkata, dukan karkata, har ku bar ta kamar wadda aka rãtaye. Kuma idan kun yi sulhu, kuma kuka yi taƙawa, to, lalle ne Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai.
4|130|Kuma idan sun rabu, Allah zai wadãtar da kõwanne daga yalwarSa. Kuma Allah Yã kasance Mayalwaci, Mai hikima.
4|131|Kuma Allah ne da mulkin abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun yi wasiyya ga waɗanda aka bai wa Littãfi a gabãninku, da kũ, cẽwa ku bi Allah da taƙawa, kuma idan kun kãfirta, to, lalle ne, Allah Yanã da abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa. Kuma Allah Yã kasance wadãtacce, Gõdadde.
4|132|Kuma Allah ne da mulkin abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa, kuma Allah Yã isa Ya zama wakĩli.
4|133|Idan Yã so, zã Ya tafi da ku, yã kũ mutãne! kuma Ya zo da wasu. Allah Yã kasance a kan haka, Mai ĩkon yi ne.
4|134|Wanda ya kasance Yanã nufin sakamakon dũniya, to, a wurin Allah sakamakon dũniya da Lãhira yake. Kuma Allah Yã kasance Mai ji, Mai gani.
4|135|Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kasance mãsu tsayuwa da ãdalci, mãsu shaida sabõda Allah, kuma kõ dã a kanku ne kõ kuwa, mahaifa da mafi kusantar zumunta, ko (wanda ake yi wa shaida kõ a kansa) ya kasance mawadãci kõ matalauci, to, Allah ne Mafi cancanta da al'amarinsu. Sabõda haka, kada ku bĩbiyi son zũciya, har ku karkata. Kuma idan kuka karkatar da magana, kõ kuwa kuka kau da kai, to lalle ne Allah Yã kasance Masani ga abin da kuke aikatãwa.
4|136|Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi ĩmãni da Allah da Manzonsa, da Littãfin da Ya sassaukar ga ManzonSa da Littãfin nan wanda Ya saukar daga gabãni. To, wanda ya kãfirta da Allah da malã'ikunSa, da LittattafanSa, da ManzanninSa, da Rãnar Lãhira, to, lalle ne yã ɓace, ɓata mai nĩsa.
4|137|Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, sa'an nan kuma suka kãfirta, sa'an nan kuma suka yi ĩmani, sa'an nan kuma suka kãfirta sa'an nan kuma suka ƙãra kãfirci, Allah bai kasance Yanã gãfarta musu ba, kuma bã zai shiryar da su ga hanya ba.
4|138|Ka yi wa munãfukai bushãra da cẽwa lalle ne sunã da azãba mai raɗaɗi.
4|139|Waɗanda suke riƙon kãfirai masõya, baicin mũminai. Shin sunã nẽman izza ne a wurinsu? To, lalle ne izza ga Allah take gabã ɗaya.
4|140|Kuma lalle ne Yã sassaukar muku a cikin Littãfi cẽwa idan kun ji ãyõyin Allah, anã kãfirta da su, kuma anã izgili da su, to, kada ku zauna tãre da sũ, sai sun shiga cikin wani lãbãri. Lalle ne kũ, a lõkacin nan misãlinsu kuke. Lalle ne, Allah Mai tãra munãfukai da kãfirai ne a cikin Jahannama gabã ɗaya.
4|141|Waɗanda suke jiran dãko game da ku; har idan wata nasara daga Allah ta kasance a gare ku, sai su ce: "Ashe, ba mu kasance tãre da kũ ba?" Kuma idan wani rabo ya sãmu ga kãfirai sai su ce: "Ashe ba mu rinjãye ku ba, kuma muka tsare ku daga mũminai?" To, Allah ne Yake yin hukunci tsakãninku a Rãnar ¡iyãma, kuma Allah bã zai sanya hanya ba ga kãfirai a kan mũminai.
4|142|Lalle ne munãfukai sunã yaudarẽwa da Allah, alhãli kuwa Shi ne mai yaudarasu; kuma idan sun tãshi zuwa ga salla, sai su tãshi sunã mãsu kasãla. Suna nũnawa mutãne, kuma ba su ambatar Allah sai kaɗan.
4|143|Mãsu kai-kawo ne a tsakãnin wancan; bã zuwa ga waɗannan ba, kuma bã zuwa ga waɗannan ba. Kuma wanda Allah Ya ɓatar, to, bã za ka sãmar masa wata hanya ba.
4|144|Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi kãfirai masõya, baicin mũminai. Shin, kanã nufin ku sanyã wa Allah dalĩli bayyananne a kanku?
4|145|Lalle ne, manãfukai sunã a magangara mafi ƙasƙanci daga wuta. Kuma bã zã ka sãma musu mataimaki ba.
4|146|Sai waɗanda suka tũba, kuma suka gyãra, kuma suka nẽmi fakuwa ga Allah, kuma suka tsarkake addininsu dõmin Allah, to, waɗannan sunã tãre da mũminai, kuma Allah zai bai wa mũminai lãda mai girma.
4|147|Mẽne ne Allah zai amfãna da yi maku azãba idan kun gõde, kuma kun yi ĩmãni? Allah Yã ksance Mai gõdiya Masani.
4|148|Allah bã Ya son bayyanãwa da mũnãna daga magana fãce ga wanda aka zãlunta. Kuma Allah Yã kasance Mai ji, Masani.
4|149|Idan kun bayyana alhẽri, kõ kuwa kuka ɓõye shi, kõ kuwa kuka yãfe laifi daga cũta, to, lalle ne Allah Yã kasance Mai yãfewa, Mai ikon yi.
4|150|Lalle ne, waɗanda uke kãfirta da Allah da ManzonSa kuma sunã nufin su rarrabe a tsakãnin Allah da manzanninSa, kuma sunã cẽwa: "Munã ĩmãni da sãshe, kuma munã kãfirta da sãshe." Kuma sunã nufin su riƙi hanya a tsakãnin wannan.
4|151|Waɗannan sũ ne kãfirai sõsai, kuma Mun yi tattali, dõmin kãfirai, azãba mai walãkantarwa.
4|152|Kuma waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da manzanninSa, kuma ba su rarrabe a tsakãnin kõwa ba daga gare su, waɗannan zã Mu bã su ijãrõrinsu, kuma Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai.
4|153|Mutãnen Littãfi sunã tambayar ka ka saukar da wani littãfi daga sama, a kansu, to, lalle ne sun tambayi Mũsã mũfã girma daga wannan, suka ce: "Ka nũna mana Allah bayyane." Sai tsãwa ta kãmã su sabõda zãluncinsu, sa'an nan kuma suka riƙi maraƙi (abin bautãwa) bãyan hujjoji bayyanannu sun je musu. Sa'an nan Muka yãfe laifi daga wancan. Kuma Mun bai wa Mũsã dalĩli bayyananne.
4|154|Kuma Muka ɗaukaka dũtse sãma da su, sabõda alkawarinsu, kuma Muka ce musu: "Ku shiga ƙõfar kunã mãsu tawãli'u," Kuma Muka ce musu: "Kada ku ƙẽtare haddi a cikin Asabat," kuma Muka riƙi alkawari mai kauri daga gare su."
4|155|To, sabõda warwarẽwarsu ga alkawarinsu, da kãfirtarsu da ãyõyin Allah, da kisansu ga Annabãwa, bã da hakki ba, da maganarsu: "Zukãtanmu sunã cikin rufi." Ã'a, Allah ne Ya yunƙe a kansu sabõda kãfircinsu, sabõda haka bã zã su yi ĩmãni ba fãce kaɗan.
4|156|Kuma sabõda kãfircinsu da faɗarsu, a kan Maryama, ƙiren ƙarya mai girma.
4|157|Da faɗarsu: "Lalle ne mu, mun kashe Masĩhu ĩsã ɗan Maryama Manzon Allah," alhãli kuwa ba su kashe shi ba, kuma ba su kẽre shi ba, kuma ammaan kamanta shi ne a garẽ su. Lalle ne waɗanda sauka sãɓã wa jũna a cikin sha'aninsa lalle ne, sunã shakka daga gare, shi, bã da wani ilmi fãce bin zato kuma ba su kashe shi ba bisa ga yaƙĩni.
4|158|Ã'a, Allah Ya ɗauke shi zuwa garẽ Shi, kuma Allah Yã kasance Mabuwãyi, Mai hikima.
4|159|Kuma bãbu kõwa daga Mutãnen Littafi, fãce lalle yanã ĩmãni da shi a gabãnin mutuwarsa, kuma a Rãnar ¡iyãma yana kasancẽwa mai shaida, a kansu.
4|160|To, sabõda zãlunci daga waɗanda suka tũba (Yahũdu) Muka haramta musu abũbuwa masu dãɗi waɗanda aka halatta su a gare su, kuma sabõda taushẽwarsu daga hanyar Allah da yawa.
4|161|Da karɓarsu ga riba, alhãli kuwa an hana su daga gare ta, da cin su ga dũkiyar mutãne daƙarya. Kuma Muka yi tattali, dõmin kãfirai, azãba mai raɗaɗi.
4|162|Amma tabbatattu a cikin ilmi daga gare su, da mũminai, suna ĩmani da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar daga gabãninka, madalla da masu tsai da salla, da mãsu bãyar da zakka, da mãsu ĩmãni daAllah da Rãnar Lãhira. Waɗannan zã Mu bã su lãda mai girma.
4|163|Lalle ne Mu, Mun yi wahayi zuwa gare ka, kamar yadda Muka yi wahayi zuwa ga Nũhu da annabãwa daga bãyansa. Kuma Mun yi wahayi zuwa ga Ibrãhĩma da Ismã'ĩla da Is'hãƙa da Yaƙũbu da jĩkõki da ĩsa da Ayũba da Yũnusa da Hãruna da Sulaimãn. Kuma Mun bai wa Dãwũda zabũra.
4|164|Da wasu Manzanni, haƙĩ ƙa, Mun bã da lãbarinsu a gare ka daga gabãni, da wasu manzanni waɗanda ba Mu bã da lãbãrinsu ba a gare ka, kuma Allah Yã yi magana da Mũsã, magana sõsai.
4|165|Manzanni mãsu bãyar da bushãra kuma mãsu gargaɗi dõmin kada wata hujja ta kasance ga mutãne a kan Allah bãyan Manzannin. Kuma Allah yã kasance Mabuwãyi, Mai hikima.
4|166|Amma Allah Yanã shaida da abin da Ya saukar zuwa gare ka. Yã saukar da shi da saninSa. Kuma malã'iku sunã shaida. Kuma Allah Yã isa Ya zama shaida.
4|167|Lalle ne, waɗanda suka kãfirta kuma suka kange (wasu mutãne) daga hanyar Allah, haƙĩƙa, sun ɓace, ɓata mai nĩsa.
4|168|Lalle ne waɗanda suka kãfirta, kuma suka yi zãlunci, Allah bai kasance Yana yi musu gãfara ba, kuma bã Ya shiryar da su ga hanya.
4|169|Fãce hanyar Jahannama, sunã mãsu dawwama a cikinta har abada, kuma wannan yã kasance, ga Allah, mai sauƙi.
4|170|Yã kũ mutãne! Haƙĩƙa, Manzo yã je muku da gaskiya daga Ubangijinku. Sabõda haka ku yi ĩmãni yã fi zama alhẽri a gare ku. Kuma idan kun kãfirta, to, Allah Yanã da abin da ke cikin sammai da ƙasa. Kuma Allah Yã kasance Masani, Mai hikima.
4|171|Yã Mutãnen Littãfi! Kada ku zurfafã a cikin addininku. Kuma kada ku faɗa, ga Allah, fãce gaskiya. Abin da aka sani kawai, Masĩ hu ĩsa ɗan Maryama Manzon Allah ne, kuma kalmarSa, yã jẽfa ta zuwa ga Maryama, kuma rũhi ne daga gare Shi. Sabõda haka, ku yi ĩmãni da Allah da manzanninSa, kuma kada ku ce, "Uku". Ku hanu (daga faɗin haka) yã fi zama alhẽri a gare ku. Abin da aka sani kawai, Allah Ubangiji ne Guda. TsarkinSa yã tabbata daga wani abin haifuwa ya kasance a gare Shi! Shĩ ne da abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa kuma Allah Yã isa Ya zama wakĩli.
4|172|Masĩhu bã ya ƙyãmar ya kasance bãwa ga Allah, kuma haka malã'ikun nan makusanta. Kuma wanda ya yi ƙyãmar bautarSa kuma yi yi girman kai, to, zai tãra su zuwa gare shi gabã ɗaya.
4|173|To, amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwaiai, to zã Ya cika musu ijãrõrinsu, kuma Yanã ƙãra musu daga falalarSa. Kuma amma waɗanda suka yi ƙyãma, kuma suka yi girman kai, to, zã Ya yi musu azãba, azãba mai raɗɗi kuma bã su samun wani masõyi dõmin kansu, baicin Allah, kuma bã su samun mataimaki.
4|174|Yã kũ mutãne! Haƙĩƙa wani dalĩli daga Ubangijinku yã je muku kuma Mun saukar da wani haske, bayyananne zuwa gare ku.
4|175|To, amma waɗanda suka yi ĩmãni da Allah kuma suka faku a gare Shi, to, zai shigar da su cikin wata rahama daga gare Shi da wata falala, kuma Ya shiryar da su zuwa gare Shi ga tafarki madaidaici.
4|176|Sunã yi maka fatawa. Ka ce: "Allah Yanã bayyana muku fatawa a cikin 'Kalãla."' Idan mutum ya halaka, ba shi da, rẽshe kuma yana da 'yar'uwa, to, tana da rabin abin da ya bari, kuma shi yana gãdon ta, idan wani rẽshe bai kasance ba a gare ta. Sa'an nan idan ('yan'uwa mãtã) suka kasance biyu, to suna da kashi biyu daga kashi uku ɗin abin da ya bari. Kuma idan sun kasance, 'yan'uwa, maza da mãtã to namiji yana da misãlin rabon mãtã biyu. Allah Yana bayyanawa a gare ku, dõmin kada ku ɓace. Kuma Allah ne, Masani ga dukan kõme.
5|1|Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! ku cika alkawurra. An halatta muku dabbobin jin dãɗi fãce abin da ake karantãwa a kanku, bã kunã mãsu halattar da farauta ba alhãli kuwa kunã mãsu harama. Lalle ne, Allah Yanã hukunta abin da yake nufi.
5|2|Ya kũ waɗanda suka yi ĩmãni! kada ku halattar da ayyukan ibãdar Allah game da hajji, kuma da watã mai alfarma, kuma da hadaya, kuma da rãtayar raƙuman hadaya, kuma da mãsu nufin ¦ãki mai alfarma, sunã neman falala daga Ubangijinsu da yarda. Kuma idan kun kwance harama, to, ku yi farauta. Kuma kada ƙiyayya da wasu mutãne ta ɗauke ku, dõmin sun kange ku daga Masallãci Mai alfarma, ga ku yi zãlunci. Kuma ku taimaki junã a kan aikin ƙwarai da taƙawa. Kuma kada ku taimaki juna a kan zunubi da zãlunci, kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne.
5|3|An haramta muku mũshe da jini da nãman alade da abin da aka ambaci sũnan wanin Allah a gare shi, da mãƙararriya da jefaffiya da mai gangarõwa da sõkakkiya, da abin da mãsu dãgi suka ci, fãce abin da kuka yanka, da abin da aka yanka a kan gunki (shĩ ma an haramta). Kuma kada ku yi rabo da kibiyoyi na cãca wannan fãsiƙanci ne, A yau waɗanda suka kãfirta sun yanke ƙauna daga addininku. Sabõda haka kada ku ji tsõronsu kuma ku ji tsõroNa. A yau Nã kammalã muku addininku, Kuma Nã cika ni'imaTa a kanku, Kuma Nã yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku. To, wanda aka sanya wa lalũra a cikin yunwa mai tsanani, bã yana mai karkata zuwa ga wani zunubi ba, to, lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
5|4|Suna tambayar ka cewa mene ne aka halatta musu? Ka ce: "An halatta muku abũbuwa mãsu dãɗi da abin da kuka sanar (farauta) daga mãsu yin mĩki, kunã mãsu sakinsu daga hannuwanku, kunã sanar da su daga abin da Allah Ya sanar da ku. To, ku ci daga abin da suka kama sabõda ku, kuma ku ambaci sunan Allah a kansa, kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle ne Allah Mai gaugawar sakamako da yawã ne.
5|5|A yau an halatta muku abũbuwa mãsu dãɗi kuma abincin waɗanda aka bai wa Littãfi halal ne a gare ku, kuma abincinku halal ne a gare su, da mãtã mãsu kãmun kai daga muminai da mãtã 'yã'ya daga waɗanda aka bai wa Littãfi a gabãninku idan kun je musu da sadãkõkinsu, kuna mãsu yin aure, ba masu yin zina ba, kuma bã mãsu riƙon abõkai ba. Kuma wanda ya kãfirta da ĩmãni to, lalle ne aikinsa yã ɓãci, kuma shĩ, a cikin Lãhira, yanã daga mãsu hasãra.
5|6|Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! idan kun tãshi zuwa ga salla, to, ku wanke fuskõkinku da hannuwanku zuwa ga magincirõri, kuma ku yi shãfa ga kãnunku, kuma ku (wanke) ƙafãfunku zuwa idãnun sãwu biyu. Kuma idan kun kasance mãsu janaba, to, ku yi tsarki, kuma idan kun kasance majinyata, kõ kuwa a kan tafiya, kõ kuwa ɗaya daga gare ku ya zo daga kãshi, kõ kuka yi shãfayyar junã da mãtã, sa'an nan ba ku sãmi ruwa ba to ku yi nufin wuri mai kyau, sa'an nan ku yi shãfa ga fuskõkinku da hannuwanku daga gare shi. Allah bã Ya nufi dõmin Ya sanya wani ƙunci a kanku, kuma amma Yanã nufi dõmin Ya cika ni'imarSa a kanku, tsammãninku kunã gõdewa.
5|7|Kuma ku tuna ni'imar Allah akanku da alkawarinku wanda Ya ɗaure ku da shi, a lõkacin da kuka ce: "Mun ji kuma mun yi ɗã'a Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle ne Allah Masani ne ga abin da ke a cikin zukata."
5|8|Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kasance mãsu tsayin daka dõmin Allah mãsu shaida da ãdalci. Kuma kada ƙiyayya da wasu mutane ta ɗauke ku a kan bã zã ku yi ãdalci ba. Ku yi ãdalci Shĩ ne mafi kusa ga taƙawa. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa.
5|9|Allah Yã yi wa'adi ga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai. Sunã da wata gãfara da lãda mai girma.
5|10|Kuma waɗanda suka kãfirta, kuma suka ƙaryatã, game da ãyõyinMu, waɗannan su ne abõkan wuta.
5|11|Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku tuna ni'imar Allah a kanku a lõkacin da wasu mutãne suka yi niyyar su shimfiɗa hannuwansu zuwa gare ku sai Ya kange hannuwansu daga gare ku, kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma sai muminai su dogara ga Allah kawai.
5|12|Kuma lalle Allah Yã riƙi alkawarin Banĩ lsrã' ĩla kuma Muka ayyana wakilai gõma shã biyu daga gare su kuma Allah Ya ce: "Lalle ne Nĩ, Inã tãre da ku, haƙĩƙa, idan kun tsayar da salla, kuma kun bãyar da zakka, kuma kun yi ĩmani da manzannĩNa, kuma kuka taimake su, kuma kuka bai wa Allah rance mai kyau, haƙĩƙa, Inã kankare laifukanku daga gare ku, kuma haƙĩƙa, Inã shigar da ku gidãjen Aljanna (waɗanda) ƙõramu sanã gudãna a ƙarƙashinsu, sa'an nan wanda ya kãfirta a bãyan wannan daga gare ku, to, lalle ne, yã ɓace daga tsakar hanya."
5|13|To, sabõda warwarewarsu ga alkawarinsu Muka la'ane su, kuma Muka sanya zukãtansu ƙeƙasassu, sunã karkatar da magana daga wurãrenta, kuma suka manta da wani yanki daga abin da aka tunãtar da su da shi, kuma bã zã ka gushe ba kana tsinkãyar yaudara daga gare su fãce kaɗan daga gare su. To, ka yãfe laifi daga gare su, kuma ka kau da kai. Lalle ne, Allah Yanã son mãsu kyautatãwa.
5|14|Kuma daga waɗanda suka ce: "Lalle ne mu Nasãra ne" Mun riƙi alkawarinsu, sai suka manta da wani yanki daga abin da aka tunãtar da su da shi, sai Muka shushuta adãwa da ƙeta a tsakãninsu har ya zuwa ga Rãnar ¡iyãma. Kuma Allah zai bã su lãbari da abin da suka kasance sunã sanã'antawa.
5|15|Yã Mutãnen littãfi! Lalle ne, ManzonMu yã je muku, yanã bayyana muku abu mai yawa daga abin da kuka kasance kunã ɓõyewa daga Littãfi, kuma yanã rangwame daga abu mai yawa. Haƙĩƙa, wani haske da wani Littafi mai bayyanãwa yã je muku daga Allah.
5|16|Dashĩ, Allah Yanã shiryar da wanda ya bi yardarsa zuwa ga hanyõyin aminci, kuma Yanã fitar da su daga duffai zuwa ga haske da izninsa, kuma Yanã shiryar da su zuwa ga hanya madaidaiciya.
5|17|Lalle haƙĩƙa waɗanda suka ce: "Lalle Allah Shĩ ne Masĩhu ɗan Maryama," sun kãfirta. Ka ce: "To, wane ne ke iya mallakar wani abu daga Allah, idan Yã nufi Ya halakar da Masĩhu ɗanMaryama da uwarsa da wanda yake a cikin ƙasa gabã ɗaya?" Kuma Allah ne da mallakar sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, Yanã halitta abin da Yake so. Kuma Allah a kan dukkan kõme, Mai ĩkon yi ne.
5|18|Kuma Yahudu da Nasãra sun ce: "Mu ne ɗiyan Allah, kuma masõyansa." Ka ce: "To, don me Yake yi muku azãba da zunubanku? Ã'a ku mutãne ne daga waɗanda Ya halitta, Yanã gãfartãwa ga wanda Yake so, kuma Yanã azabta wanda Yake so. Kuma Allah ne da mulkin sammai da ƙasa da abin da ke tsakãninsu kuma zuwa gare shi makomã take."
5|19|Yã Mutãnen Littãfi! Lalle ManzonMu yã je muku yanã bayyana muku, a kan lõkacin fatara daga manzanni, dõmin kada ku ce: "wani mai bayar da bushãra bai zo mana ba, kuma haka wani mai gargaɗi bai zo ba." To, haƙĩƙa, mai bãyar da bushãra da mai gargaɗi sunje muku. Kuma Allah ne, a kan dukkan kõme, Mai ĩkon yi.
5|20|Kuma a lõkacin da Musa ya ce wa mutãnensa: "Yã ku mutãnena! Ku tuna ni'imar Allah a kanku; dõmin Yã sanya annabãwa a cikinku, kuma Yã sanya ku sarãkuna, kuma Yã bã ku abin da bai bai wa kõwa ba daga tãlikai."
5|21|"Yã mutãnena! Ku shiga ƙasar nan, abar tsarkakewa, wadda Allah Ya rubuta sabõda ku, kuma kada ku kõma da bãya, har ku juya kunã mãsu hasara."
5|22|Suka ce: "Ya Musã! Lalle ne, a cikinta akwai wasu mutãne mãsu ƙarfi kuma lalle ne bã zã mu shige ta ba sai sun fice daga gare ta, to, idan sun fice daga gare ta, to, lalle ne mu, masu shiga ne."
5|23|Wasu maza biyu daga waɗanda suke tsõron Allah, Allah Yã yi ni'ima a kansu, suka ce: "Ku shiga gare su, daga ƙõfar, dõmin idan kuka shige shi, to, lalle ne ku, mãsu rinjãya ne, kuma ga Allah sai ku dogara idan kun kasance muminai."
5|24|Suka ce: "Ya Musa! Lalle ne mu, bã za mu shige ta ba har abada matuƙar sun dawwama a cikinta sai ka tafi kai da Ubangijinka dõmin ku yi yãƙi. Lalle ne mu, munã a nan zaune."
5|25|Ya ce: "Yã Ubangijina! Lalle ne nĩ, bã ni mallakar kõwa fãce kaina da ɗan'uwãna, sai Ka rarrabe a tsakãninmu da tsakãnin mutãne fãsiƙai."
5|26|(Allah) Ya ce: "To, lalle ne ita abar haramtãwa ce a gare su, shekara arba'in, sunã yin ɗimuwa a cikin ƙasa. Sabõda haka kada ka yi baƙin ciki a kan mutãne fãsiƙai."
5|27|Kuma karantã musu lãbãrin ɗiya biyu na Ãdamu, da gaskiya, a lõkacin da suka bãyar da baiko, sai aka karɓa daga ɗayansu kuma ba a karɓa daga ɗayan ba, ya ce: "Lalle ne zan kashe ka." (¦ayan kuma) ya ce: "Abin sani dai, Allah Yana karɓã daga mãsu taƙawa ne."
5|28|"Lalle ne idan ka shimfiɗa hannunka zuwa gare ni dõmin ka kashe ni, ban zama mai shimfiɗa hannuna zuwa gare ka ba dõmin in kashe ka. Lalle ne nĩ inã tsõron Allah Ubangijin tãlikai.
5|29|"Lalle ne nĩ inã nufin ka kõma da zunubina game da zunubinka, har ka kasance daga abõkan wuta. Kuma wannan shĩ ne sakamakon azzãlumai."
5|30|Sai ransa ya ƙawãtar masa kashewar ɗan'uwansa, sai kuwa ya kashe shi, sa'an nan ya wayi gari daga mãsu hasãra.
5|31|Sai Allah Ya aiki wani hankãka, yanã tõno a cikin ƙasa dõmin ya nuna masa yadda zai turbuɗe gãwar ɗan'uwansa. Ya ce: "Kaitõna! Nã kãsa in kasance kamar wannan hankãka dõmin in turbuɗe gãwar ɗan'uwana?" Sai ya wãyi gari daga mãsu nadãmã.
5|32|Daga sababin wannan, Muka rubuta a kan Banĩ lsrã'ĩla cewa, lalle ne wanda ya kashe rai bã da wani rai ba, ko ɓarna a cikin ƙasa, to kamar yã kashe mutãne duka ne, kuma wanda ya rãya rai, to, kamar yã rãyar da mutãne ne gabã ɗaya. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, ManzanninMu sun je musu da hujjõji bayyanannu, sa'an nan kuma lalle ne, mãsu yawa daga gare su, a bãyan wannan, haƙĩƙa, mãsuɓarna ne a cikin ƙasa.
5|33|Abin sani kawai sakamakon waɗanda suke Yãƙin Allah da Manzonsa, kuma sunã aiki a cikin ƙasa dõmin ɓarna a kashe su ko kuwa a ƙere su, kõ kuwa a kakkãtse hannuwansu da ƙafãfunsu daga sãɓãni, ko kuwa a kõre su daga ƙasa. Sannan gare su wulakanci ne a cikin rãyuwar duniya, kuma a Lãhira sunã da wata azãba mai girma.
5|34|Fãce fa waɗanda suka tuba tun a gabãnin ku sãmi ĩko akansu, to, ku sani cewa lalle ne, Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
5|35|Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa, kuma ku nemi tsari zuwa gare shi, kuma ku yi jihãdi a cikin hanyarsa, tsammãninku, za ku ci nasara.
5|36|Lalle ne waɗanda suka kãfirta, lalle dã sunã da abin da ke a cikin ƙasa gabã ɗaya da misãlinsa tãre da shi, dõmin su yi fansa da shi daga azãbar Rãnar ¡iyãma, bã a karɓarsa daga gare su, kuma sunã da azãba mai raɗadi.
5|37|Sunã nufin su fita ne daga wuta, kuma ba su zama mãsu fita daga gare ta ba, kuma sunã da azãba zaunanniya.
5|38|Kuma ɓarãwo da ɓarauniya sai ku yanke hannuwansu, bisa sakamako ga abin da suka tsirfanta, a kan azãba daga Allah. Kuma Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima.
5|39|To, wanda ya tuba a bãyan zãluncinsa, kuma ya gyãra (halinsa), to, lalle ne Allah Yanã karɓar tubarsa. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
5|40|Shin, ba ka sani ba cewa lalle ne, Allah Shi ne da mulkin sammai da ƙasa, Yanã azãbtar da wanda Yake so, kuma Yanã yin gãfara ga wanda yake so, kuma Allah a dukkan kõme, Mai ĩkon yi ne?
5|41|Yã kai Manzo! Kada waɗanda suke tseren gaugawa a cikin kãfirci su ɓãta maka rai, daga waɗanda suka ce: "Mun yi ĩmãni" da bãkunansu, alhãli zukatansu ba su yi ĩmãnin ba, kuma daga waɗanda suka tuba (watau Yahudu) mãsu yawan saurare ga wasu mutane na dabam waɗanda ba su je maka ba, sunã karkatar da zance daga bãyan wurarensa, sunã cewa: "Idan an bã ku wannan, to, ku karɓa, kuma idan ba a bã ku shĩ ba, to, ku yi sauna."Kuma wanda Allah Ya yi nufin fitinarsa, to bã zã ka mallaka masa kõme ba, daga Allah. Waɗannan ne waɗanda Allah bai yi nufin Ya tsarkake zukãtansu ba. Sunã da kunya a cikin duniya, kuma sunã da wata azãba mai girma a cikin 1ãhira.
5|42|Mãsu yawan saurãre ga ƙarya ne, mãsu yawan ci ga haram, to, idan sun zo maka, sai ka yi hukunci a tsakãninsu kõ ka bijira daga gare su. Kuma idan ka bijira daga gare su, to, bã zã su cuce ka da kõme ba, kuma idan ka yi hukunci, to, sai ka hukunta a tsakãninsu da ãdalci. Lalle ne, Allah Yanã son mãsu ãdalci.
5|43|Kuma yãya suke gabãtar da kai ga hukunci, alhãli a wurinsu akwai Attaura, a cikinta akwai hukuncin Allah, sa'an nan kuma sunã karkacewa a bãyan wannan? waɗannan bã muminai ba ne!
5|44|Lalle ne Mu, Mun saukar da Attaura, a cikinta akwai shiriya da haske Annabãwa waɗanda suke sun sallamã, sunã yin hukunci da ita ga waɗanda suka tuba (Yahudu), da mãlaman tarbiyya, da manyan malamai ga abin da aka neme su da su tsare daga Littãfin Allah, kuma sun kasance, a kansa, mãsu bã da shaida. To, kada ku ji tsõron mutãne kuma ku ji tsõroNa kuma kada ku sayi 'yan kuɗi kaɗan da ãyoyiNa. wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah Ya saukar, to, waɗannan su ne kafirai.
5|45|Kuma Mun rubuta a kansu, a cikinta cewa, lalle (anã kashe) rai sabõda rai, kuma (anã ɗebe) idõ sabõda idõ, kuma (ana katse) hanci sabõda hanci, kuma kunne sabõda kunne kuma haƙori sabõda haƙõri kuma a raunuka a yi sakayya. To, wanda ya yi sadaka da shi, to, shi kaffãra ce a gare shi. Kuma wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah Ya saukar, to, waɗannan su ne azzãlumai.
5|46|Kuma Muka biyar a kan gurãbansu da Ĩsa ɗan Maryama, yãnã mai gaskatãwa ga abin da yake a gaba gare shi daga Attaura, kuma Muka bã shi Injĩla a cikinsa akwai shiriya da haske, yanã mai gaskatãwa ga abin da yake a gaba gare shi daga Attaura, kuma shi shiriya ne da wa'azi ga mãsu taƙawa.
5|47|Kuma sai mutãnen injĩla su yi hukunci da abin da Allah ya saukar a cikinta. Kuma wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah ya saukar, to, waɗannan su ne fãsiƙai.
5|48|Kuma Mun saukar da Littãfi zuwa gare ka da gaskiya, yanã mai gaskatãwa ga abin da yake a gaba gare shi daga Littãfi (Attaura da Injĩla), kuma mai halartãwa a kansa. sai ka yi hukunci a tsakãninsu da abin da Allah Ya saukar kuma kada ka bĩbiyi son zũciyõyiniu daga abin da ya zo maka daga gaskiya. Ga kõwanne daga gare ku Mun sanya sharĩa da hanya (ta bin ta). Kuma dã Allah Yã so, dã Yã sanya ku al'umma guda, kuma amma dõmin Ya jarraba ku a cikin abin da Ya bã ku. Sai ku yi tsere ga ayyukan alheri. Zuwa ga Allah makõmarku take gabã ɗaya. Sa'an nan Ya bã ku lãbãri ga abin da kuka kasance kunã sãɓãwa a cikinsa.
5|49|Kuma ka yi hukunci a tsakãninsu da abin da Allah Ya saukar kuma kada ka bĩbiyi son zũciyõyinsu, kuma ka yi saunar su fitine ka daga sãshen abin da Allah Ya saukar zuwa gare ka. To, idan sun juya bãya, to, ka sani cewa, kawai Allah yana nufin Ya sãme su da masĩfa ne sabõda sãshen zunubansu. Kuma lalle ne, mãsu yawa daga mutãne, haƙĩƙa, fãsiƙai ne.
5|50|Shin, hukuncin Jãhiliyya suke nema? Kuma wane ne mafi kyau ga hukunci daga Allah sabõda mutãne waɗanda suke yin yaƙĩni (tabbataccen ĩmãni)?
5|51|Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi Yahudu da Nasãra majiɓinta. Sãshensu majiɓinci ne ga sãshe. Kuma wanda ya jiɓince su daga gare ku, to, lalle ne shĩ, yanã daga gare su. Lalle Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai.
5|52|Sai ka ga waɗanda a cikin zukatansu akwai cuta, sunã tseren gaugawa a cikinsu, sunã cewa: "Munã tsõron kada wata masĩfa ta sãme mu." To, akwai tsammãnin Allah Ya zo da buɗi, kõ kuwa wani umurni daga wurinSa, har su wãyi gari a kan abin da suka ɓõye a cikin zukatansu, sunã mãsu nadãmã.
5|53|Kuma waɗanda suka yi ĩmãni sunã cewa: "Shin, waɗannan ne waɗanda suka yi rantsuwa da Allah iyãkar rantsuwõyinsu, cewa su, lalle sunã tãre da ku?" Ayyukansu sun ɓãci, sabõda haka suka wãyi gari sunã mãsu hasãra.
5|54|Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! wanda ya yi ridda daga gare ku daga addininSa, to, Allah zai zo da wasu mutãne, Yanã son su kuma sunã son Sa, mãsu tawãlu'i a kan muminai mãsu izza a kan kãfurai. Sunã yin, jihãdi a cikin hanyar Allah, kuma bã su tsõron zargin wani mai zargi. Waccan falalar Allah ce, Yanã bãyar da ita ga wanda Yake so. Kuma Allah Mayalwaci ne, Mai ilmi.
5|55|Abin sani kawai, majiɓincinku Allah ne da ManzonSa da waɗanda suka yi ĩmãni, waɗanda suke sunã tsayar da salla kuma sunã bãyar da zakka kuma sunã ruku'i,
5|56|Kuma wanda ya jiɓinci Allah da ManzonSa da waɗanda suka yi ĩmãni, to, ƙungiyar Allah sune mãsu rinjãya.
5|57|Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi waɗanda suka riƙi addininku bisa izgili da wãsa, daga waɗanda aka bai wa Littãfi daga gabãninku da kãfirai, masõya, Kuma ku bi Allah da taƙawa idan kun kasance muminai.
5|58|Kuma idan kuka yi kira zuwa ga salla, sai su riƙe ta bisa izgili da wãsa. Wannan dõmin lalle ne su, mutãne ne (waɗanda) bã su hankalta.
5|59|Ka ce: "Ya Mutãnen Littãfi! Shin, kunã ganin wani laifi daga gare mu? Fãce dai dõmin mun yi ĩmãni da Allah da abin da aka Saukar zuwa gare mu da abin da aka saukar daga gabãni, kuma dõmin mafi yawanku fãsiƙai ne."
5|60|Ka ce: "Shin, in gaya muku mafi sharri daga wannan, dõmin sakamako daga wurin Allah? wanda Allah Ya la'ane shi kuma Ya yi fushi da shi, kuma Ya sanya daga gare su birai da aladai, kuma ya bauta wa ¦ãguta. Waɗannan ne mafiya sharrin wuri, kuma mafiya ɓata daga tsakar hanya."
5|61|Kuma idan sun zo muku sai su ce: "Mun yi ĩmãni." Alhãli kuwa haƙĩƙa, sun shigo da kãfirci, kuma su lalle ne, sun fita da shi, kuma Allah ne Mafi sani ga abin da suka kasance sunã ɓõyewa.
5|62|Kuma kana ganin mãsu yawa daga gare su, sunã tseren gaugawa a cikin zunubi da zãlunci da cinsu ga haram. Haƙĩƙa, tir da abin da suka kasance suna aikatãwa.
5|63|Don me Malaman Tarbiyya da manyan malamai (na Yahudu) ba su hanã su daga faɗarsu ga zunubi da cinsu ga haram ba? Haƙiƙa, tir daga abin da suka kasance sunã sanã'antãwa.
5|64|Kuma Yahudu suka ce: "Hannun Allah abin yi wa ƙuƙumi ne. " An sanya hannuwansu a cikin ƙuƙumi! Kuma an la'ane su sabõda abin da suka faɗa. Ã'a, hannuwanSa biyu shimfiɗaɗɗu ne, Yanã ciyarwa yadda Yake so. Kuma lalle ne abin da aka saukar zuwa gare ka yanã ƙãra wa mãsu yawa daga gare su, girman kai da kãfirci. Kuma Mun jefa a tsakãninsu, ƙiyayya da ƙeta, zuwa Rãnar ¡iyãma, kõ da yaushe suka hura wata wuta dõmin yãƙi, sai Allah Ya bice ta. Sunã aiki a cikin ƙasa dõmin ɓarna, alhãli kuwa Allah bã Ya son mãsu fasãdi.
5|65|Kuma dã dai lalle Mutãnen Littãfi sun yi ĩmãni, kuma sun yi taƙawa, haƙĩƙa, dã Mun kankare miyãgun ayyukansu daga gare su, kuma dã Mun shigar da su gidãjen Aljannar Ni'ima.
5|66|Kuma dã dai lalle su, sun tsayar da Attaura da Injĩla da abin da aka saukar zuwa gare su daga Ubangijinsu, haƙĩƙa, dã sun ci daga bisansu da kuma daga ƙarƙashin ƙafãfunsu. Daga gare su akwai wata al'umma mai tsakaitãwa kuma mãsu yawa daga gare su, abin da suke aikatawa yã munana.
5|67|Yã kai Manzo! Ka iyar da abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka. Kuma idan ba ka aikata ba, to, ba ka iyar da manzancinSa ba ke nan. Kuma Allah Yanã tsare ka daga mutãne. Lalle ne, Allah bã Ya shiryar da mutãne kãfirai.
5|68|Ka ce: "Yã ku Mutãnen Littãfi! Ba ku zama a kan kõme ba, sai kun tsayar da Attaura da Injĩla da abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku."Kuma lalle ne, abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka, yanã ƙara wa mãsu yawa daga gare su girman kai da kãfirci. To, kada ka yi baƙin ciki a kan mutãne kãfirai.
5|69|Lalle ne, waɗanda suka yi ĩmãni da waɗanda sukatuba (Yahũdu) da Karkatattu da Nasãra, wanda ya yi ĩmãni da Allahda Rãnar Lãhira, kuma ya aikata aiki na ƙwarai, to, bãbu tsõro a kansu, kuma bã su zamo sunã baƙin ciki ba.
5|70|Lalle ne haƙĩƙa Mun riƙi alkawarin Bani Isrã'ĩla, kumaMun aiki manzanni zuwa gare su, ko da yaushe wani manzo ya je musu da abin da rãyukansu bã su so, wani ɓangare sun ƙaryata, kuma wani ɓangare sunã kashewa,
5|71|Kuma suka yi zaton cewa wata fitina bã zã ta kasance ba sai Suka makanta, kuma suka kurubta, sa'an nan Allah Ya karɓi tuba a gare su, sa'an nan suka makanta kuma suka kurunta mãsu yawa daga gare su, alhãli Allah Mai gani ne ga abin da suke aikatãwa.
5|72|Lalle ne haƙĩƙa waɗanda suka ce: "Lalle ne Allah, shĩne Masĩhu, ɗan Maryama," sun kãfirta. Alhãli kuwa Masĩhu yã ce: "Yã Banĩ Isrã'ĩla! Ku bauta wa Allah Ubangijina, kuma Ubangijinku." Lalle ne shĩ, wanda ya yi shirki da Allah, to, lalle ne, Allah Yã haramta masa Aljanna. Kuma bãbu wasu mataimaka ga azzãlumai.
5|73|Lalle ne, haƙĩƙa, waɗanda suka ce: "Allah na ukun uku ne," sun kãfirta, kuma babu wani abin bautãwa fãce Ubangji Guda. Kuma idan ba su hanu daga abin da suke faɗa ba, haƙĩƙa, wata azãba mai raɗaɗi tãnã shãfar waɗanda suka kãfirta daga gare su.
5|74|shin fã, bã su tuba zuwa ga Allah, kuma su neme Shi gãfara, alhãli kuwa Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai?
5|75|Masĩhu ɗan Maryama bai zama ba fãce Manzo ne kawai, haƙĩƙa, manzanni sun shige dage gabãninsa, kuma uwarsa siddika ce. Sun kasance sunã cin abinci. Ka duba yadda Muke bayyana musu ãyõyi. Sa'an nan kuma ka duba yadda ake karkatar da su.
5|76|Ka ce: "Ashe kunã bauta wa, baicin Allah, abin da ba ya mallakar wata cuta sabõda ku kuma haka wani amfani alhãli kuwa Allah Shi ne Mai ji, Masani?"
5|77|Ka ce: "Yã ku Mutanen Littãfi! Kada ku zurfafa a cikin addininku, abin da bã gaskiya ba, kuma kada ku bĩbiyi son zuciyõyin waɗansu mutãne waɗanda suka riga suka ɓace a gabãni, kuma suka ɓatar da wasu mãsu yawa, kuma suka ɓace daga tsakar hanya."
5|78|An la'ani waɗanda suka kãfirta daga Banĩ Isrã'ĩla a kan harshen Dãwuda da Ĩsa ɗan Maryama. wannan kuwa sabõda sãɓãwar da suka yi ne, kuma sun kasance suna ta'addi.
5|79|Sun kasance bã su hana juna daga abin ƙi, wanda suka aikata. Haƙĩƙa abin da suka kasancesunã aikatãwa yã munana.
5|80|Kana ganin mãsu yawa daga gare su, sunã jiɓintar waɗanda suka kãfirta. Haƙĩƙa tir da abin da rãyukansu suka gabãtar sabõda su, watau Allah Yã yi fushi da su, kuma a cikin azãba su mãsu dawwama ne
5|81|Kuma dã sun kasance sunã ĩmãni da Allah da Annabi da abin da aka saukar zuwa gare shi, dã ba su riƙe su masõya ba. Kuma amma mãsu yawa daga gare su, fãsiƙai ne.
5|82|Lalle ne kana sãmun mafiya tsananin mutãne a adãwa ga waɗanda suka yi ĩmãni, Yahudu ne da waɗanda suka yi shirki. Kuma lalle ne kanã sãmun mafiya kusantarsu a sõyayya ga waɗanda suka yi ĩmãni su ne waɗanda suka ce: "Lalle mu ne Nasãra." Wancan kuwa sabõda akwai ¡issawa da ruhubãnãwa daga cikinsu. Kuma lalle ne su, bã su yin girman kai.
5|83|Kuma idan suka ji abin da aka saukar zuwa ga Manzo, kanã ganin idanunsu sunã zubar da hawãye, sabõda abin da suka sani daga gaskiya, sunã cewa: "Yã Ubangijinmu! Mun yi ĩmãni, sai ka rubuta mu tãre da mãsu shaida.
5|84|"Kuma mene ne yake gare mu, bã zã mu yi ĩmãni daAllah ba, da kuma abin da ya zo mana daga gaskiya, kuma munã gurin Ubangijinmu Ya shigar da mu tãre da mutãne sãlihai?"
5|85|Sabõda haka, Allah Yã sãkã musu, dõmin abin da suka faɗa da gidãjen Aljanna (waɗanda) ƙõramu sunã gudãna a ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu, kuma wannan ne sakamakon mãsu kyautatãwa.
5|86|Kuma waɗanda suka kãfirta kuma suka ƙaryata game da ãyõyinMu, waɗancan ne abõkan Wuta.
5|87|Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku haramta abubuwa mãsu dãɗi da Allah Ya halatta muku, kuma kada ku ƙetare haddi. Lalle ne, Allah bã Ya son mãsu ƙetare haddi.
5|88|Kuma ku ci daga abin da Allah Ya azurta ku, halat mai daɗi, kuma ku bi Allah da taƙawa, wanda yake ku, mãsu ĩmãni ne da shi.
5|89|Allah bã Ya kãmã ku sabõda yãsassa a cikin rantsuwõyinku, kuma amma Yanã kãmã ku da abin da kuka ƙudurta rantsuwõyi (a kansa). To, kaffãrarsa ita ce ciyar da miskĩni gõma daga matsakaicin abin da kuke ciyar da iyãlanku, kõ kuwa tufãtar da su, kõ kuwa 'yantãwar wuya. Sa'an nan wanda bai sãmu ba, sai azumin kwãna uku. wannan ne kaffãrar rantsuwõyinku, idan kun rantse. Kuma ku kiyãye rantsuwoyinku. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana muku ãyoyinsa, tsammãninku kunã gõdewa.
5|90|Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Abin sani kawai, giya da cãca da refu da kiban ƙuri'a, ƙazanta ne daga aikin shaiɗan, sai ku nĩsance shi, wa la'alla ku ci nasara.
5|91|Abin sani kawaĩ Shaiɗan yanã nufin ya aukar da adãwa da ƙeta a tsakãninku, a cikin giya da cãca, kuma ya kange ku daga ambaton Allah, kuma daga sallah. To, shin, ku mãsu hanuwa ne?
5|92|Ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga Manzo, kuma ku kiyãye. To, idan kun jũya, to, ku sani abin da kawai yake kan ManzonMu, iyarwa bayyananniya.
5|93|Bãbu laifi a kan waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, a cikin abin da suka ci, idan sun yi taƙawa kuma suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sa'an nan suka yi taƙawa kuma suka yi ĩmãni, sa'an nan kuma suka yi taƙawa kuma suka kyautata. Kuma Allah Yana son mãsu kyautatãwa.
5|94|Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Lalle ne, Allah zai jarraba ku da wani abu, daga farauta, hannuwanku da mãsunku sunã sãmun sa dõmin Allah Ya san wanda yake tsoron Sa a fake. To, wanda ya yi ta'addi a bãyan wannan, to, yanã da azãba mai raɗaɗi.
5|95|Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku kashe farauta alhãli kunã mãsu harama. Kuma wanda ya kashe shi daga gare ku, yanã mai ganganci, sai sakamako misãlin abin da ya kashe, daga dabbõbin ni'ima, ma'abuta ãdalci biyu daga cikinku sunã yin hukunci da shi. Ya zama hadaya mai isa ga Ka'aba ko kuwa kaffãra da abincin miskĩnai ko kuwa a matsayinsa ya yi azumi dõmin ya ɗanɗani masifar al'amarinsa. Allah Yã yafe laifi daga abin da ya gabãta. Kuma wanda ya kõma, to, Allah zai yi azãbar rãmuwa daga gare shi, kuma Allah Mabuwãyi ne, ma'abũcin azabãr rãmuwa.
5|96|An halatta muku farautar ruwa da abincinsa dõmin jin dãɗi a gare ku, kuma dõmin matafiya. Kuma an haramta farautar tudu a kanku, matuƙar kun dawwama mãsu harama. Kuma ku bi Allah da taƙawa, wanda yake zuwa gare Shi ne ake tãra ku.
5|97|Allah Ya sanya Ka'aba ¦aki Tsararre, ma'aunin addini ga mutane, kuma Yã sanya watã Mai alfarma da hadaya da rãtayõyin Allah Yã san abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, kuma cewa lalle Allah, ga dukkan, kõme, Masani ne.
5|98|Ku sani cewa lalle Allah Mai tsananin uƙuba ne, kuma lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
5|99|Bãbu abin da yake a kan Manzo, sai iyarwa, kuma Allah Yanã sanin abin da kuke bayyanãwa da abin da kuke ɓõyewa.
5|100|Ka ce: "Mummuna da mai kyau bã su daidaita, kuma kõ dã yawan mummuan yã bã ka sha'awa. Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, yã ma'abuta hankula ko la'alla zã ku ci nasara."
5|101|Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku yi tambaya ga abubuwa, idan an bayyana muku (hukuncinsu) su ɓãta muku rai. Kuma idan kuka yi tambaya a gare su a lõkacin da ake saukar da Alƙur'ãni, zã a bayyana maku. Allah Yã yãfe laifi daga gare su, Allah Mai gãfara ne, Mai haƙuri.
5|102|Lalle ne wasu mutãne sun tambaye su daga gabãninku, sa'an nan kuma suka wãyi gari da su sanã kãfirai.
5|103|Kuma Allah bai sanya wata bahĩra ba, kuma haka sã'iba, kuma haka wasĩla, kuma haka hãmi, amma waɗanda suka kãfirta, su suke ƙirƙira ƙarya ga Allah, kuma mafi yawansu bã su hankalta.
5|104|Kuma idan aka ce musu: "Ku zo zuwa ga abin da Allah Ya saukar, kuma zuwa ga Manzo," sai su ce: "Mai isarmu shi ne abin da muka iske ubanninmu a kansa." Shin, kuma kõ dã ubanninsu sun kasance bã su sanin kõme kuma bã su shiryuwa?
5|105|Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku lazimci rãyukanku, wanda ya ɓace bã zai cuce ku ba idan kun shiryu, zuwa ga Allah makõmarku take gabã ɗaya. Sa'an nan Ya bã ku lãbari ga abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
5|106|Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Shaidar tsakãninku, idan mutuwa ta halarci ɗayanku, a lõkacin wasiyya, maza biyu ne ma'abuta ãdalci daga gare ku, kõ kuwa wasu biyu daga wasunku idan kun tafi a cikin ƙasa sa'an nan masĩfarmutuwa ta sãme ku. Kunã tsare su daga bãyan salla har su yi rantsuwa da Allah; idan kun yi shakka: "Bã mu sayen kuɗi da shi, kõ dã ya kasance ma'abucin zumunta kuma bã mu ɓõye shaidar Allah. Lalle ne mu, a lõkacin, haƙĩƙa, munã daga mãsu zunubi."
5|107|To, idan aka gane cewa lalle sũ, sun cancanci zunubi to sai wasu biyu su tsayu matsayibsu daga waɗanda suka karɓa daga gare su, mutãne biyu mafiya cancanta, sa'an nan su yi rantsuwa da Allah: "Lalle ne shaidarmu ce mafi gaskiya daga shaidarsu, kuma ba mu yi zãlunci ba. Lalle mu, a lõkacin haƙĩƙa, munã daga azzãlumai."
5|108|Wannan ne mafi kusantar su zo da shaida a kan fuskarta kõ kuwa su yi tsõron a tũre rantsuwõyi a bãyan rantsuwõyinsu. Kuma ku bi Allah da taƙawa kuma ku saurara, kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne fãsiƙai.
5|109|A ranar da Allah Yake tãra manzanni sa'an nan Ya ce: "Mene ne aka karɓa muku?" (zã) su ce: "Bãbu ilmi a gare mu. Lalle ne Kai, Kai ne Masanin abubuwan fake."
5|110|A lõkacin da Allah Ya ce: "Yã Ĩsã ɗan Maryama! Ka tuna ni'ima Ta a kanka, kuma a kan mahaifiyarka, a lõkacin da Na ƙarfafa ka da Rũhul ¡udusi, kanã yiwa mutãne magana a cikin shimfiɗar jariri, da kuma kanã dattijo. Kuma a lõkacin da Na sanar da kai rubutu da hikima da Attaura da Injĩla, kuma a lõkacin da kake yin halitta daga lãkã kamar surar tsuntsu da izinĩNa, sa'an nan ka hura a cikinta sai ta zama tsuntsu da izinĩNa, kuma kanã warkar da haifaffen makaho da kuturu, da izinĩNa, kuma a lõkacin da kake fitar da matattu da izinĩNa, kuma a lõkacin da Na kange Banĩ Isrã'ĩla daga gare ka, a lõkacin da ka je musu da hujjõji bayyanannu, sai waɗanda suka kãfirta daga cikinsu suka ce: 'Wannan bã kõme ba ne, fãce sihiri bayyananne.'
5|111|"Kuma a lõkacin da Na yi wahayi zuwa ga Hawãriyãwa cewa ku yi ĩmãni da Ni, kuma da ManzoNa. Suka ce: "Mun yi ĩmãni, kuma ka shaida da cewa lalle mu, mãsu sallamãwa ne."
5|112|A lõkacin da Hawarãyãwa suka ce: "Ya Ĩsa ɗan Maryam! shin, Ubangijinka Yanã iyãwa Ya saukar da kaɓaki a kanmu daga samã?" (Ĩsã) Ya ce: "Ku bi Allah da taƙawa idan kun kasance muminai."
5|113|Suka ce: "Munã nufin mu ci daga gare shi ne, kuma zukãtanmu su natsu kuma mu san cewa lalle ne, kã yi mana gaskiya, kuma mu kasance daga mãsu shaida a kansa."
5|114|Ĩsã ɗan Maryam ya ce: "Yã Allah. Ubangijinmu! Ka saukar da kaɓaki a kanmu daga sama dõmin ya zama ĩdi ga na farkonmu da na ƙarshenmu, kuma ya zama ãyã daga gare Ka. Ka azurta mu, kuma Kai ne Mafĩfĩcin mãsu azurtawa."
5|115|Allah Ya ce: "Lalle ne Nĩ mai saukar da shi ne a kanku sa'an nan wanda ya kãfirta daga gare ku, to, lalle ne Nĩ, Inã azabta shi, da wata azãba wadda bã Ni azabta ta ga kõwa daga tãlikai."
5|116|Kuma a lõkacin da Allah Ya ce: "Yã Ĩsã ɗan Maryama! Shin, kai ne ka ce wa mutãne, 'Ku riƙe ni, ni da uwata, abubuwan bautãwa biyu, baicin Allah?" (Ĩsã) Ya ce: "Tsarkinka yã tabbata! Bã ya kasancewa a gare ni, in faɗi abin da bãbu wani hakki a gare ni. Idan nã kasance nã faɗe shi, to lalle Ka san shi, Kanã sanin abin da ke a cikin raina, kuma bã ni sanin abin da ke a cikin nufinKa. Lalle ne Kai Masanin abubuwan fake ne."
5|117|"Ban faɗa musu ba fãce abin da Ka umurce ni da shi; watau: 'Ku bauta wa Allah Ubangijina kuma Ubangijinku;' kuma nã kasance mai shaida a kansu matuƙar nã dawwama a cikinsu, sa'an nan a lõkacin da Ka karɓi raina Kã kasance Kai ne mai tsaro a kansu, kuma Kai, a kan dukkan kõme, Halartacce ne.
5|118|"Idan Ka azabta su, to lalle ne su, bãyinKa ne, kuma idan Ka gãfarta musu, to, lalle ne Kai ne Mabuwayi Mai hikima."
5|119|Allah Ya ce: "Wannan ce rãnar da mãsu gaskiya, gaskiyarsu take amfãninsu. Sunã da gidãjen Aljanna, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu har abada. Allah Yã yarda da su, kuma sun yarda da Shi. wannan ne babban rabo mai girma."
5|120|Allah ne da mallakar sammai da ƙasa da abin da ke a cikinsu kuma shi, a kan dukkan kõme Mai ĩkon yi ne.
6|1|Gõdiya ta tabbata ga Allah wanda Ya halitta sammai da ƙasa, kuma Ya sanya duffai da haske, sa'an nan kuma waɗanda suka kãfirta, da Ubangijinsu suke karkacewa.
6|2|Shi ne wanda Ya halitta ku daga lãkã, sa'an nan kuma Ya yanka ajali alhãli wani ajali ambatacce yanã wurinSa. Sa'an nan kuma ku kunã yin shakka.
6|3|Kuma Shĩ ne Allah a cikin sammai, kuma a cikin ƙasa Yanã sanin asĩrinku da bayyanenku, kuma Yanã sanin abin da kuke yi na tsirfa.
6|4|Kuma wata ãyã daga Ubangijinsu ba zã ta jẽ musu ba, fãce su kasance, daga gare ta, mãsu bijirẽwa.
6|5|Sabõda haka, lalle sun ƙaryata (Manzo) game da gaskiya, a lõkacin da ta jẽ musu, to lãbãrun abin da suka kasance sunã izgili da shi, zã su jẽ musu.
6|6|Shin, ba su gani ba, da yawa Muka halakar da wani ƙarni daga gabãninsu, Mun mallaka musu, a ckikin ƙasa, abin da ba Mu mallaka muku ba kuma Muka saki sama a kansu tanã ta zuba, kuma Muka sanya kõguna sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sa'an nan Muka halakã su sabõda zunubansu kuma Muka ƙãga halittar wani ƙarni na dabam daga bayansu?
6|7|Kuma dã Mun sassaukar da wani littãfi, zuwa gare ka, a cikin takarda, sa'an nan suka taɓa shi da hannuwansu, lalle dã waɗanda suka kãfirta sun ce: "Wannan bai zama ba, face sihiri bayyananne."
6|8|Suka ce: "Don me ba a saukar da wani malã'ika ba a gare shi?" to dã Mun saukar da malã'ika haƙĩƙa dã an hukunta al'amarin sa'an nan kuma ba zã a yi musu jinkiri ba.
6|9|Kuma dã Mun sanya malã'ika ya zama manzo lalle ne dã Mun mayar da shi mutum, kuma dã Mun rikita musu abin da suke rikitãwa.
6|10|Kuma lalle ne, haƙĩƙa, an yi izgili da manzanni daga gabaninka, sai waɗanda suka yi izgilin, abin da suka kasance sunã izgili da shi ya fãɗa musu.
6|11|Ka ce: "Ku yi tafiya a cikin ƙasa, sa'an nan kuma ku dũba yadda ãƙibar mãsu ƙaryatãwa ta kasance."
6|12|Ka ce: "Na wãne ne abin da yake a cikin sammai da ƙasa?" Ka ce: "Na Allah ne." Yã wajabta rahama ga kanSa. Lalle ne Yanã tãra ku zuwa ga Rãnar ¡iyãma, babu shakka a gare Shi. Waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu, to, sũ ba zã su yi ĩmani ba."
6|13|"Kuma Shĩ ne da mallakar abin da ya yi kawaici a cikin dare da yini, kuma Shi ne Mai ji, Masani."
6|14|Ka ce: "Shin, wanin Allah nike riƙo majiɓinci, (alhãli Allah ne) Mai ƙãga halittar sammai da ƙasa, kuma Shi, Yanã ciyarwa, kuma ba a ciyar da Shi?" Ka ce: "Lalle ne nĩ, an umurce ni da in kasance farkon wanda ya sallama, kuma kada lalle ku kasance daga mãsu shirki."
6|15|Kace: "Lalle ne nĩ inã tsõron azãbar Yini Mai girma, idan nã sãɓã wa Ubangijina."
6|16|"Wanda aka jũyar da shi daga gare shi, a wannan Rãnar, to, lalle ne, (Allah) Yã yi masa rahama, Kuma wannan ne tsĩra bayyananniya."
6|17|"Idan Allah Ya shãfe ka da wata cũta, to, babu mai kuranyẽwa gare ta, fãce Shĩ, kuma idanYa shãfe ka da wani alhẽri to shĩ ne, a kan kõme, Mai ĩkon yi."
6|18|"Kuma Shĩ ne mai Tanƙwasa a kan bayinSa, kuma Shi ne Mai hikima, Masani."
6|19|Ka ce: "Wane abu ne mafi girma ga shaida?" Ka ce: "Allah ne shaida a tsakãnina da tsakaninku. Kuma an yiwo wahayin wannan Alƙur'ãni dõmin in yi muku gargaɗi da shi, da wanda lãbãri ya kai gare shi. Shin lalle ne ku, haƙĩƙa, kunã shaidar cẽwa, lalle ne tãre da Allah akwai wasu abũbuwan bautawa?" Ka ce: "Bã zan yi shaidar (haka) ba." Ka ce: "Abin sani, Shi ne Abin bautãwa Guda kumã lalle ne nĩ barrantacce ne daga abin da kuke yi na shirki."
6|20|Waɗanda Muka bã su Littãfi sunã sanin sa kamar yadda suke sanin ɗiyansu. Waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu, to, sũ bã su yin ĩmãni.
6|21|Wãne ne mafi zãlunci daga wanda yake ƙirƙira karya ga Allah, kõ kuwa ya ƙaryata game da ãyõyinsa? Lalle ne shĩ, azzalumai bã zã su ci nasara ba.
6|22|Kuma rãnar da Muka tãra su gabã ɗaya, sa'an nan Mu ce wa waɗanda suka yi shirki: "Inã abõkan tãrayyarku waɗanda kuka kasance kunã riyãwa?"
6|23|Sa'an nan kuma fitinarsu ba ta kasance ba, fãce dõmin sun ce: "Munã rantsuwa da Allah Ubangijinmu, ba mu kasance mãsu yin shirki ba."
6|24|Ka dũba yadda suka ƙaryata kansu! Kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙira ƙaryarsa, ya ɓace daga gare su.
6|25|Kuma daga cikinsu akwai wanda yake saurãre gare ka. Kuma Mun sanya abũbuwan rufi a kan zukãtansu dõmin kada su fahimcẽ shi kuma a cikin kunnuwansu (Mun sanya) wani nauyi. Kuma idan sun ga kõwace ãyã bã zã su yi ĩmãni da ita ba har idan sunjẽ maka sunã jãyayya da kai, waɗanda suka kãfirta sunã cẽwa: "Wannan bai zama ba fãce tãtsũniyõyin mutãnen farko."
6|26|Kuma sunã hanãwa daga gare shi, kuma sunã nĩsanta daga gare shi, kuma bã su halakarwa, fãce kansu, kuma bã su sansancẽwa.
6|27|Kuma dã kanã gani, a lõkacin da aka tsayar da su a kan wuta, sai suka ce: "Yã kaitõnmu! Dã ana mayar da mu, kuma bã zã mu ƙaryata ba daga ãyõyin Ubangijinmu, kuma zã mu kasance Daga mũminai."
6|28|Ã'aha, abin da suka kasance suna ɓõyẽwa, daga gabãni, ya bayyana a gare su. Kuma dã an mayar da su, lalle dã sun kõma ga abin da aka hana su daga barinsa. Kuma lalle ne sũ, haƙĩƙa, maƙaryata ne.
6|29|Kuma suka ce: "Ba ta zama ba, fãce rayuwarmu ta duniya, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba."
6|30|Kuma dã kana gani, a lõkacin da aka tsayar da su ga UbangiJinsu, Ya ce: "Ashe wannan bai zama gaskiya ba?" Suka ce: "Nã'am, muna rantsuwa da Ubangijinmu!" Ya ce: "To ku ɗanɗani azaba sabõda abin da kuka kasance kuna yi na kãfirci."
6|31|Lalle ne waɗanda suka ƙaryata game da gamuwa da Allah sun yi hasara, har idan Sa'a ta je musu kwatsam, sai su ce: "Yã nadãmarmu a kan abin da muka yi sakaci a cikinta!" Alhãli kuwa su suna ɗaukar kayansu masu nauyi a kan bayayyakinsu. To, abin da suke ɗauka yã mũnana.
6|32|Kuma rãyuwar dũniya ba ta zama ba, fãce wãsa da shagala, kuma lalle ne, Lãhira ce mafi alhẽri ga waɗanda suka yi taƙawa. Shin, ba za ku yi hankali ba?
6|33|Lalle ne Muna sani cewa haƙĩƙa, abin da suke faɗa yana ɓãta maka rai. To, lalle ne su, bã su ƙaryata ka (a cikin zukatansu) kuma amma azzãlumai da ãyõyin Allah suke musu.
6|34|Kuma lalle ne, haƙĩƙa, an ƙaryata manzanni daga gabãninka, sai suka yi haƙuri a kan abin da aka ƙaryata su, kuma aka cũtar da su, har taimakonMu ya je musu, kuma babu mai musanyãwa ga kalmõmin Allah. Kuma lalle ne (abin da yake natsar da kai) ya zo maka daga lãbãrin (annabãwan) farko.
6|35|Kuma idan yã kasance cewa finjirewarsu tã yi nauyi a gare ka, to, idan kana iyãwa, ka nemi wani ɓullõ a cikin ƙasa, kõ kuwa wani tsãni a cikin sama dõmin ka zo musu da wata ãyã, (sai ka yi). Kuma dã Allah Yã so haƙĩƙa dã Yãtãra su a kan shiriya. Sabõda haka, kada lalle ka kasance daga jãhilai.
6|36|Abin sani kawai, waɗanda suke saurare ne suke karɓãwa, kuma matattu Allah Yake tãyar da su, Sa'an nan kuma zuwa gare Shi ake mayar da su.
6|37|Kuma suka ce: "Don me ba a saukar da ãyã ba, a kansa, daga Ubangjinsa?" Ka ce: "Lalle ne Allah Mai ĩko ne a kan Yasaukar da ãyã, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba."
6|38|Kuma bãbu wata dabba a cikin ƙasa kuma bãbu wani tsuntsu wanda yake tashi da fukafukinsa fãce al'umma ne misãlanku. Ba Mu yi sakacin barin kõme ba a cikin Littãfi, sa'an nan kuma zuwa ga Ubangjinsu ake tãra su.
6|39|Kuma waɗanda suka ƙaryata gameda ãyõyinMu, kurãme ne kuma bebãye, acikin duffai. Wanda Allah Ya so Yanã ɓatar da shi, kuma wanda Ya so zai sanya shi a kan hanya madaidaiciya.
6|40|Ka ce: "Shĩn, kun gan ku, idan azãbar Allah ta zo muku, kõ Sã'ar Tashin Kiyãma ta zo muku, shin wanin Allah kuke kira, idan dai kun kasance mãsu gaskiya?"
6|41|"Ã'a, Shĩ dai kuke kira sai Ya kuranye abin da kuke kira zuwa gare Shi, idan Ya so, kuma kunã mantãwar abin da kuke yin shirkin tãre da shi."
6|42|Kuma lalle Mun aika zuwa ga al'ummai daga gabãninka, sai Muka kãmã su da tsanani da cũta, tsammãninsu zã su ƙanƙan da kai,
6|43|To, don me, a lõkacin da tsananinMu ya jẽ musu ba su yi tawãlu'i ba? Kuma amma zukatansu sun ƙẽƙashe kuma shaiɗan yã ƙawãta musu abin da suka kasance sunã aikatãwa.
6|44|Sa'an nan kuma alõkacin da suka manta da abin da aka tunãtar da su da shi, sai Muka bũɗe, a kansu, ƙõfõfin dukkan kõme, har a lõkacin da suka yi farin ciki da abin da aka ba su, Muka kãmã su, kwatsam, sai gã su sun yi tsuru tsuru.
6|45|Sai aka katse ƙarshen mutãnen, waɗanda suka yi zãlunci. Kuma gõdiya tã tabbata ga Allah Ubangijin tãlikai.
6|46|Ka ce: "Shin, kun gani, idan Allah Ya riƙe jinku, da gannanku, kuma Ya sanya hãtimi a kan zukãtanku, wane abin bauttãwa ne, wanin Allah, zai jẽ muku da shi?" Ka dũba yadda Muke sarrafaãyõyi, Sa'an nan kuma sũ, sunã finjirẽwa.
6|47|Ka ce: "Shin, kun gan ku, idan azãbar Allah ta jẽ muku, kwatsam, kõ kuwa bayyane, shin, anã halakãwa, fãce dai mutãne azzãlumai?"
6|48|Kuma bã Mu aikãwa da manzãnni fãce mãsu bayar da bushãra, kuma mãsu gargaɗi. To, wanda ya yi ĩmãni kuma yagyãra aiki, to, babu tsõro a kansu, kuma ba su yin baƙin ciki.
6|49|Kuma waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu, azãba tanã shãfar su sabõda abin da suka kasance sunã yi na fãsiƙanci.
6|50|Ka ce: "Ba zan ce muku, a wurina akwai taskõkin Allah ba. Kuma ba ni sanin gaibi, kuma ba ni gaya muku cẽwa ni malã'ika ne. Ba ni bi, fãce abin da ake yiwo wahayi zuwa gare ni." Ka ce: "Shin, makãho da mai gani sunã daidaita? Shin fa, ba ku yin tunãni?"
6|51|Kuma ka yi gargaɗi da shi ga waɗanda suke jin tsõron a tãra su zuwa ga Ubangijinsu, ba su da wani masõyi baicinSa, kuma babu mai cẽto, tsammãninsu, sunã yin taƙawa.
6|52|Kuma kada ka kõri waɗanda suke kiran Ubangijinsu sãfe da maraice, sunã nufin yardarSa, babu wani abu daga hisãbinsu a kanka, kuma babu wani abu daga hisãbinka a kansu, har ka kõre su ka kasance daga azzãlumai.
6|53|Kuma kamar wannan ne, Muka fitini sãshensu da sãshe, dõmin su ce: "Shin waɗannan ne Allah Ya yi falala a kansu daga tsakãninmu?" Shin, Allah bai zama Mafi sani ba ga mãsu gõdiya?
6|54|Kuma idan waɗanda suke yin ĩmãni da ãyõyinMu suka jẽ maka, sai ka ce: "Aminci ya tabbata a gareku; Ubangjinku Ya wajabta rahama ga kanSa, cẽwa lalle ne wanda ya aikata aibi da jãhilci daga cikinku, sa'an nan kuma ya tũba daga bãyansa, kuma ya gyãra, to, lalle Shi, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."
6|55|Kuma kamar wannan ne Muke bayyana ãyõyi, daki-daki, kuma dõmin hanyar mãsu laifi ta bayyana.
6|56|Ka ce: "Lalle ne ni, an hana ni in bauta wa waɗanda kuke kira daga baicin Allah." Ka cc: "Ba ni bin son zũciyõyinku, (dõmin in nã yi haka) lalle ne, nã ɓace. A sa'an nan, kuma ban zama daga shiryayyu ba."
6|57|Ka ce: "Lalle ne inã kan hujja daga Ubangjina, kuma kun ƙaryata (ni) game da Shi; abin da kuke nẽman gaugãwarsa, bã ya wurina, hukunci kuwa bai zama ba fãce, ga Allah, Yanã bãyar da lãbãrin gaskiya, kuma shĩ ne mafi alhẽrin mãsu rarrabẽwa."
6|58|Ka ce: "Lalle ne, dã a wurina akwai abin da kuke nẽman gaugãwa da shi, haƙĩƙa dã an hukunta al'amarin, a tsakãnina da tsakãninku, kuma Allah Shĩ ne Mafi sani ga azzũlumai."
6|59|Kuma a wurinSa mabũdan gaibi suke, babu wanda yake sanin su fãce Shi, kuma Yanã sanin abin da ke a cikin tudu da ruwa, kuma wani ganye ba ya fãɗuwa, fãce Yã san shi, kuma bãbu wata ƙwãya a cikin duffan ƙasã, kuma babu ɗanye, kuma babu ƙẽƙasasshe, fãce yanã a cikin wani Littãfi mai bayyanãwa.
6|60|Kuma Shĩ ne wanda Yake karɓar rãyukanku da dare, kuma Yanã sanin abin da kuka yãga da rãna, sa'an nan Yanã tãyar da ku a cikinsa, dõmin a hukunta ajali ambatacce sa'an nan kuma zuwa gare shi makõmarku take, sa'an nan kuma Ya ba ku lãbari da abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
6|61|Kuma Shĩ ne Mai rinjãya bisa ga bãyinSa, kuma Yanã aikan mãsu tsaro a kanku, har idan mutuwa ta jẽ wa ɗayanku, sai manzanninMu su karɓi ransa alhãli su ba su yin sakaci.
6|62|Sa'an nan kuma a mayar da su zuwa ga Allah Ubangjinsu na gaskiya. To! A gare shi hukunci yake, kuma Shi ne Mafi gaugãwar mãsu bincike.
6|63|Ka ce: "Wane ne Yake tsĩrar da ku daga duhũhuwan tududa ruwa, kunã kiran Sa bisa ga ƙanƙan da kai Kuma a ɓõye: 'Lalle ne idan Ka tsĩrar da mu daga wannan (masĩfa), haƙĩƙa, muna kasancẽwa daga mãsu gõdiya?'"
6|64|Ka ce: "Allah ne Yake tsĩrar da ku daga gare ta, kuma daga dukan baƙin ciki sa'an nan kuma ku, kunã yin shirki!"
6|65|Ka ce: "Shĩ ne Mai ĩko a kan Ya aika da wata azãba a kanku daga bisanku, kõ kuwa daga ƙarƙashin ƙafãfunku, kõ kuwa Ya gauraya ku ƙungiyõyi, kuma Ya ɗanɗanã wa sãshenku masĩfar sãshe." "Ka dũba yadda Muke sarrafa ãyõyi, tsammãninsu sunã fahimta!"
6|66|Kuma mutãnenka sun ƙaryata (ka) game da Shi, alhãli kuwa Shi ne gaskiya. Ka ce: "Nĩban zama wakĩli a kanku ba."
6|67|"Akwai matabbata ga dukan lãbãri, kuma zã ku sani."
6|68|Kuma idan kã ga waɗanda suke kũtsawa a cikin ãyõyinMu, to, ka bijire daga gare su, sai sun kũtsa a cikin wani lãbãri waninsa. Kuma imma dai shaiɗan lalle ya mantar da kai, to, kada ka zauna a bayan tunãwa tãre da mutãne azzãlumai.
6|69|Kuma babu wani abu daga hisãbinsu (mãsu kutsãwa a cikin ayõyin Allah (a kan mãsu taƙawa amma akwai tunãtarwa (a kansu), tsãmmãninsu (mãsu kutsawar) zã su yi taƙawa.
6|70|Kuma ka bar waɗanda suka riƙi addĩninsu abin wãsa da wargi alhãli rãyuwar dũniya tã rũɗe su, kuma ka tunãtar game da shi (Alƙur'ãni): Kada a jẽfa raia cikin halaka sabõda abin da ya tsirfanta; ba shi da wani majiɓinci baicin Allah, kuma babu wani mai cẽto; kuma, kõ ya daidaita dukan fansa, ba zã a karɓa ba daga gare shi. Waɗancan ne aka yanke wa tsammãni sabõda abin da suka tsirfanta; sunã da wani abin shã daga ruwan zãfi, da wata azãba mai raɗaɗi, sabõda abin da suka kasance sunã yi na kãfirci.
6|71|Ka ce: "Shin, zã mu yi kiran abin da bã ya amfãninmu, baicin Allah, kuma bã ya cũtar damu, kuma a mayar da mu a kan dugãduganmu, a bayan Allah Yã shiryar da mu kamar wanda shaiɗãnu suka kãyar da shi a cikin ƙasa, yanã mai ɗĩmuwa, yanã da abõkaisunã kiran sa zuwa ga shiriya, 'Ka zo mana'" Kace: "Lalle ne, shiriyar Allah ita ce shiriya. Kuma an umurce mu, mu sallama wa Ubangijin tãlikai."
6|72|"Kuma (an ce mana): Ku tsai da salla kuma ku bĩ shi (Allah) da taƙawa kuma Shi ne wanda Yake zuwa gare Shi ake tãra ku."
6|73|Kuma Shĩ ne wanda Ya halitta sammai da ƙasa da mulkinSa, kuma a Rãnar da Yake cẽwa: "Ka kasance," sai abu ya yi ta kasancẽwa. MaganarSa ce gaskiya, kuma gare Shi mulki yake a Rãnar da ake bũsa a cikin ƙaho. Masanin fake da bayyane ne, Kuma Shi ne Mai hikima Masani.
6|74|Kuma a lõkacin da Ibrãhĩma ya ce wa ubansa Ãzara: "Shin, kanã riƙon gumãka abũbuwan bautãwa? Lalle nĩ, inã ganin ka kai damutã- nenka, a cikin ɓata bayyananniya."
6|75|Kuma kamar wancan ne, Muke nũna wa Ibrãhĩma mulkin sammai da ƙasa, kuma dõmin ya kasance daga mãsu yaƙĩni.
6|76|To, a lõkacin da dare ya rufe a kansa, ya ga wani taurãro, ya ce: "Wannan ne, ubangijina?" Sa'an nan a lõkacin da ya faɗi, ya ce: "Ba ni son mãsu fãɗuwa."
6|77|Sa'an nan a lõkacin da ya ga watã yanã mai bayyana, ya ce: "Wannan ne Ubangijina?" Sa'an nan a lõkacin da ya fãɗi, ya ce: "Lalle ne idan Ubangijina bai shiryar da ni ba, haƙĩƙa, inã kasancẽwa daga mutãne ɓatattu."
6|78|Sa'an nan a lõkacin da ya ga rãnã tanã bayyana, ya ce: "Wannan shĩ ne Ubangijina, wannan ne mafi girma?" Sa'an nan a lõkacin da ta fãɗi, ya ce: "Ya mutãnena! Lalle ne ni barrantacce nake daga abin da kuke yi na shirki."
6|79|"Lalle ne nĩ, na fuskantar da fuskata ga wanda, Ya ƙãga halittar sammai da ƙasa, inã mai karkata zuwa ga gaskiya, kuma bã ni cikin mãsu shirki."
6|80|Kuma mutãnensa suka yi musu da shi. Ya ce: "Shin kunã musu da ni a cikin sha'anin Allah, alhãli kuwa Yã shiryai da ni? Kuma bã ni tsõron abin da kuke yin shirki da shi, fãce idan Ubangijina Yã so wani abu. Ubangijina Ya yalwaci dukkan kõme da ilmi. Shin, ba zã ku yi tunãni ba?"
6|81|"Kuma yãyã nake jin tsõron abin da kuka yi shirki da shi, kuma ba ku tsõron cẽwa lalle ne kũ, kun yi shirki da Allah, abin da (Allah) bai saukar da wata hujja ba game da shi? To, wane ɓangare daga sãshen biyu ne mafi cancanta da aminci, idan kun kasance kunã sani?"
6|82|"Waɗanda suka yi ĩmãni, kuma ba su gauraya ĩmãninsu da zãlunci ba, waɗannan sunã da aminci, kuma sũ ne shiryayyu."
6|83|Kuma waccan ita ce hujjarMu, Mun bayãr da ita ga Ibrãhĩma a kan mutãnensa. Munã ɗaukaka wanda Muka so da darajõji. Lalle ne Ubangijinka Mai hikima ne, Masani.
6|84|Kuma Muka bã shi Is'hãƙa da Yãƙubu, dukansu Mun shiryar, kuma Nũhu Mun shiryar da shi a gabãni, kuma daga zuriyarsa akwai Dãwũda da Sulaimãnu da Ayyũba, da Yũsufu da Mũsã da Hãrũna, kuma kamar wancan ne Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
6|85|Da Zakariyya da Yahaya da Isa da Ilyasu dukansu daga sãlihai suke.
6|86|Da Ismã'la da Ilyasa, a da Yũnusa da Luɗu, kuma dukansu Mun fĩfĩtã su a kan tãlikai.
6|87|Kuma daga ubanninsu, da zũriyarsu, da 'yan'uwansu, kuma Muka zãɓe su, kuma Muka shiryar da su zuwa ga hanya madaidaiciya.
6|88|Wancan ne shiryarwar Allah, Yanã shiryar da wanda Yake so daga bayinSa. Kuma dã sun yi shirki dã haƙĩƙa abin da suka kasance sunã, aikatãwa yã lãlãce.
6|89|Waɗancan ne waɗanda Muka bai wa Littãfi da hukunci da Annabci. To idan waɗannan (mutãne) sun kãfirta da ita, to, haƙĩƙa, Mun wakkala wasu mutãne gare ta, ba su zama game da ita kãfirai ba.
6|90|Waɗancan ne Allah Ya shiryar, sabõda haka ka yi kõyi da shiryarsu. Ka ce: "Ba ni tambayar ku wata ijãra. Shĩ (Alƙur'ãni) bai zama ba fãce tunãtarwa ga tãlikai."
6|91|Kuma ba su ƙaddara Allah a kan hakkin ƙaddara shi ba, a lõkacin da suka ce: "Allah bai saukar da kõme ba ga wani mutum." Ka ce: "Wãne ne ya saukar da Littãfi wanda Mũsã ya zo da shi, yanã haske da shiriya ga mutãne, kunã sanya shi takardu, kũna bayyana su, kuma kunã ɓõye mai yawa, kuma an sanar da ku abin da ba ku sani ba, ku da ubanninku?" Ka ce: "Allah," sa'an nan ka bar su a cikin sharhõliyarsu sunã wãsã.
6|92|Kuma wannan Littãfi ne, Mun saukar da shi, mai albarka ne, mai gaskata wanda yake a gabansa ne, kuma dõmin ka yi gargaɗi ga Uwar Alƙaryu (Makka) da wanda yake gefenta. Kuma waɗanda suke yin ĩmãni da Lãhira sunã ĩmãni da shi (Alƙur'ãni), kuma sũ, a kan sallarsu, sunã tsarẽwa.
6|93|Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kõ kuwa ya ce: "An yi wahayi zuwa gare ni," alhãli kuwa ba a yi wahayin kõme ba zuwa gare shi, da wanda ya ce: "zan saukar da misãlin abin da Allah Ya saukar?" Kuma dã kã gani, a lõkacin da azzãlumai suke cikin mãyen mutuwa, kuma malã'iku sunã mãsu shimfiɗa hannuwansu, (sunã ce musu) "Ku fitar da kanku; a yau anã sãka muku da azãbar wulãƙanci sabõda abin da kuka kasance kunã faɗa, wanin gaskiya, ga Allah kuma kun kasance daga ãyõyinSa kunã yin girman kai."
6|94|Kuma lalle ne haƙĩƙa, kun zo Mana ɗai ɗai, kamar yadda Muka halittã ku a farkon lõkaci. Kuma kun bar abin da Muka mallaka muku a bayan bayayyakinku, kuma ba Mu gani a tãre da kũ ba, macẽtanku waɗanda kuka riya cẽwa lalle ne sũ, a cikinku mãsu tãrayya ne. Lalle ne, hãƙĩƙa, kõme yã yanyanke a tsakãninku, kuma abin da kuka kasance kunã riyãwa ya ɓace daga gare ku.
6|95|Lalle ne, Allah ne Mai tsãgewar ƙwãyar hatsi da kwalfar gurtsu. Yanã fitar da mai rai daga mamaci, kuma (Shi) Mai fitar da mamaci ne daga mai rai, wannan ne Allah. To, yãya ake karkatar da ku?
6|96|Mai tsãgẽwar sãfiya, kuma Ya sanya dare mai natsuwa, kuma da rãna da watã a bisa lissãfi. vwannan ne ƙaddarãwar Mabuwãyi Masani.
6|97|Kuma Shi ne Ya sanya muku taurãri dõmin ku shiryu da su a cikin duffan tudu da ruwa. Lalle ne Mun bayyana ãyõyi daki-daki, ga mutãne waɗanda suke sani.
6|98|Kuma Shi ne Ya ƙãga halittarku daga rai guda, sa'an nan da mai tabbata da wanda ake ajẽwa. Lalle ne Mun bayyanã ãyõyi daki-daki, ga mutãne waɗanda suke fahimta.
6|99|Kuma Shi ne Ya saukar da ruwa daga sama, Muka fitar da tsiron dukkan kõme game dã shi, sa'an nan Muka fitar da kõre daga gare shi, Muna fitar da kwãya ɗamfararriya daga gare shi (kõren), kuma daga dabĩno daga hirtsinta akwai dumbuje-dumbuje makusanta, kuma (Muka fitar) da gõnaki na inabõbi da zãitũni da rummãni, mãsu kamã da jũna da wasun mãsu kama da jũna. Ku dũba zuwa 'ya'yan itãcensa, idan ya yi 'ya'yan, da nunarsa. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyõyi ga waɗanda suke yin ĩmãni.
6|100|Kuma suka sanya wa Allah abõkan tãrayya, aljannu, alhãli kuwa (Shi) Ya halitta su. Kuma sun ƙirƙira masa ɗiya da 'yã'ya, bã da ilmi ba. TsarkinSa yã tabbata! Kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke sifantãwa.
6|101|Mafarin halittar sammai da ƙasa. Yãya ɗã zai zama a gare Shi alhãli kuwa mãta ba ta kasance ba, a gare Shi, kuma Ya halitta dukkan, kõme, kuma Shĩ, game da dukan kõme, Masani ne?
6|102|Wancan ne Allah Ubangijinku. Bãbu wani abin bautãwa fãce Shĩ, Mahaliccin dukan kõme. Sabõda haka ku bauta Masa kuma Shi ne wakĩli a kan dukan, kõme.
6|103|Gannai bã su iya riskuwarSa, kuma Shĩ Yanã riskuwar gannai, kuma Shĩ ne Mai tausasãwa, Masani.
6|104|Lalle ne abũbuwan lũra sun je muku daga Ubangijinku, to, wanda ya kula, to, dõmin kansa, kuma wanda ya makanta, to, laifi yanã a kansa, kuma nĩ, a kanku, bã mai tsaro ba ne.
6|105|Kamar wannan ne Muke sarrafa ãyõyi, kuma dõmin su ce: "Kã karanta!" Kuma dõmin Mu bayyana shi ga mutãne waɗanda sunã sani.
6|106|Ka bi abin da aka yi wahayi zuwa gare ka daga Ubangijinka; babu wani abin bautãwa fãce Shi, kuma ka bijire daga mãsu shirki.
6|107|Kuma dã Allah Yã so, dã ba su yi shirki ba, kuma ba Mu, sanya ka mai tsaro a kansu ba, kuma ba kai ne wakĩli a kansu ba.
6|108|Kuma kada ku zãgi waɗanda suke kira, baicin Allah, har su zãgi Allah bisa zãlunci, ba, da ilmi ba. Kamar wannan ne Muka ƙawãta ga kõwace al'umma aikinsu, sa'an nan zuwa ga Ubangijinsu makõmarsu take, sa'an nan Ya ba su lãbari da abin da suka kasance sunã aikatãwa.
6|109|Kuma suka yi rantsuwa da Allah iyakar rantsuwõyinsu (cẽwa) lalle ne idan wata ãyã ta jẽmusu, haƙĩƙa, sunã yin ĩmãni da ita. Ka ce: "Abin sani kawai, ãyõyi a wurin Allah suke. Kuma mẽne nezai sanya ku ku sansance cẽwa, lalle ne su, idan ãyõyin sun je, ba zã su yi ĩmãni ba?"
6|110|Kuma Munã jujjũya zukãtansu da ganansu, kamar yadda ba su yi ĩmãni da shi ba a farkon lõkaci kuma Munã barin su a cikin kũtsãwarsu, sunã ɗĩmuwa.
6|111|Kuma dã a ce, lalle Mũ Mun saukar da Malã'iku zuwa gare su, kuma matattu suka yi musu magana, kuma Muka tãra dukkan kõme a kansu, gungu-gungu, ba su kasance sunã iya yin ĩmãni ba, sai fa idan Allah Yã so, Kuma amma mafi yawansu sunã jãhiltar haka.
6|112|Kuma kamar wancan ne Muka sanya wa kõwane Annabi maƙiyi; shaiɗãnun mutãne da aljannu, sãshensu yanã yin ishãra zuwa sãshe da ƙawãtaccen zance bisa ga rũɗi. Kuma dã Ubangijinka Yã so, dã ba su aikatã shi ba, don haka ka bar su da abin da, suke ƙirƙirãwa.
6|113|Kuma dõmin zukãtan waɗanda ba su yi ĩmãni da Lãhira ba su karkata saurãrẽ zuwa gareshi, kuma dõmin su yarda da shi, kuma dõmin su kamfaci abin da suke mãsu kamfata.
6|114|Shin fa, wanin Allah nake nẽma ya zama mai hukunci, alhãli kuwa Shĩ ne wanda Ya saukar muku da Littãfi abin rabẽwadaki-daki? Kuma waɗanda Muka bai wa Littãfi sunã sanin cẽwa lalleshi (Alƙur'ãni) abin saukarwa ne daga Ubangijinka, da gaskiya? Sabõda haka kada ku kasance daga mãsu shakka.
6|115|Kuma kalmar Ubangijinka tã cika, tanã gaskiya da ãdalci. Babu mai musanyãwa ga kalmõminSa, kuma Shi ne Maiji, Masani.
6|116|Kuma idan ka bi mafiya yawan waɗanda suke a cikin ƙasa da ɗã'a sunã ɓatar da kai daga hanyar Allah. Ba su bin kõme sai fãce ƙaddari-faɗi suke yi.
6|117|Lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Mafi sani ga wanda yake ɓacẽwa daga hanyarsa kuma Shi ne mafi sani ga masu shiryuwa.
6|118|Sabõda haka ku ci daga abin da aka ambaci sũnan Allah kansa, idan kun kasance mãsu ĩmãni da ãyõyinSa.
6|119|Kuma mẽne ne ya sãme ku, bã zã ku ci ba daga abin da aka ambaci sũnan Allah a kansa, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Ya rarrabe, muku daki-daki, abin da Ya haramta a kanku, fãce fa abin da aka bukãtar da ku bisa lalũra zuwa gare shi? Kuma lalle ne mãsu yawa sunã ɓatarwa, da son zũciyõyinsu, ba da wani ilmi ba. Lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Mafi sani ga mãsu ta'addi.
6|120|Kuma ku bar bayyanannen zunubi da ɓõyayyensa. Lalle ne waɗanda suke tsiwurwurin zunubi za a sãka musu da abin da suka kasance sunã kamfata.
6|121|Kada ku ci daga abin da ba a ambaci sũnan Allah ba a kansa. Kuma lalle ne shĩ fãsiƙanci ne. Kuma lalle ne, shaiɗãnu, haƙĩƙa, suna yin ishãra zuwa ga masõyansu, dõmin su yi jãyayya da ku. Kuma idan kuka yi musu ɗã'a, lalle ne kũ, haƙĩƙa, mãsu shirki ne.
6|122|Shin, kuma wanda ya kasance matacce sa'an nan Muka rãyar da shi, kuma Muka sanya wani haske dõminsa, yanã tafiya da shi, yanã zama kamar wanda misãlinsa yanã cikin duffai, shĩ kuma ba mai fita ba daga gare su? Kamar wancan ne aka ƙawãta wa kãfirai abin da suka kasance sunã aikatãwa.
6|123|Kuma kamar wancan ne Mun sanya a cikin kõwace alƙarya, shugabanni sũ ne mãsu laifinta dõmin su yi mãkirci a cikinta, alhãli kuwa ba su yin makirci fãce ga rayukansu, kuma ba su sansancẽwa.
6|124|Kuma idan wata ãyã ta je musu sai su ce: "Ba zã mu yi ĩmãni ba, sai an kãwo mana kamar abin da aka kãwo wa manzannin Allah." Allah Mafi sanin inda Yake sanya manzancinSa. Wani wulaƙanci a wurin Allah da wata azãba mai tsanani zã su sãmi waɗanda suka yi laifi, sabõda abin da suka kasance sunã yi na mãkirci.
6|125|Dõmin haka wanda Allah Ya yi nufin ya shiryar da shi sai ya bũɗa ƙirjinsa dõmĩn Musulunci, kuma wanda Ya yi nufin Ya ɓatar da shi, sai Ya sanya ƙirjinsa mai ƙunci matsattse, kamar dai yanã tãkãwa ne a ckin sama. Kamar wannan ne Allah Yake sanyãwar ƙazanta a kan waɗanda bã su yin ĩmãni.
6|126|Wannan ita ce hanya ta Ubangijinka madaidaiciya. Lalle ne Mun bayyana ãyõyi daki-daki ga mutãne mãsu karɓar tunãtarwa.
6|127|Sunã da gidan aminci a wurin Ubangjinsu, kuma Shĩ ne Majiɓincinsu, sabõda abin da suka kasance sunã aikatãwa.
6|128|Kuma rãnar da yake tãra su gaba ɗaya (Yanã cẽwa): "Yã jama'ar aljannu! Lalle ne kun yawaita kanku daga mutãne." Kuma majiɓantansu daga mutãne suka ce: "Yã Ubangjinmu! Sãshenmu ya ji dãɗi da sãshe, kuma mun kai ga ajalinmu wanda Ka yanka mana!" (Allah) Ya ce: "Wuta ce mazaunarku, kunã madawwama acikinta, sai abin da Allah Ya so. Lalle ne Ubangijinka Mai hikima ne, Masani."
6|129|Kuma kamar wancan ne Muke jiɓintar da sãshen azzãlumai ga sãshe, sabõda abin da suka kasance sunã tãrãwa.
6|130|Yã jama'ar aljannu da mutãne! Shin, manzanni daga gare ku ba su jẽ muku ba sunã lãbarta ãyõyiNa a kanku, kuma sunã yi muku gargaɗin haɗuwa da wannan yini nãku? Suka ce: "Mun yi shaida a kan kãwunanmu." Kuma rãyuwar dũniya tã rũɗẽ su. Kuma suka yi shaida a kan kãwunansu cẽwa lalle ne sũ, sun kasance kãfirai.
6|131|Wanan kuwa sabõda Ubangijinka bai kasance Mai halaka alƙaryõyi sabõda wani zãlunci ba ne, alhãli kuwa mutãnensu sunã jãhilai.
6|132|Kuma ga kõwanne, akwai darajõji daga abin da suka aikata. Kuma Ubangijinka bai zama mai shagala ba daga abin da suke aikatãwa.
6|133|Kuma Ubangijinika Wadãtacce ne Ma'abũcin rahama. Idan Yã so zai tafi da ku, kuma Ya musanya daga bãyanku, abin da Yake so, kamar yadda Ya ƙãga halittarku daga zũriyar wasu mutãne na dabam.
6|134|Lalle ne abin da ake yi muku wa'adi lalle mai zuwa ne kuma ba ku zama mãsu buwãya ba,
6|135|Ka ce: "Yã ku mutãnena! Ku yi aiki a kan halinku, lalle ne nĩ mai aiki ne, sa'an nan da sannu zã ku san wanda ãƙibar gida zã ta kasance a gare shi. Lalle ne shi, azzãlumai bã zã su ci nasarã ba."
6|136|Kuma sun sanya wani rabõ ga Allah daga abin da Ya halitta daga shũka da dabbõbi, sai suka ce: "Wannan na Allah ne," da riyãwarsu "Kuma wannan na abũbuwan shirkinmu ne." Sa'an nan
6|137|Kuma kamar wancan ne abũbuwan shirkinsu suka ƙãwata wa mãsu yawa, daga mãsu shirkin; kashewar 'ya'yansu, dõmin su halaka su kuma dõmin su rikitar da addininsu a gare su, Kuma dã Allah Yã so dã ba su aikatã shi ba. Sabõda haka ka bar su da abin da suke ƙirƙirãwa.
6|138|Kuma sukace: "Waɗannan dabbõbi da shũka hanannu ne; bãbu mai ɗanɗanar su fãce wanda muke so," ga riyãwarsu. Da wasu dabbõbi an hana bãyayyakinsu, da wasu dabbõbi bã su ambatar sũnan Allah a kansu, bisa ƙirƙiren ƙarya gare Shi. Zai sãka musu da abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa.
6|139|Kuma suka ce: "Abin da yake a cikin cikkunan waɗannan dabbõbi kẽɓantacce ne ga mazanmu, kuma hananne ne a kan mãtan aurenmu. Kuma idan ya kasance mũshe, to, a cikinsa sũ abõkan tãrayya ne, zai sãka musu sifantãwarsu. Lalle ne Shĩ, Mai hikima ne, Masani."
6|140|Lalle ne waɗanda suka kashe ɗiyansu sabõda wauta, ba da ilmi ba, sun yi hasãra! Kuma suka haramta abin da Allah Ya azurta su, bisa ƙirƙira ƙarya ga Allah. Lalle ne sun ɓace, kuma ba su kasance mãsu shiryuwa ba.
6|141|Kuma Shĩ ne Wanda Ya ƙãga halittar gõnaki mãsu rumfuna da wasun mãsu rumfuna da dabĩnai da shũka, mai sãɓãwa ga 'yã'yansa na ci, da zaituni da rummãni mai kama da jũna da wanin mai kama da jũna. Ku ci daga 'ya'yan itãcensa, idan ya yi 'yã'yan, kuma ku bãyar da hakkinSa a rãnar girbinsa, kuma kada ku yi ɓarna. Lalle ne Shĩ, ba Ya son mafarauta.
6|142|Kuma daga dabbõbi (Ya ƙãga halittar) mai ɗaukar kãya da ƙanãna; Ku ci daga abin da Allah Ya azurta ku, kuma kada ku bi zambiyõyin shaiɗan: LalLe ne shi, a gare ku, maƙiyi ne bayyananne.
6|143|Nau'õ'i takwas daga tumãkai biyu, kuma daga awãkai biyu; ka ce: Shin mazan biyu ne Ya haramta ko mãtan biyu, ko abin da mahaifar mãtan biyu suka tattara a kansa? Ku bã ni lãbãri da ilmi, idan kun kasance mãsu gaskiya.
6|144|Kuma daga rãƙuma akwai nau'i biyu, kuma daga shãnu biyu; ka ce: Shin, mazan biyu ne Ya hana ko mãtan biyu Ya hana, kõ abin da mahaifar mãtan biyu suka tattara a kansa? Kõ kun kasance halarce ne a lõkacin da Allah Ya yi muku wasiyya da wannan? To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, dõmin ya ɓatar da mutãne bã da wani ilmi ba? Lalle ne, Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai.
6|145|Ka ce: "Bã ni sãmu, a cikin abin da aka yõ wahayi zuwa gare Ni, abin haramtãwa a kan wani mai ci wanda yake cin sa fãce idan ya kasance mũshe kõ kuwa jini abin zubarwa kõ kuwa nãman alade, to lalle ne shi ƙazanta ne, kõ kuwa fãsiƙanci wanda aka kurũrũta, dõmin wanin Allah da shi." Sa'an nan wanda larũra ta kãmã shi, bã mai fita jama'a ba, kuma bã mai ta'addi ba, to, lalle Ubangijinka Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
6|146|Kuma a kan waɗanda suka tũba (Yahũdu) Mun haramta dukan mai akaifa, kuma daga shãnu da bisãshe Mun haramta musu kitsattsansu fãce abin da bãyukansu suka ɗauka, kõ kuwa kãyan ciki, kõ kuwa abin da ya garwaya da ƙashĩ wannan ne Muka sãka musu sabõda zãluncinsu, kuma Mu, haƙĩƙa, Mãsu gaskiya ne.
6|147|To, idan sun ƙaryatã ka, sai ka ce: "Ubangijinku Ma'abũcin rahama ne Mai yalwa; kuma bã a mayar da azãbarSa daga mutãne mãsu laifi."
6|148|Waɗanda suka yi shirki zã su ce: "Dã Allah Yã so dã ba mu yi shirki ba, kuma dã ubanninmu ba su yi ba, kuma dã ba mu haramta wani abu ba." Kamar wannan ne mutãnen da suke a gabãninsu suka ƙaryata, har suka ɗanɗani azãbarMu. Ka ce: "Shin, kunã da wani ilmi a wurinku dõmin ku fito mana da shi? Bã ku bin kõme fãce zato kuma ba ku zama ba fãce ƙiri-faɗi kawai kuke yi."
6|149|Ka ce: "To Allah ne da hujja isasshiya, sabõda haka: Dã Yã so, dã Yã shiryar da ku gabã ɗaya."
6|150|Ka ce: "Ku kãwo shaidunku, waɗanda suke bãyar da shaidar cẽwa Allah ne Ya haramta wannan." To idan sun kãwo shaida kada ka yi shaida tãre da su. Kuma kada ka bi son zũciyõyin waɗanda suka ƙaryata, game da ãyõyinMu, da waɗanda bã su yin ĩmãni da Lãhira, alhãli kuwa sũ daga Ubangijinsu suna karkacẽwa.
6|151|Ka ce: "Ku zo, in karanta abin da Ubangijinku Ya haramta." wãjibi ne a kanku kada ku yi shirkin kõme da Shi, kuma ga mahaifa biyu (ku kyautata) kyautatãwa, kuma kada ku kashe ɗiyanku sabõda talauci, Mũ ne Muke azurta ku, kũ da su, kuma kada ku kusanci abũbuwa alfãsha, abin da ya bayyana daga gare ta da abin da ya ɓõyu, kada ku kashe rai wanda Allah Ya haramta, fãce da hakki. Wannan ne (Allah) Ya yi muku wasiyya da Shi: Tsammãninku, kunã hankalta.
6|152|Kada ku kusanci dũkiyar marãya fãce da wadda take ita ce mafi kyau, har ya kai ga ƙarfinsa. Kuma ku cika mũdu da sikẽli da ãdalci, bã Mu kallafã wa rai fãce iyãwarsa. Kuma idan kun faɗi magana, to, ku yi ãdalci, kuma ko dã yã kasance ma'abũcin zumunta ne. Kuma da alkawarin Allah ku cika. wannan ne Ya yi muku wasiyya da shi: Tsammãninku, kunã tunãwa.
6|153|Kuma lalle wannan ne tafarkĩNa, yana madaidaici: Sai ku bĩ shi, kuma kada ku bi wasu hanyõyi, su rarrabu da ku daga barin hanyãTa. Wannan ne Allah Ya yi muku wasiyya da shi tsammãninku, kunã yin taƙawa.
6|154|Sa'an nan kuma Mun bai wa Mũsã Littãfi, yanã cikakke bisa ga wanda ya kyautata (hukuncin Allah) da rarrabẽwa, daki-daki, ga kõwane abu, da shiriya da rahama, tsammãninsu, sunã yin ĩmãni da haɗuwa da Ubangijinsu.
6|155|Kuma wannan Littãfi ne, Mun saukar da shi, mai albarka ne, sai ku bĩ shi kuma ku yi taƙawa, tsammãninku, anã jin ƙanku.
6|156|(Dõmin) kada ku ce: "Abin sani kawai, an saukar da littãfi a kan ƙungiya biyu daga gabãninmu, kuma lalle ne mũ, mun kasance, daga karatunsu, haƙĩƙa, gãfilai."
6|157|Kõ kuwa ku ce: "Dã dai lalle mũ an saukar da Littãfi a kanmu, haƙĩƙa, dã mun kasance mafiya, shiryuwa daga gare su." To, lalle ne wata hujja bayyananniya, daga Ubangijinku, tã zo muku, da shiriya da rahama. To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙaryata game da ãyõyin Allah, kuma ya finjire daga barinsu? Zã Mu sãka wa waɗanda suke finjirẽwa daga barin ãyõyinMu da mugunyar azãba, sabõda abin da suka kasance sunã yi na hinjirẽwa.
6|158|Shin, sunã jiran (wani abu), fãce dai malã'iku su je musu kõ kuwa Ubangijinka Ya je, kõ kuwa sãshen ãyõyin Ubangijinka ya je. A rãnar da sãshen ãyõyin Ubangijinka yake zuwa, ĩmãnin rai wanda bai kasance yã yi ĩmãnin ba a gabãni, kõ kuwa ya yi tsiwirwirin wani alhẽri, bã ya amfãninsa. Ka ce: "Ku yi jira: Lalle ne mũ, mãsu jira ne."
6|159|Lalle ne waɗanda suka rarraba addininsu, kuma suka kasance ƙungiyã-ƙungiyã, kai ba ka zama daga gare su ba, a cikin kõme: abin sani kawai al'amarinsu zuwa ga Allah yake. Sa'an nan Ya bã su lãbãri game da abin da suka kasance sunã aikatãwa.
6|160|Wanda ya zo da kyakkyãwan aiki guda, to, yanã da gõma ɗin misãlansa. Kuma wanda ya zo da mũgun aiki gũda, to, bã zã a sãka masa ba fãce da misãlinsa. Kuma sũ bã a zãluntar su.
6|161|Ka ce: "Lalle nĩ, Ubangijina Yã shiryar da ni zuwa ga tafarki madaidaici, addĩni, ƙĩmantãwa (ga abũbuwa), mai aƙĩdar Ibrãhĩm, mai karkata zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba."
6|162|Ka ce: "Lalle ne sallãta, da baikõna, da rãyuwãta, da mutuwãta, na Allah ne Ubangijin tãlikai."
6|163|"Bãbu abõkin tãrayya a gare Shi. Kuma da wancan aka umurce ni, kuma ni ne farkon mãsu sallamãwa."
6|164|Ka ce: "Shin wanin Allah nake nẽma ya zama Ubangiji, alhãli kuwa Shĩ ne Ubangijin dukan kõme? Kuma wani rai bã ya yin tsirfa fãce dõmin kansa, kuma mai ɗaukar nauyi, bã ya ɗaukar nauyin wani, sa'an nan kuma kõmawarku zuwa ga Ubangijinku take; Sa'an nan Yã bã ku lãbãri ga abin da kuka kasance, a cikinsa, kunã sãɓã wa jũnã?"
6|165|"Kuma Shĩ ne wanda Ya sanya ku mãsu maye wa jũnaga ƙasa. Kuma Ya ɗaukaka sãshenku bisa ga sãshe da darajõji; dõmin Ya jarraba ku a cikin abin da Ya bã ku." Lalle ne, Ubangijinka Mai gaggãwar uƙkũba ne, kuma lalle ne Shi, haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
7|1|A. L̃. M̃. Ṣ̃.
7|2|Littãfi ne aka saukar zuwa gare ka, kada wani ƙunci ya kasance a cikin ƙirjinka daga gare shi, dõmin ka yi gargaɗi da shi. Kuma tunãtarwa ne ga mũminai.
7|3|Ku bi abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku, kuma kada ku dinga bin wasu majiɓinta baicinSa. Kaɗan ƙwarai kuke tunãwa.
7|4|Kuma da yawa wata alƙarya Muka halaka ta, sai azãbarMu ta jẽ mata da dare kõ kuwa sunã mãsu ƙailũla.
7|5|Sa'an nan bãbu abin da yake da'awarsu, a lõkacin da azãbarMu ta jẽ musu, fãce suka ce: "Lalle ne mũ muka kasance mãsu zãlunci,"
7|6|Sa'an nan lalle ne Munã tambayar waɗanda aka aika zuwa gare su, kuma lalle Munã tambayar Manzannin.
7|7|Sa'an nan haƙĩƙa Munã bã su lãbãri da ilmi kuma ba Mu kasance mãsu fakowa ba.
7|8|Kuma awo a rãnar nan ne gaskiya. To, wanda sikẽlansasuka yi nauyi, to, waɗannan sũ ne mãsu cin nasara.
7|9|Kuma wanda sikẽlansa suka yi sauƙi, to, waɗannan ne waɗanda suka yi hasarar rayukansu, sabõda abin da suka kasance, da ãyõyinMu, sunã yi na zãlunci.
7|10|Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun sarautar da ku, a cikin ƙasa, kuma Mun sanya muku abũbuwan rãyuwa, a cikinta; kaɗan ƙwarai kuke gõdẽwa.
7|11|Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halittã ku sa'an nan kuma Mun sũrantã ku, sa'an nan kumaMun ce wa malã'iku: "Ku yi sujada ga Ãdam." Sai suka yi sujada fãce Iblĩs, bai kasance daga mãsuyin sujadar ba.
7|12|Ya ce: "Mẽne ne ya hana ka, ba ka yi sujada ba, alõkacin da Na umurce ka?" Ya ce: "Nĩ ne mafĩfĩci daga gare shi, Ka halitta ni daga wuta alhãli kuwa Kã halitta shi daga lãka."
7|13|Ya ce: "To, ka sauka daga gare ta; dõmin bã, ya kasancẽwa a gare ka ga ka yi girman kai a cikinta. Sai ka fita. Lalle ne kanã daga mãsu ƙasƙanci."
7|14|Ya ce: "Ka yi mini jinkiri zuwa ga rãnar da ake tãyar da su."
7|15|Ya ce: "Lalle ne, kanã daga waɗanda aka yi wa jinkiri."
7|16|Ya ce: "To inã rantsuwa da halakarwar da Ka yi mini, lalle ne, inã zaune musu tafarkinKa madaidaici."
7|17|"Sa'an nan kuma haƙĩƙa, Inã je musu daga gaba gare su, kuma daga bãya gare su, kuma daga jihõhin damansu da jihõhin hagunsu; Kuma bã zã ka sãmi mafi yawansu mãsu gõdiya ba."
7|18|Ya ce: "Ka fita daga gare ta kanã abin zargi kõrarre. Lalle ne wanda ya bĩ ka daga gare su, haƙĩƙa, zã Ni cika jahannama daga gare ku, gabã ɗaya."
7|19|"Kuma ya Ãdam! Ka zauna kai da matarka a Aljanna sai ku ci daga inda kuka so; kuma kada ku kusanci wannan itãciya, har ku kasance daga azzãlumai."
7|20|Sai Shaiɗan ya sanya musu waswãsi dõmin ya bayyana musu abin da aka rufe daga barinsu, daga al'aurarsu, kuma ya ce: "Ubangijinku bai hanã ku daga wannan itãciya ba fãce dõmin kada ku kasance malã'iku biyu ko kuwa ku kasance daga madawwama."
7|21|Kuma ya yi musu rantsuwa; Lalle ne nĩ, a gare ku, haƙĩƙa, daga mãsu nasĩha ne.
7|22|Sai ya saukar da su da rũɗi. Sa'an nan a lõkacin da suka ɗanɗani itãciyar, al'aurarsu ta bayyana gare su, kuma suka shiga sunã lĩƙawar ganye a kansu daga ganyen Aljanna. Kuma Ubangjinsu Ya kira su: "Shin, Ban hanã ku ba daga waccan itãciya, kuma Na ce muku lalle ne Shaiɗan, a gare ku, maƙiyi ne bayyananne?"
7|23|Suka ce: "Ya Ubangijinmu! Mun zãlunci kanmu. Kuma idan ba Ka gãfarta mana ba, kuma Ka yi mana rahama, haƙĩƙa, Munã kasancẽwa daga mãsu hasãra."
7|24|Ya ce: "Ku sauka, sãshenku zuwa ga sãshe yanã maƙiyi, kuma kunã da matabbata a cikin ƙasa, da ɗan jin dãɗi zuwa ga wani lõkabi."
7|25|Ya ce: "A cikinta kuke rãyuwa, kuma a cikinta kuke mutuwa, kuma daga gare ta ake fitar da ku."
7|26|Yã ɗiyan Ãdam! Lalle ne Mun saukar da wata tufa a kanku, tanã rufe muku al'aurarku, kuma da ƙawã. Kuma tufar taƙawa wancan ce mafi alhẽri. Wancan daga ãyõyin Allah ne, tsammãninsu sunã tunãwa!
7|27|Yã ɗiyan Ãdam! Kada Shaiɗan, lalle, ya fitine ku, kamar yadda ya fitar da iyãyenku, biyu daga Aljanna, yanã fizge tufarsu daga gare su, dõmin ya nũna musu al'aurarsu. Lalle ne shĩ, yanã ganin ku, shi da rundunarsa, daga inda bã ku ganin su. Lalle ne Mũ, Mun sanyaShaiɗan majiɓinci ga waɗanda bã su yin ĩmãni.
7|28|Kuma idan suka aikata alfãsha su ce: "Mun sãmi ubanninmu akanta." Kuma Allah ne Ya umurce mu da ita."Ka ce: "Lalle ne, Allah bã Ya umurni da alfãsha. Shin kunã faɗar abin da bã ku da saninsa ga Allah?"
7|29|Ka ce: "Ubangjina Yã yi umurni da ãdalci; kuma ku tsayar da fuskõkinku a wurin kõwane masallãci, kuma ku rõƙẽ Shi, kunã mãsu tsarkake addini gare Shi. Kamar yadda Ya fãra halittarku kuke kõmãwa."
7|30|Wata ƙungiya (Allah) Yã shiryar, kuma wata ƙungiya ɓata tã wajaba a kansu; lalle ne sũ, sun riƙi shaiɗanu majiɓinta, baicin Allah, kuma sunã zaton, lalle sũ, mãsu shiryuwa ne.
7|31|Yã ɗiyan Ãdam! Ku riƙi ƙawarku a wurin kõwane masallãci kuma ku ci, kuma ku sha; Kuma kada ku yi ɓarna. Lalle ne Shĩ (Allah), bã Ya son mãsu ɓarna.
7|32|Ka ce: "Wãne ne ya haramta ƙawar Allah, wadda Ya fitar sabõda bãyinSa, da mãsu dãɗi daga abinci?" Ka ce: "Sũ, dõmin waɗanda suka yi ĩmani suke a cikin rãyuwar dũniya, suna keɓantattu a Rãnar Kiyãma. "Kamar wannan ne Muke bayyana ãyõyi, daki-daki, ga mutãnen da suke sani.
7|33|Ka ce: "Abin sani kawai, Ubangijina Yã hana abũbuwanalfãsha; abin da ya bayyana daga gare su da abin da ya ɓõyu, da zunubi da rarraba jama'a, bã da wani hakki ba, kuma da ku yi shirki da Allah ga abin da bai saukar da wani dalĩli ba gare shi, kuma da ku faɗi abin da ba ku sani ba, ga Allah."
7|34|Kuma ga kõwace al'umma akwai ajali. Sa'an nan idan ajalinsu ya je, bã zã a yi musu jinkiri ba, sa'a guda, kuma bã zã su gabãce shi ba.
7|35|Yã ɗiyan Ãdam! Ko dai wasu manzanni, daga cikinku, su jẽ muku, sunã gaya muku ayõyiNato, wanda ya yi taƙawa, kuma ya gyara aikinsa, to, bãbu tsoro a kansu, kuma bã su yin baƙin ciki.
7|36|Kuma waɗanda suka ƙaryatã game da ãyõyinMu, kuma suka yi girman kai daga gare su, waɗannan sũ ne abõkan wuta, sũ, a cikinta madawwama ne.
7|37|To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kõ kuwa ya ƙaryata game da ãyõyinSa? Waɗannan rabonsu daga Littãfi yanã sãmunsu, har a lõkacin da ManzanninMu suka je musu, sunã karɓar rãyukansu, su ce: "Ĩnã abin da kuka kasance kunã kira, baicin Allah?" Su ce: "Sun ɓace daga gare mu, "Kuma su yi shaida a kansu cẽwa lalle sũ, sun kasance kãfirai."
7|38|Ya ce: "Ku shiga a cikin al'ummai waɗanda, haƙĩƙa, sun shige daga gabãninku, daga aljannu da mutãne, a cikin Wuta. A kõ da yaushe wata al'umma ta shiga sai ta la'ani 'yar'uwarta, har idan suka riski jũna, a cikinta, gabã ɗaya, ta ƙarshensu ta ce wa ta farkonsu: "Ya Ubangijinmu! Waɗannan ne suka ɓatar da mu, sai Ka kãwo musu azãba ninki daga wuta." Ya ce: "Ga kõwane akwai ninki; kuma amma ba ku sani ba."
7|39|Kuma ta farkonsu ta ce wa ta ƙarshe: "To, bã ku da wata falala a kanmu, sai ku ɗanɗana azãba sabõda abin da kuka kasance kunã tãrãwa!"
7|40|Lalle ne waɗanda suka ƙaryatã game da ãyõyinMu, kuma suka yi girman kai daga barinsu, bã zã a bubbuɗe musu kõfõfin sama ba, kuma bã su shiga Aljanna sai raƙumi ya shiga kafar allũra, kuma kamar wannan ne Muke sãka wa mãsu laifi.
7|41|Sunã da wata shimfiɗa daga Jahannama kuma daga samansu akwai wasu murafai. Kuma kamar wancan ne Muke sãka wa azzãlumai.
7|42|Kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, bã Mu ƙallafa wa rai fãce iyãwarsa, Waɗannan ne abõkan Aljanna, sũ, a cikinta, madawwma ne.
7|43|Kuma Muka fitar da abin da yake a cikin ƙirãzansu, daga ƙiyayya, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, kuma suka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah, wanda Ya shiryar da mu ga wannan. Kuma ba mu kasance munã iya shiryuwa ba, bã dõmin Allah Ya shiryar da mu ba. Lalle ne haƙĩƙa, Manzannin Ubangjinmu, sun jẽ mana da gaskiya." Kuma aka kira su, cẽwa: "Waccan Aljlnna an gãdar da ku ita, sabõda abin da kuka kasance kunã aikatãwa."
7|44|Kuma 'yan Aljanna suka kirãyi 'yan Wuta suka ce: "Lalle ne mun sãmi abin da Ubangijinmu Ya yi mana wa'adi, gaskiya ne. To, shin, kun sãmi abin da Ubangijinku Ya yi muku wa'adi, gaskiya?" Suka ce: "Na'am." Sai mai sanarwa ya yi yẽkuwa, cẽwa: "La'anar Allah ta tabbata a kan azzãlumai."
7|45|"Waɗanda suke kangẽwa daga hanyar Allah, kuma sunã nẽman ta ta zama karkatacciya,. kuma sũ, game da Lãhira, kãfirai ne."
7|46|Kuma a tsakãninsu akwai wani shãmaki, kuma a kan A'arãf akwai wasu maza sunã sanin kõwa da alãmarsu; Kuma suka kirãyi abõkan Aljamia cẽwa: "Aminci ya tabbata a kanku: "Ba su shige ta ba, alhãli kuwa sũ, sunã tsammãni.